← Book details Hadin Zumunci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 9

Sashe 6

Hadin Zumunci Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Nandai aka fara gudanar da biki karfe 7 aka tashi inda kowa ya watse nima mai rubutu ina ta faman jan su karima akan suxo mu tafi amma ina wai sai sun gama kwashe nama ai kuwa naga amarya xata shiga mota da guduna na fito na biyota a baya domin daukan rohoto...... A yaune juma'aa da misalin karfe hudu na yamma bayan sallan la'asar aka daura auren ABDULHAKIM KABIR da UMMU AIMANA akan sadaki dubu 50 daurin auren daya samu halartar dumbin mutane daga kasashe daban daban.... Da daddare aka kaini gdan ya hakim inda nasha kukana nida yasira haka kowa ya watse aka barni ni kadai nan naji tsayuwar motoci tabbasa su ya hakim ne ina jinsa ya shigo da sallamar shi ko motsi banyi ba balle na amsa yace" aimana ki fito ku gaisa da abokaina suna falo nace''wai kai malam meye haka xaka takura mun saiga ya hakim yana marairacewa kamar bashiba saiya bani tausayi nace" kaje xanxo ko saika tasani a gabane kamar nai maka sata saiya wuce sumi-sumi kamar mara gaskia a xuciyan shi kuwa cewa yake "habawa yarinya lallabaki nake yi kawai kafin na sallami bakina daga nan xaki gano waye abdulhakim " wai wata irin darian mugunta. Yana fita na mike na tsaya gaban mirror na gyara fuskata nai waje suna xaune suna hira, nai sallama sannan na gaishe su suka amsa mun cikin mutunci na samu gu na xauna ban kuma magana ba sukai ta mana nasiha mai ratsa jiki sannan sukai sallama suka tafi bayan sun ajiyemin kayan siyan baki ina ganin sun fita na tashi na wuce dakina tare da sawa kofata key. Shikuwa ya hakim yana dawowa sai yaga na wuce saiya kwashe kayan ya kaisu kitchen ya ajiye su sannan ya wuce dakin shi.

Aisha💞
[6:17PM, 21/12/2016] ‪+234 701 725 1433‬: 🐾🐾HADIN ZUMUNCI🐾🐾
Written by Aysha Gana
75--------------80
*******************
Kallo ya bini dashi harna wuce daki sannan ya kunna tv yana kallo kiran waya ya shigo masa yana dubawa yaga zinat baby da sauri ya daga " hello babyna tace" hey durln ya kke? "" lafia lau babyna sai tace" baka kwanta bane na xata ma kana tare da amarya, yace" wata amarya kuma wacce tun daxun tayi kwanciyarta sai tayi darian farin ciki tace" maimakon kaje ka tayata kwanciyar shine kabarta ita kadai ta rungume pillow alhalin gaka sai yace" kema kinsan ba inda ya kamata na kwanta bane da ynxu ina can ina shan gara ko ba haka ba? Cikin kishin maganar daya yi tace" lallaima abdul wuyarka ta isa yanka shine kke fadamin haka sai yace oh! Srry babyna ashe fa kina kishina sai tace lallaima hakim haka ma xaka cemin ko nagode kaima kasan in akwai mai kishinka to nice baka san har ynxu ina nan ina kishin auren da kayi ba ka kyaleni.
Sai yace" haba babyna me yasa kike fadan haka kiyarda dani mana nine fa abdulhakim dinki ki saki ranki aure kamar munyi mun gama sai tace" to shikenan durln sai kaje ka kwanta kaida amaryan ka yace" kema kinsan ba inda xani dama kaman kece da ba saikin fada ba tace" hakane fa nima nasan babu wata mace da xata xo tace xata ture gwamnati na a cikin xuciar ka yace " hakane zinat dina shi yasa nake bala'in sonki tace''haba nawan dan allah kai wani abu akai nifa na kosa naxo gdanka muyi rayuwar aure mai kyau dan gaskia na gaji da rayuwar da muke ba aure a tsakaninmu yace " shknn babyna amma nafi son mu samu kaman 5months saina samu alhajina da maganan tace " to shknn saida safe.

Yaune na cika sati biyu da auren kaddaran da akai mun da ya hakim kasancewar yau asabar ce xaune yake yana karatun jarida naxo na tsaya nace" malam kana sane da cewa monday xan fara xuwa sch ko daga kai yayi ya kalleni sama da kasa yaci gaba da karatun sa nace malam magana fa nake maka kai banxa dani saiya dago kai a fusace yace" ke karki dameni bakin fadi maganarki ba kije sai nayi shawara akai nace" har saika yi wata shawara ko, kinga wuce ki bani wuri banson surutu kin wani tsayamin akai sai kace wani sa'an wasanki nace" oho nidai na fada maka xuwa ba fashi na juya ina rangajin masifa shi kanshi saida abun ya bashi daria amma haka ya gimtse ya cigaba da karatun shi.

Yau kasancewar monday ne da wuri na kammala aikina na shirya nai shigar wani material pink colour doguwar riga rigar mai A shape yai matukar amsata na yafa gyale akaina na fito falo na xauna nagansa yana brkfast daga idonsa yayi ya kallen yace ke kuma sai ina? Tambayar taxo mun wata iri na juya na kalle shi nace" ka manta inda xani yau sai yace ban sani ba amma ina so ki sanar dani a xuciata nace" lallai ma wannan mutumin akwai shida rainin wayo danma ya samu ana sanar dashi shine yake so yayi ma mutum iyayinsa daya saba" shirun da yaji nayi yace" tunda baki da niyyar amsawa saiki koma ciki abinki bakin ciki duk yabi ya dameni gashi nama rasa bakin magana nakai kusan 10 minute a tsaye lokacim shima ya kammala brkfast yasa kai xai fita nai karfin hali nace" ya hakim juyowa yayi yana mun kallon rainin daya saba yace" kingama tsayuwar na xata xaki samu kamar awa daya kina tsaye ya kuma cewa" yace baki shirya tafia ba tunda kikai irin wannan shigan kina ganin xan barki ki rika fita da shigar da kika ga dama ne sam baxa ki jamin zagi a gari ba da kuma wurin su mami saboda haka idan kina son karatu ki sake shawara karki ga ina miki haka ki xata kishin ki nakeyi a'a xanyi hakane danna kare mutuncina tunda mutane da dama sun san akwai aure tsakaninmu, daga yau na miki iyaka da irin wannan shigan kuma ki fita matukar kina cikin gdan nan a matsayin matata ke koma inane na fada miki xabi ya rage naki tunda yake maganar kallon sa kawai nake yi a xuciata nace" lallaima ya hakim yadda naci burin karatun nan yace sai dai na barshi ba xai yiwu ba " haka na koma na saka hijab nasan dama saboda shi yake magana mutum kenan sai allah, kana so naka ya shiryu amma kai kana lalata na wasu allah kyauta. Harna bude sabuwar mota na wanda abba ya bani xan shiga yace" daga nan bance ki wuce ko ina ba inba hala ba ranki xai baci ko kallonsa banyi ba balle ya samu amsar tambayan sa.
Chapter 6 · 0% Book details