← Book details Hadin Zumunci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 9

Sashe 4

Hadin Zumunci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

****ABUJA****
Ya hakim bai dawo gdan ba sai wurin karfe uku na rana yana shigowa mami ta kirashi tace''ka shirya xaka raka su yasira kasuwa aimana xata kara kaya naga kaman kayanta suna so suyi mata kadan a karo mata sababbi'' yace '' mami baxan samu xuwa ba akwai inda xani''wani mugun kallo mami tamai saida ya dukar da kansa tace '' da kyau har uxurinka yafi nawa kodan kaji ance aimana xaka raka shine kke so ka xamar da tafiyar to wlh saika je,ni dama nasan ka raina maganata amma idan alhaji ya dawo saina sanar dashi a daura muku aure akai maka ita in yaso sai muje mu dauko gawarta anan ne xamu gane kiyayyar da kke mata.... Nan dai mami taci gaba da xuna mishi masifa nan da nan ya durkusa har kasa yace, kiyi hkr mami allah ya huci xuciar ki, su shirya na kaisu idan na dawo saina wuce inda xani '' mami tace ywwa allah maka albarka yace '' amiin.
Muka shirya muka fito sanye nake da wata atamfa riga da skirt, na dauko gyalr na yafa kalar atamfar yasira ta kallen tace, '' allah yasa kar ya hakim ya yaga miki wannan gyalen da kika yafa, amma koda yake bakwa shiri baxai ce miki komai ba. Muna fitowa shima yana fitowa daga bangaren shi cikin shigar kananan kaya sun masa kyau muna hada ido dashi sai ya hada rai yace''ke baki da kunya ko yasira bata fada miki basa yawo da gyale ba'" nima na hada rai nace''bata fada mun ba sai daii in kai ynxu xaka fada mun''tsawa ya daka mun yace ba rashin kunya nace kimin ba tambayarki nake, duk wata muguwar dabi'an ki sai kin barta indai muna gda daya dake kuma ki koma ki cireshi na fada miki''na yamutsa fuska nace '' ni bani dashi haka kurum sai aita takura ma mutum kuma idan yai magana ace bashida kunya kamar shiya kawo rashin kunya dunia'' yace ' oh! Baki dashi ko to xakiyi shi da kudina xan sai miki allah yasa karki saka kiga yadda xamu kwashi yan kallo nida ke''yadai yita fadanshi ban kulashi ba ya gaji ya hkr.
Wuse market mukaje a bakin wata plaza mukai parking muka fito muka shiga wani babban shago ya hadu sosai, kayan da nake xaba daban kayan da yake xabar mun daban sai kace shi xai saka. Ya juyo ya kallan yace''wannan kayan da kike xaba kina da kudin da xaki biya ne? Nace''kai xaka bada kudin" yace" to ba suyi mun ba don ba irinsu xa'a sai miki ba''nace wai kai meyasa kke mun irin haka ne bafa kai xaka saimun ba amma kace sai wanda ya maka xan saka''saiya juyo ya kallan tare da hade rai''yace karna kuma jin kinyi magana".
Saiga wani saurayi ,dama tunda muka shigo yake kallonmu ya karaso inda muke yace, nawa ne kudin kayan data xaba saina biya'' ya hakim najin haka saiya hada rai yace, kai malam bamuyi kama da irin wanda xaka biya ma kudi ba, ko ance maka bamu da kudin biya ne'' sai mutumin yace ba haka bane nayi niyya ne kawai badan komai ba sai dan na yaba da hankalinta ne'' ya hakim yace''mungode jeka da niyyar ka bama so" mutumin yace haba abokina ya ina son nai abun alkhairi kana so ka hana, ko baka so ka bani kanwarka ne? Ya hakim ranshi ya baci yadaka mun tsawa" wuce muje" jiki na rawa muka bar wurin don a lokacin yadda na ganshi yana iya kaimin duka idan na tsaya taurin kai, ni abunma har mamaki yake bani ba dama ace ana sona a gabanshi sai yaji haushi, ko ina ruwanshi oho! Wannan shine karfin hali barawo da sallama kaki sona kuma ka hana a soni, raina a bace muka tafi har wurin da muka kai dinki shagon mus'ab tailor , shine tailor din mami ya hakim ne ya xabi dinkin da xa'ai mun ina kallon sa bance komai ba, don ko nace maganata baxa tai amfani ba yasira kuwa muguwa sai faman daria take yi har muka dawo gda. Da abin ya isheni nace''wai ke dawa kike darian nan? Tace" allah baki hkr bani na kar zomo ba rataya aka bani shi xaki yiwa bani ba.... Wai hayaniyar me nake ji ne an tafi lafia an dawo da hayaniya " mami take tambayarmu yasira ta kwashe yadda akai ta fada wa mami, sai mami tace xonan yata kyalesu shima xai xo nan ga sameni, ke kuma kar ki sake mata daria na fada miki".

Am srry rashin typing da wuri bani da charge ne ga wannan kuyi manage kafin nayi charge.

Aisha💞
[6:16PM, 21/12/2016] ‪+234 701 725 1433‬: 🐾🐾HADIN ZUMUNCI🐾🐾
Written by Aysha Gana
45----------50
*******************
Haka muka cigaba da xuwa makaranta tare dasu yasira kuma abba ya daukar mana lesson teacher yana mana kuma muna ganewa cikin ikon allah. Shima mai takuramin baya kasar abba ya turashi spain ya duba kamfanonin sa da suke can, bamma san lokacin da xai dawo ba shiasa nake cin karena ba babbaka.
Mun kammala karatunmu cikin nasara kuma da sakamako mai kyau jira kawai muke a fara bada admission mu fara xuwa jami'a har wannan lokacin ya hakim bai dawo ba mun daiji mami tana cewa yai waya cikin satin nan xai dawo amma bai fadi rana ba.
Ranar juma'aa muka shirya sai maitama gdan su wata frnd dinmu da mukai sch tare ranar acan muka wuni sai wurin magriba muka dawo mami ta dinga fada wai munje mun jima muka ce mami mun dade bamu hadu bafa shiasa tace "to naji in kunyi sallah sai kuje kuyi ma yayanku sannu da dawowa yasira tace" mami ashe yaya ya dawo " eh ya dawo bai jima ba yasira tace" aimana tashi muje muyi wa yaya barka nace" ba xani ba haka yasira ta kama hanya ta tafi nace allah raka taki gona. Bayan kwana biyu abba ya kirani falon sa yace ya kamata kije kaduna ki gaida iyayen ki tunda baku fara xuwa sch ba sauran kuma in kikaje kiqi dawowa muyi fada dake daria nayi nace" abba ai kuma na riga da na saba daman ko naje xan dawo gurin mami na abba yace da kyau yar mami ai daman mamin tana shagwaba ki daria kawia nayi sannan na tashi na koma daki.
Bayan munyi sallar magariba mami ta kwalla mun qira naje da sauri tace in dauki abinci ya hakim na kai mishi daki saida gabana ya fadi saboda tunda ya dawo banje na mishi sannu ba haushina yake ji kaman ya kasheni.
Haka badan ina so ba na dauka na wuce da sallamata na tsaya a bakin kofa yasan nice amma yake tambayar wanene dana ga xai raina mun hankali kawai saina kutsa kqina cikin dakin zaune yake kan doguwar kujera riga ce armless a jikinsa sai 3 quarter, wuce shi nayi naje kan table xan aje kenan yace kawo min nan da kamar baxan juya ba sai kawai na durkusa na ajiye a gabansa xan tashi kenan ya riqe mun hanu da karfi saida nayi kara yace waya ce ki shigo mun daki da yake baki da mutunci na dawo kowa yaxo yamin sannu da dawowa amma ke baki xo ba saboda ban isa da ke bako xaki bani hakuri ko kuma, nai shiru '' magana nake miki fa " naqi magana saiko ya take mun dayan hanun dana yi dafe dashi bansan lokacin dana ce kayi hkr yaya sannan ya sakeni, ina xuwa bakin kofa nace anki xuwa gaida kai din nina aikeka da xaka dameni wlh sa'a ma kaci dana xo wannan kuturun dakain naka, yace''to sarauniyan marasa kunya yi waje kuma kinsan allah xan kamaki saikin yi fitsari xan kyaleki nace " a hayye ashe aimana tana da matsayi tunda har an nada ni sarauniyan marasa kunya kasan allah tunda kaqi kama girmanka raini ynxu na fara maka shi da idonka kaman na mujiya aiko da gudu ya tashi xai biyoni aikuwa da gudu na ari na kare ina xuwa mami tace kinkai masa nace eh...

Aisha💞
[6:17PM, 21/12/2016] ‪+234 701 725 1433‬: 🐾🐾HADIN ZUMUNCI🐾🐾
Written by Aysha Gana
50------------55
********************
Muna cikin tafia gdan wata kawar hajia mariam mami nida yasira tace" niko bana son xuwa gdannan haidar da jabir sun cika sa ido shiasa bana son xuwa nace" kema dai yasira ina ruwanki dasu wurinsu kika xo da xaki dami kanki akan me, sallama mukayi falon tana xaune muka gaidata tace hajia bilki ce ta aiko ku ko? Mukace eh tace gashi kuma ba'a kawo sakon ba amma kuce mata tayi hkr ana kawowa da kaina xan kawo mata muka ce to. Muna fitowa muka hadu da jabir din mukai kamar bamu ganshi ba, shine yace ko gaisuwa bbu? Muka ce kayi hkr ina wuni yace saida na roka yasira tace ba haka bane kasan ance hankali ke gani ba ido ba, sai ya kallen yace ke kuma madam ya sunanki? Murmushi nayi nace ummu aimana yace" kai sunan ya dace dake mukace bari muje kada dare yai mana yace " to saina xo" saida muka wuce yasira tace ke aimana kinyi kasuwa fa , nace " wani irin kasuwa me ya dameni dashi ya dade bai xoba shiya sani yasira tace " kedai kibi a hankali ku rabu lafia muna dawowa mukaci karo da ya hakim ko kallonshi banyi ba muka wuce gda....

A gurguje plss....
Chapter 4 · 0% Book details