← Book details Hadin Zumunci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 9

Sashe 3

Hadin Zumunci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan mun dawo gda mami ta kallen tace''yar mami ya naga fuskan ki ya canja ne ba kamar yadda kuka fita ba, '' yasira tai sauri tace mami fada sukayi ita da ya hakim a wurin lunching, ' tana shirin fadar abunda ya hadamu, karaf! Sai muka ji sallaman shi da gudu yasira tai bayan mami. Yace, '' ke ni idan kika ce xaki rainani wlh xan balla ki wawiya kawai, '' ya kama hanya xai wuce sai mami tace, '' kaii xonan wai kai wani irin mutumne ka cika xafin xucia, kullum cikin fada kake da kannen ka kamar sa'annin ka to bari kaji raina ka xasuyi tsoron da suke maka ma su daina, ku kuma ku tashi ku bani wuri..... Muka tashi sum-sum muka wuce, mami tace, '' mai kuma ya hada ka da aimana? Yace, '' mami yarinyan nan ta raina ni'' nan ya kwashe yanda a kai ya fada mata ya kuma cewa, " mami kuma kuna cewa xaku hadamu haka xamu xauna ban isa na fada mata tayi ba, gaskia mami da sake a sako shawara''mami tace''da kyau ubanmu ai dole mubi yadda kke so saboda kada ka tsine mana mubi dunia" yace '' mami wlh ba laifina bane kunce ga yadda kuke so kuma na amince sai kuma ta riqa rainani gaskia baxan yarda ba'" nandai mami ta riqa baiwa ya hakim hkr harya hakura ya fita.

Bayan mun cika kwana biyun mu washe gari da safe na tashi na fara hada kaya yasira tace" kar dai ince har hada kayan tafia? Nace''ina ruwanki da hada kaya na ko laifi ne dan na hada? Tace''aa allah baki hkr. Da sallamata na shiga falon abba yana nan kasan cewar yau weekend ne, daga shi sai mami ne a falon ya kalleni yace, ummu aimana ya akai ne? Nace dama abba naxo nai maka sallama ne ya samir yace da wuri xamu tafi''yace, da wuri haka aimana na xata xaki mana kaman wata guda''sai nai dan murmushi nace, abba ai akwai makaranta shiasa '' yace hajia bilki kinaji yar taki wai tafia xatai ta barmu''mami tace alhaji dama ina so nai maka wata magana yace ta mefa mami tace '' mai xai hana aimana ta dawo nan da xama inyaso saita karasa karatun ta dama ina da burin rikonta tun tana karama allah ne bai yiba,kaga saisu kara shakuwa da yan uwanta'abba yace kwarai kuwa bilki kin kawo shawara haka ko xa'ayi '' ni kuwa wata irin faduwan gaba ne ya sameni nan ko gumi ya rinka ketomin saika ce wadda aka kama xa'a kai gdan yari innalillahi wa inna ilaihi raji'un kalman danake ta nanatawa kenan a xuciata, na shiga uku ni aimana da rayuwata ta yaya xamu xauna gda daya da ya hakim alhalin bama jituwa dashi? Sai da nace ma ya samir baxan xoba ya takura mun irin abunda nake gudu kenan... Mami ta lura dani yadda na canxa tace '' yar mami ya naga kinyi shiru kodai baki son xaman ne? Nace aa mami ba komai Abba yace '' bari na kira mansur dinma nan take abba ya kira numbern abbana bugu daya xuwa uku ya dauka cikin ladabi yake amsa wayar '' yaya ina kwana''yace kalau muke abbana yace ''yasu hajiar da yara '' duk suna lafia'' Abba yace '' dama ina son sanar dakai cewan karkaga samir ya dawo shikadai to na kwace yata ta dawo wurina da xama abbana yace''haba dai yaya har saika fadamun ai duk yanda kayi daidai ne kagaida mun hajia da yaran '' abba yace '' insha allahu xasuji '' haka sukai sallama.... Mami tace ' to yar mami kin xama yar abuja ki saki jikinki komai kike bukata ki sanar mana karki cuci kanki nan ma gda kika xo.....

To fa Ku biyoni don jin yaya xaman Aimana da Abdulhakim Xai kasance.

Luv u oll😘
[6:16PM, 21/12/2016] ‪+234 701 725 1433‬: 🐾🐾HADIN ZUMUNCi🐾🐾
Written by Aysha M. Gana
*****************
30------------35
Can sai ga wani daga cikin abokan ango ya zagayo kusa da yaya hakeem yace, '' ya kai abdul wannan babe din fa? Sai ya kallan ta gefen idonsha yace, '' kanwata ne kuma tana da miji ba ruwanka da ita kai abinda ya kawo ka. " mutumin yace,'' shknn abokina tunda kaimin bakin cikin samun xukekiyar budurwa ko ince mata amma ba komai in rabo nane xan samu'' ya hakim ko bai kuma asa magana ba, nan aka kira abokin ango dan bada tarihin ango, ita kuma yasira ta bada tarihin amarya, bayan sun gama aka bukaci ango da amarya domin su fito suma su chashe a fili, nanfa DJ ya saki sauti da wakar da akai ma amarya da ango kudi ko like su ake kamar ba gobe.

Banda wulakanci irin na yasira anama amarya da ango liki amman ita nida ya hakim take mawa sai daukan mu hoto akeyi, da naga haka saina zame zan fito daga fili sai ta riko mun gyalen dana yafa.
Tace, '' haba dan allah ina xakije? "
Nace, '' nidai ki barni kawai nagaji ne gda ma xani. ''
Tace, '' saboda me ba'a gama ba xaki tafi '' nace saboda sa'idawa sunyi yawa duk inda mutum ya gilma ido na kansa shiasa xan bar wurin''tace, '' yi hkr dan allah mana a tashi ai an kusa tashi ba wani dadewa xa'a kuma yi ba" Haka na koma har aka tashi, muna fitowa mukaci karo da mai hoto har yaje ya wanko hotunan, yasira ta karba ta bashi kudin. Nace, '' mu gani'' tace, '' baxan bada ba salon ki yaga''nace, '' oh ashe ke kika sashi ya rika mana hoto, '' tace '' eh mana kuma mami xan kai mawa ta gani''nan da nan na marairaice mata nace, '' dan allah karki kai mata ki yagasu''tace''lallai ma haka kurum na yaga kudina''nace to ga wani kudin sai na baki a yagasu don allah hkr''ta kallan tayi daria tace, '' kanki ake ji wai mahaukaci ya fada rijiya yace ni ku kyale ni wanka na nake yi. ''nace ynxu haka xamuyi dake yasira? Tace to waii miye abun damuwa kawai don ka dau hoto da dan uwanka naga aiba komai bane karin *HADIN ZUMUNCI*ne''nace a wurinki ba don kinyi hakane dan ki kulla mun sharri a wajen su mami, to yadda kika kulla haka xaki kwance muguwa kawai''sai tai tamin daria.
"Assalamu alaikum"
Sai muka juya domin muga mai sallama,wa xan gani inba mutumin daya xo wurin ya hakim lokacin muna cikin *hall*,muka amsa sallamar sa kaman yanda ya mana.
Yace dan allah malama aimana idan baxa ki damu ba ina son magana dake''sai muka juya muka kalli juna nida aimana sai naga kaman ranta baiso ba.
Nace, '' ya naga kaman ranki bai soba? Tace, '' ni wlh bana son naga kina kula samari''nace''kamar yaya aure gareni ko rana aka samun? Tace lallai aimana wuyarki ta isa yanka, nidai kiyi sauri kiji abunda xaice kar ya hakim ya fito nace nima ba dadewa xanyi ba sannan na karasa gunshi nace''malam ya akayi kasan sunana? Yace''kinsan in mutum yana son abu dole ne kabi diddigi har ka gano wani abu daga gareshi, cikin lokaci kankani sonki da kaunarki sun mamaye xucia ta ina fatan xan samu karbuwa.. Nace, " allah sarki ngde da irin kaunar da kke mun allah xaba mana abunda yafi alheri''yace a wani gari kke? Nace''a kaduna nake '' yace ni anan iyayena suke da xama amma ni costume ne ina aiki a lagos bikin nanne ya kawoni sunana Jameel alkaseem muna xaune a maitama''ni kuma naxo hutun gdan yayan babana alhaji kabir '' yace oh minister? Nace eh yace kice ke yar manya ce,nidai murmushi nayi saiya miko mun rafar kudi har naira dubu goma yace''gashi kwa sha ruwa''nace''gaskia nidai baxan karba ba" yace haba aimana baki san ba'a maida hanun kyauta baya ba, maida hanun kyauta baya sai shaidan nace"hakane yace to tunda kinsan da haka saiki karba indai ba kin raina ba.
Na saka hanu xan karba kenan sai ga ya hakim nan ya fito,wani mugun kallo da yai min saida hanjin cikina ya motsa yasira ma nan da nan jikinta ya fara rawa...
[6:16PM, 21/12/2016] ‪+234 701 725 1433‬: 🐾🐾HADIN ZUMUNCI🐾🐾07017251433
Written by Aysha M.Gana
40-----------45
*********************
Haka rayuwata ta kasance a garin abuja maganar jituwa kuwa bbu ita tsakanina da ya hakim kullum muke nan fada kaman kaji, mami taita fada har abun ma ya isheta tasa mana ido, shiko abba abunma daria yake bashi idan yaga muna fada. Har mami ta gaji ta same abba a daki tace'' ynxu alhaji haka xa aita xuba ma yaran nan idanu suna tashin hankali? Abba yace''kedai kawai ki rabu dasu kuruciya ce ke damunsu wata rana xasu daina so nake ma naje kaduna danmu tattauna maganar aurensu shida aimana daga xaran ta gama makaranta sai a fara shirin biki''mami tace''ywwa hakan ma yafi in sukayi auren idan suka ga suna gda daya aii dole su hkr, amma alhaji yaushe xaka je? Abba yace''ranan asabar insha allah mami tace to allah kaimu abba yace '' amiin''.

Ranar asabar abba ya tafi kaduna naso na bishi amma mami tace aa, muna xaune a falo saiga mami tace''ku shirya yayanku xai kaiku kasuwa ku xabi abunda kuke so'' yasira da murnarta tace''to mami ynxu ko xamu shirya kar ya dawo yaga bamu shirya ba yace ya fasa'' niko raina ya baci dan kawai kar mami tayi fada ne da wlh ba inda xani da wannan mugun mutumin ko hanya bana so mu hada balle tafia mai tsawo.

*** KADUNA***
Abba yana isa kaduna kai tsaye gdanmu ya wuce bayan yaje ne suka gaisa da umma da abbana sannan abba yace''mansur dama naxo ne akan maganan aimana da hakim ya kamata mu tsayar da lokaci da xaran ta gama makaranta sai a fara shirin biki '' abbana yace to yaya''duk yanda kace haka xa aii allah ya tabbatar mana da alheri '' amiin''sannan ya mike yace shi xai koma saboda ba kwana xaiyi ba nandai abbana da umma na suka rako shi ya shiga motan shi saii abj.
Chapter 3 · 0% Book details