← Book details Hadin Zumunci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 9

Sashe 8

Hadin Zumunci Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Aisha💞
[6:17PM, 21/12/2016] ‪+234 701 725 1433‬: 🐾🐾HADIN ZUMUNCI🐾🐾
Written by Aysha Gana
90---------------95
*********************
Ina isa cikin falon na fara jin shewa abunda yafi tayarmin da hankali shine muryan mace dana jiyo innalillahi wa'inna ilaihi raji'un kalman dana keta fada kenan har na samu nutsuwa lallai ya hakim abun nashi ya kai ya kawo har cikin gda ni aimana naga ta kaina da lamarin ya hakim muna hada ido da ita saida jikinta yai sanyi shima ya lura da haka sai yace ki saki jikinki babyna meta isa ta miki cikin jin tsoro tace nidai gaskia dear mu tafi tunda ta dawo sao yai murmushi yace muje ko tunda kinji tsoronta niko bakin ciki ne ya hanani magana lallai ma ya hakim ni xai dauko ma karuwa ya kawo cikin gda lallai ya hakim ya cuceni ya gama xubar mun da mutunci a idon mutane amma ba komai wlh ni aimana saina koya wa ya hakim yanda xai soni nai wata daria na wuce dakina.

Washe gari da safe bani da lecture dana tashi na shiga kitchen na hada ma ya hakim brkfast sannan na koma daki nayi wanka na saka wani riga mai hanu daya da wani pencil jeans nayi parking gashina sannan na fesa turare mai suna "passport for luv" sannan na fito kai tsaye dakin ya hakim na wuce cikin tsoro ina turo kofan na ganshi yana kokarin saka neck tie da sauri naje nace" ya hakim ina kwana mamaki ne karara a fuskan shi ya bini da kallo tun daga sama har kasa gabadaya ya kasa dauke idonshi a kaina saida yaga ina kallon shi sannan ya hade rai yace" lafia kika shigo mun daki? Nan na karasa na karbi neck tie din hanun shi na fara daura mishi saiya samu kanshi da qin hanata nace" laifine danna shigo dakin mijina? Tsayawa kawai yayi yana kallona baice komai ba ya dauki briefcase dinshi ya fita raina ya matukar baci amma ban nuna ba nace " saika dawo allah kiyaye hanya bai kulani ba ya fice, nan na tsaya ina tunanin yanda xanyi na jawo hankalin ya hakim kaina yanda xai manta da zinat dana ga tunani baxai mun ba kawai saina hau gyara wa ya hakim daki na wanke mishi toilet sannan na fito na dau wayata na fara game.

Misalin karfe 1:30 bayan na idar da sallah na tashi na shiga kitchen na dafa shinkafa da miya bayan na gama na hada hadadden zobo na na saka a cikin jug sannan nasa a fridge kana na dauki abincin na jera a dining sannan na koma daki na yi wanka bayan na fito na tsala kwalliya ta cikin wata doguwar riga wanda tunda ga kasa tsagu ne har xuwa cinya sannan na gyara gashina banyi parking ba saina barshi a haka ya xubo a kafada na falo na koma na duba agogo saura minti goma ya hakim ya dawo tv na kunna ban jima da fara kallo ba naji tsayuwar motar shi ko minti uku baiyi ba naji ya bude kofar falon da sauri na tashi na karbi briefcase dinshi tare da bashi peack a kumatu tsayawa kawai yayi yana kallon ikon allah danaga kallon yayi yawa saina hure mishi ido nace" ya dai honey na banyi xaton xai mun magana ba kawai saiji nayi yace" ba komai kinyi kyau fari da ido nayi nace" tnxx swt luv kana nace ka xo muje kayi wanka sannan kaci abinci kama hanun ya hakim nayi xuwa daki shikuwa sai bina yake kaman wani akuya😂 har kofan toilet na raka shi bayan ya shiga toilet ne na nufi wordrobe dinshi na fito mishi da fari sol din jallabiya na feshe shi da turare kana na fito na koma falo sh kuwa ya hakim yana fitowa daga wanka yaga na ajiye mishi kaya murmushi kawai yayi a ranshi yace" aimana kenan ina xaune a falo ya fito kai tsaye dining ya nufa ina ganin haka nayi sauri na tashi na fara serving dinshi sannan na koma na xauna gara cin abincin yayi dadi ne yaji ya ratsa har cikin kunnen shi ina lura dashi a haka yaci abincin nan sosai sannan yace" aimana nace" na'am ya hakim yace" wai ko kina da aljanu ne nace" aljanu kuma yaya yace" to naga yau tunda safe u have been acting so strange i thought ko aljanune suka shafe ki daria nayi nace" ko kadan yaya dama so nake na rokeka yafiya akan duk irin abunda nake maka dan allah kayi hkr ka yafe mun ynxu ya kamata ace mun yada duka makaman mu mun rungumi kaddara ya kamata mu xauna lafia ko dan su mami suyi alfahari damu tunda na fara magana ido kawai ya hakim ya xuba mun....

To fa masu karatu kuna ganin Hakim zai yarda da shawaran Aimana? Duka amsoshin ku yana cikin page na gaba kuma na karshe ku biyoni dan jin amsoshin tambayar.

Aisha💞
🐾🐾HADIN ZUMUNCI🐾🐾
Written by Aysha Gana
95-----------------100
***********************
Nace " ya hakim baka ce komai ba numfashi ya hakim yaja sannan yace" aimana kenan asali ni dama ban tsaneki ba halinki ne na rashin kunya da tsiwa bana so shiasa kika ga ina miki haka amma tunda keda kanki kika nema mu shirya shknn allah ya qara hada kanmu nace" amin ya hakim nandai hira ya barke a tsakaninmu wanda mu kanmu abun mamaki yake bamu sai kace ba aimana da hakim ba wanda kullum cikin fada muke kaman kajii amma wai sai gamu a karkashin inuwa daya muna zaune harda tadi lallai kam sai ynxu muka ga wautan mu na rashin bin umarnin iyayen mu wanda suka ce mu xauna lafia amma mu kenan kullum cikin tashin hankali sai kace a filin yaqi lol......

Da daddare bayan na idar da sallahn isha'i na shiga kitchen na dafa mana indomie wanda yaji ingredients sannan na hada mana kunun aya na saka a fridge kana na koma daki na tsalo wanka na shafa mai me shegen kamshi sannan na ciro wata nyt gown red mai shegen kyau na saka na feshe jikina da turare har lokacin ya hakiim bai shigo ba falo na fito na xauna ko minti biyar banyi da xama ba sai gashi ya shigo da sallamar shi tsayawa yayi yana kallona tashi nayi na isa gabanshi na tsaya har ynxu ni yake kallo hure mishi ido nayi nace " ya hakim irin wannan kallo haka yace" gani nayi kin chanja mun aii kinyi kyau murmushi nayi nace " kaxo muje kayi wanka ga abinci yana jiranka daki ya shiga ni kuma na koma falo na xauna can sai gashi ya fito sai bula kamshi yake yi nan dai muka zauna nayi serving dinshi cin abincin yake yi amma gaba daya idonshi yana kaina wani irin kallo yake mun a haka muka kammala cin abincin yaya yace" aimana yau kam aii xaki tayani kwana ko? Sunkuyar da kaina kasa nayi nace"duk yanda kace tashi yayi ya kamo hanuna kai tsaya hanyar dakin shi ya nufa ni kuwa mai kawo muku rahoto na tsaya ina sude sauran indomie din da suka ci sai gani nayi sun nufi hanyar daki da gudu na tattaro littafina da biro na dan binsu dakin amma ko kafin na isa har sun rufe kofar su, asuba ta gari hakim and aimana.

Cikin satin nan wata irin shaquwa ce me karfi ta shiga tsakaninmu wani tattali yake nuna mun kullum inya dawo daga aiki muna tare komai tare muke yi rayuwa muke cikin farin ciki wanda muke fatan ya dore har karshen rayunmu.

*YA LABARIN ZINAT*?
Kullum cikin kiran hakim take yi a waya wataran ya dauka wataran yaqi dauka duk hankalin ta ya tashi ta rasa gane kan hakim a cikin yan kwanakin nan ranan kamma da ta qira shi ta gwammace dama bata kirashi ba domin kuwa aimana ce ta dauka lokacin ya shiga wanka xinat tace" hello aimanaa tace " ke karaman yar bariki karki kuskura ki qara kiran mijina domin kuwa yafi karfin ki ke bakya ma jin kunya ace ke kike bibiyar namiji bashi ba ya kamata ki shiga makarantar ta nutsu kije ki nemi miji kiyi aure domin kuwa hakim mijin mace daya ne idan kuma kika kuskura kika yi gigin shigowa gdana to wlh gdana kaman wuta yake bnxa kawai shashasha sannan ta kashe wayar zinar kuwa ranan yini tayi tana kuka.

Mu kuwa Soyayya muke sha nida ya hakim kullum muna tare munje gdan mami taji dadin ganinmu a haka ta qara mana nasiha anan ma take fada mana an saka auren yasira da ya samir nayi murna sosai...... Shirye shiryen bikin yasira muke yi wanda a satin ne kuma na tashi da wani irin xaxxabi ga yawan barci nan dai ya hakim ya daukeni sai asibiti gwajin farko likita yace ina da ciki murna a gun ya hakim ba'a cewa komai nan da nan ya yada a cikin dangi kowa sai murna yake yi.
Chapter 8 · 0% Book details