Sashe 1
Hadin Zumunci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[6:16PM, 21/12/2016] +234 701 725 1433: 🐾🐾HADIN ZUMUNCI🐾🐾
17/8/2016 8:30am
Written by Aysha M. Gana
***********************
1-5
'Kinsan allah xainab banson tafiyar nan, yaya samir ne ya takura min in ba haka ba ba abunda xai kaini abj... Zainab tace aimana kenan nasan abinda yasa baki son zuwa saboda mutuminki, kinsan Allah aimana da abbanku zai burgeni ya hadaku aure keda hakeem naga yanda xakuyi in ganku gida daya"
Nai mata wani irin mugun kallo nace"lallai ma zainab ban taba tsammanin xaki min irin wannan mugun baki ba sai yau, ashe baki sona ki rasa wanda zaki min fatan na aura sai wanda idonsa ya bude da yawon dunia ya saba rayuwa da gogaggun yanmata ya saba holewa dasu, me xanyi dashi allah ya sauwake min, ni ummu aimana bana fata shida daya ganni gwanda yaga muturwa da xata daukeshi ina xaman xamana ki rika yimun mugun baki bana so gaskia'.... Zainab tayi daria tace aimana kenan kinsan kowa da irin nasa salon soyayyar, haka taku salon soyayyar ku take, Allah yasa mu dace kawai" nace aii ke dama zainab bakya sona don duk maison aimana ba xai mata fatan auren abdulhakim ba " zainab tace to miye matsalar sa dan kawai kuna takun saka na dan wani lokaci xaku bari, baki ji ance wani son idan yai yawa ya kan zama kiyayyya ba, wani kin ya kana xama so mai karfi har xuwa karshen rayuwa.kinsan allah duk abinda yake miki da an hadaku gda daya xai daina, baki ji ance *Biri a hannun malamai yake karya ba inko yaje gdan arna yasan kwanan sa ya kare. Ai wlh aimana yadda kuke haka din nan lokaci kadan zaki juyar masa da kwakwalwa,kina da kyau,kina da diri, duk inda mace takai kin kai, ai banga namijin da xai daga miki hankalinki ba sai dai ke ki daga masa hankali, Aimana allah ya baki baiwar kyaun da duk namijin daya kalleki sai yayi sha'awan mallakanki a matsayin matarsa ta aure.... Nace, 'to malama xainab bama hada mun xa'ayi ba balle ki rika mun kakalan tsiyarki. Zainab tace, 'aimana allah ya bamu rai da lafia musha kallo' nace, 'xainab dan allah ki fito fili ki fada wlh in kina sonsa ne, allah ko ba matsala kinga saimu sha biki xako kiji dadi cikin family dinmu' zainab tace, 'Allah baki hkr aimana abinma bai kai haka ba"....... Haka muka karaci hirarmu har lokacin tashi yayi malam musa yaxo ya daukeni, direban gdanmu kenan shi yake kaimu duk inda xamu kuma ya koma ya dauko mu aikinsa kenan a cikin gdanmu,abbanmu duk wata yake biyansa'...

Written by Aysha Gana
******************5-10
ASALINSU
Sunana Ummu Aimana, mahaifina Alhaji mansur su biyu iyayensu suka haifa shida yayanshi Alhaji kabir wanda ake ce mishi 'alhaji babba....yana da mata 1 da yaya uku babbansu shine Abdulhakim sai yasira wacce take sa'a na sai kuma autarsu hanifa....mu kuma mu biyu iyayena suka haifa yaya sameer shine babba saini ummu aimana.. Mun taso cikin shakuwa da kaunar juna tsakanin nida yasira da hanifa amma babu wanda na tsani na gani irin ya hakim bama shiri ko kadan... Gashi kuma ayau ne xamu je abj gdansu nida yaya sameer....
CIGABAN LABARIN
Da sallam na shiga gda umma ta amsa, ita kadai ce kawai a cikin falon. Umma tace, "har kin dawo aimana" nace, ' eh umma mun dawo kinsan yau juma'aa kurarren lokacine saboda xuwa masallaci sallah " umma tace, "hakane fa, to saikiyi maxa ki fara shiri kafin yayanki ya dawo yace kifito,nasan ki da nawan tsiya,in dai akan kwalliya ne kin rinka bata lokaci kenan, shiasa ma na hada miki kayanki saiki duba idan akwai abunda xaki kara saiki qara da sauri" nace, "yawwa umma kin hada mun har da kayan da na karba wurin ja'afar tela?umma tace ban saka ba bansan inda kika ajiyesu ba" "Na manta ashe suna cikin wordrobe dinki. Umma tace, "meya kai kayanki cikin wordrobe dina? Bana hanaki ba allah baki sa'a na kuma gani sai daii ki dawo ki samesu a waje na watso miki. " nace ''allah baki hkr umma baxan kuma sawa ba''.
Harna kammala shirina ya samir bai dawo ba naita jin dadi saboda na gama shirina a tsanake dan shi ma wani lokacin akwai shi da fada kaman ya hakim, amma shi yafi ya hakim saukin kai yaya hakim kam! Sai fadin ran tsiya, sai yaita ma wanda ya damu dashi, ni kam ko a jikina bai ma isheni kallo ba balle har abinda yake yi ya dameni.
Muna xaune ya samir yai sallama muka amsa yace, '' ina fatan kin shirya ko? " nai dariya nace, '' ai yaya kai kawai nake jira sai yace, '' umma kinga har xamu tafi abba bai dawo ba balle muyi sallama. '' umma tace, '' kawai ku yi tafiarku indai abbanku ne ba ynxu xai shigo ba. '' ......muka dau kaya muka saka a cikin booth din motar sai ya sameer yace, '' to mudai umma sai allah yai mana dawowa. '' umma tace to allah kaiku lafia banda dai gudun tsiya ku tafi a hankali sannu-sannu bata hana isa saidai a dade ba'a je ba. '' muka amsa da to umma''

10-15
**************
Mun dau hanyar birnin tarayya muna isa ana kiran sallar magariba, nan danan ya samir yai ma masu gadin gidan horn, sai da suka fito suna ganin ya samir sai suka bude da saurin su.
''Oga barka da xuwa. '' cikin farin ciki da murna ya samir ya amsa musu mukai cikin gdan, daidai lokacin hanifa ta fito tana ganin mu sai tai cikin gda da gudu saiko ga yasira da saurinta tana xuwa ta rungumeni.
Tace, ''oyoyo yar uwata, oyoyo aimana mafarki nake kodai haka idona yake gani? '' sai nai murmushi nace, ''nice yasira kina mamaki ne? " tace, "kwarai ma kuwa yaushe rabonki da garin nan sai nace to yau Allah ya kawoni shikenan ko. " taja hanuna muka shiga ciki, lokacin mami tana sallah, muma sallah muka wuce yi.
Bayan mun idar da sallah sai yasira tace " To aimana sai muje ku gaida mami dama kullum tana maganar ki waii ta dade bata ganki na. "
Muna shiga falon mami da murnarta ta tareni tace, '' Oyoyo yar mami har maminki tayi fushi dake tunda ko dan hutu baki xuwa yi mana, ko dai hajia hadixa ke hanaki xuwa yi mana hutu? Dama ina da niyar xuwa in taho dake sai gashi allah ya kawoki. "
Nidai tunda take maganar ba abinda nake sai murmushi nace, ''mami dama ina da niyar xuwar sai kuma ga yaya sameer shine muka taho tare. '' mami tace,''Oh! Ni bilki girman ya mace ba wuya kalli yadda yar tawa ta xama babbar mace sai aure ko aimana? "
Bance komai ba sai yasira ce take dariya, mami tace" ki gama darian ki tare xa'a hadaku a aurar. '' yasira tace "mami ni ba ynxu ba sai nan da shekara uku"
mami tai mata wani irin kallo tace ''ko goma ba, kinaso ki tsufa mun a gida kenan to ku fara shirin yin aure a yan shekarun nan. " yasira tace''mami akwai ta da iya tsokanar mutum'' mami tace ''oh! Tsokanarki ma nakeyi ko to naji aje a ina tsokanarki shikenan allah kaimu. Saita juya kaina tace, "amman dai aimana kin dawo nan kenan ko?
Nace, '' aa mami kwana biyu kawai xamu yi saboda makaranta. '' mami tace," to sai ku tashi kuyi sallahn isha'i lokaci na neman kurewa, sai kuci abinci. Muka ce, ' to mami''
15-20
Muna idar da sallah kande mai aiki ta dire mana abincinmu tuwon shinkafa ne miyar ganye, sai da mukaci mukayi kat! Mukai hamdala sannan muka mike.
Nace,"to nifa yasira kwanciya xanyi don a gajiye nake so nake nadan huta'" yasira tace " da kyau yar hutu".
Shiko yaya sameer yana can shida mutuminsa basu shigo ba sai wurin karfe tara na dare lokacin ba kowa a falo daga abba sai mami suna kallon NTA news. Ya samir ya durkusa yana gaida su mami.
mami tace" na xata wurin hakim din kaxo shiyasa baka xo mun gaisa ba. " ya sameer yace, " Allah sarki mami mun tsaya yin sallah ne shiasa'" Mami tace, " ni dama ga yar gdana nan ina tare da ita kuma sai kuje ku karata kaida hakim din" ya hakim yace, '' mami muba yan gdan naki bane? " tace, ''ehh" ya samir yace, '' to mami ai mana afuwa abba kasa baki, '' Abab yace '' ba wani bakin da xansa a cikin maganar, ai gaskia mamin taku ta fada'' hakim yace '' to munji munyi laifi ayi hakuri, mami an kai mana abincin ne? " eh, kande ta kai muku bangaren ka." sai suka tashi sukayi wa su mami saida safe. Abba yace da mami''hajia bilki ina yar tawa ne banganta ba? Mami tace " aiko tai bacci kasan yar taka yar hutu ne" abba yace to allah kaimu gobe na ganta da kyau".
20-25
Washe gari da safe yaya samir suka je gaida abba, Abba yace "samir inace dai kuna xuwa ga sauran yan uwa ko? "abba muna xuwa'' to Alhamdulillah haka muke so ku rika karfafa xumunci a tsakaninku ko bayan ranmu bance ku yadda zumunci ba kuso junan ku,ku xama tsintsiya madaurinku daya"suka ce ''abba insha allah xamubi abunda kakeso" Abba yace '' Allah ya muku Albarka ''Ameen''.