← Book details Hadin Zumunci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 9

Sashe 7

Hadin Zumunci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aisha💞
[6:17PM, 21/12/2016] ‪+234 701 725 1433‬: 🐾🐾HADIN ZUMUNCI🐾🐾
Written by Aysha Gana
70------------------75
***********************
Washe gari tunda nai sallan asuba ban farka ba sai karfe 9 na shiga wanka nayi tare dayin brush na tsala kwalliya cikin wata red super wax dinkin yamin kyau sosai kitchen na nufa nomin samarwa kaina abun da xanci. A falo ma sameshi shingide jikin kujera three seater yana kallon tv ko kallonsa banyi ba balle ya samu arxikin gaisuwa kallo ya bini dashi yadda yaga ina rafia kaman baxan iya taka kasa ba. Kitchen din ya hadu sosai babu abinda babu a kayan abinci, ba wani abu mai wahala na dafa ba illa chips na soya da kwai na gasa bread na hada da ruwan lipton ina gama wa na diba na xuba a plate na wuce falona ina cikin yin brkfast dina har na kusa gamawa sai kawai ganin mutum nayi ya tsaya min akai kamar wani soja yace" ke baki da kunya ko, baki iya gaisuwa ba nai banxa dashi yace " dake fa nake magana kinyi bnxa dani nace" au ashe dani kake aiban sani ba.... Ke! Ya dakamin tsawa ba rashin kunya na tambayeki ba na kalleshi sama da kasa nace kaso rashin kunyar tunda kaxo inda nakr, sai yace" ina brkfast dina? Ni mai aikinka ce daxan dafa maka na kawo maka tabdi ba dai aimana ba idan ka matsu sai dai kaje ka diba da kanka ni ba abinda ya dameni yace" amma xan iya kawowa kici ko? Nace kwarai kuwa tunda aka ajeni cikin kadararren gdan nan dole a nemo a bani saiko yace, dama irin wannan gdan bai dace da irin kuba sai yai ficewar shi yana ta surutu, kitchen din ya nufa dole tunda ba yanda ya iya.
Tunda yake a rayuwarshi bai taba shiga kitchen ko saboda daukar cokali ba amma sai gashi wai shine ya shiga dauko abinci lallai dole ya dauki mataki. Yana gama abinda yake ya shirya sai dai jin tashin mota naji ina fitowa naje na tsabtace inda na taba a kitchen na dawo falo nai kwanciyata akan kujera ina karanta littafin " ko wani tsuntsu" na ummu nass nayi nisa cikin karatun sai naji bugun kofa da sauri naje na bude saiga yasira da wata kawarmu na makaranta faty nace" na xata baxa kuxo bane ai faty tace" kinsan ba'a xuwa gdan amare da wuri saboda kar a katsemusu hanxari nace" wani irin hanxari kefa yar iska ce nan dai muka yi ta hira har girkin rana suka mun favorite food din ya hakim suka yi sai wajen yamma suka mun sallama nan na cika su da kayan kwalliya bayan tafin sune na dawo nayi kunun aya yaji madara na ajiye a falo na shiga dan nayi sallah aiko ya hakim yana shigowa da yunwar shi ya nufi kitchen ai kuwa yaga abunda yafi so nan ya xubo a plate ya fito falo nan idonshi ya sauka akan kunun aya na ai kuwa ya dauka ya kafa bakin shi ya hau sha harda lumshe ido kamar ance na fito aiko na hangoshi ina karasawa na wafce a hanun shi nace" sannu mai bakin sha maiyasa inda kaje baka sa an maka ba tunfa safe kuke tare saini baiwa ko to baka isa ba dariyar mugunta yayi yace" kinsan ita din yar hutuce kuma nasan ina da mai aiki a gda shiasa ban damu ba haushi ya kamani nace an daiyi asara ba abinda aka iya sai dai bin matan bnxa ya isa haka karki kara furta mummumam kalma akan matar aurena na fada miki nace" oho dai inka isa gbe a daura muku aure yace karki damu indai zinat ne kamar na aureta ta shigo gdan nan nace" tobta shigo mana ai ba'a kaina xata xauna ba kasan sai kana son abu kke kishin sa niko ko a jikina ina ruwan kallo da gajia kama daukota ku riqa kwana tare karshen soyayya kenan nayi tsaki na wuce dakina.

Aisha 💞
[6:17PM, 21/12/2016] ‪+234 701 725 1433‬: 🐾🐾HADIN ZUMUNCI🐾🐾
Written by Aysha Gana
80-----------------85
*********************
Ban dawo gdan ba sai karfe uku, falo na yada xango nai kwanciyata saboda ban jin yunwa nan barci yai awon gaba dani kiran sallahr la'asar ne ya farkar dani na mike nai hamdala ga ubangiji toilet na shiga na watsa ruwa hadi da dauro alwala na gabatar da sallah. In banda dole ba yanda xa'ai na shiga kitchen yadda na gajin nan amma sarkin masifan nan yana shigowa yaga table empty sai a sauko mun gonar masifa kwando kwando, aini aimana haka allah ya jarabeni da wannan rayuwar *HADIN ZUMUNCI*ko bata xumunci kana xaman xamanka a hadaka da alakakai kai magana ace kacika rashin kunya sai kace kaika kawo rashin kunya dunia ni wlh auran nan ba Karamin takura ni yayi ba kullum kana xaune a gda a jabe kaman kayan wanki in dana godema allah ma karatun dana ke xai rika ragemin bakim cikin danake ciki, ga dai gda har gda amma maigida babu halin kirki allah ya sauwake.
Tare suka shigo shida abbakar da wani abokin sa lawan ina xaune ina naxarin wani littafi sai jin sallamar shi nayi da kyar na amsa ya shaka soaai yace " sallamar ma saikin ga daman amsawa sai kace ba musulma ba ko kallan shi banyi ba hakanne ya kara sashi jin haushi, dama shi ya tsani yai magana a share shi muguwar tsawa ya daka mun saida hanjim cikina ya motsa nan hankalina ya dawo jikina ban nuna masa naji tsoro ba cikin gadara yake magana " ina abincin da kika dafa nayi baki ki xubo ki kawo musu raina ya kara baci nace" kaje mana ka dauka ko nan nake ajewa salon neman magana baka san inda kke xuwa ka dauka bane ko me yace" ke nake so ki kawo nace" nifa baxan fito ba saboda nima kuku bace sa'annan ba mai aiki aka kawo maka ba balle kace saina maka abinda ranka yake so, dan ma ka samu ina dafa maka shine kake wani daka mun tsawa sai kace wata yar cikinka cikin sauri yace " insha allah yar cikina bada tamun haka ba nace" oho dai kaika sani a tafi abani wuri kar a samun ciwon kai gda shiru daka dawo shikenan sai fada yace " to ki koreni mana ko kuma daga yau ki hanani shigowa cikin gdan idan naki ne, nace" oho yarage naka kuma.......... Haka ya hakura ya dauko musu da kanshi sai ganinsa suka yi niki-niki da tray abbakar yace "a'ah abokina ina madam din take na ganka haka ya hakim yace" ai ta riga tai bacci kasan taje sch ta gaji sannan ga aikin gda yayi haka ne dan kar lawan ya gane lawan yace" kasan mata akwai su da saurin bacci balle idan sukayi aiki sun gaji, kai allah yai ma mata albarka abbakar yace" amiin shiko ya hakim a xuciarsa yace wasu matan ba ,banda irinsu aimana wanda basu san darajan aure ba.

Aisha💞
[6:17PM, 21/12/2016] ‪+234 701 725 1433‬: 🐾🐾HADIN ZUMUNCI🐾🐾
Written by Aysha Gana
85----------------90
*********************
Yau kusan watana biyu kenan da aure amma babu abinda ya taba shiga tsakaninmu na dangantakar data shafi aure, sai dai kawai yai harkar gabansa nayi nawa.

Yau lahadi ce zaune nake shawar taxo mun ya kamata naje gdan mami tunda shi baida tunanin da zaice naje, gashi har mami tayi fushi dani ta hana kowa xuwa inda nake gashi ba halin kiran waya ya dauko min waya ya canxamin sabuwa da sabon layi haka nake xaune kaman kifin rijiya ban kira ba'a kirana.

Zaune yake a falo ya daura kafa daya akan daya waya ma yake amsawa yana hangoni ya hada rai karasowa nayi, yakai minti goma yana waya naga dai baida niyyar saurarata saina samu kujera na xauna naga ikon allah kana ganinsa kasan cikin nishadi yake kuma da mace yake wayar saboda gabadaya ya mayar da hankalinsa kan wayar, amma dan rashin mutunci irin nashi yana kallona harda kara kashe murya yana jefa mata kalaman soyayya masu xafi, xuciyata ko taxo mun iya wuya gashi dukda ba sonshi nake na amma na tsinci kaina da jin xafin abinda yaimin ni gashi ban isa nai haka ba.
Na gaji nace''ya hakim wannan wane irin wulakanci ne tun tuni naxo ina son nai maka magana kai bnxa dani saboda kana waya da wannan bnxan yarinyan nan kasan allah taraka kawai nakeyi duk abinda kakemin akan wannan karuwar ko....... Tsawa ya daka min yace" daga yau idan ina amsa waya karki kuma xuwa inda nake karuwar da kike magana akanta tafi mun ke tsaki yaja ya wuce.
Nan take kukan bakin ciki ya subuce min wannan wace irin rayuwace wai mijin auranka shine yake amsa wayan yan mata a gabanka kai wannan rayuwa da nake ciki ni aimana allah ne kadai xai fidda ni dakina na shiga kai tsaye toilet na wuce nayi wanka kwalliya nayi cikin less baqi mai ratsin golden kudi na dauka sannan na fito na shiga motata na fita kai tsaye wani super market na tsaya nayi wasu mami tsaraba ina shiga gdan da sallamata yasira na gani tace" aimana kece a gdannan nace" ke wlh bnxa ne idan bani bane to waye nan dai ta rakani na gaida su mami sannan muka wuce daki yasira tace "kin ganki kuwa ko dai mun samu baby ne nace " zaki fara iskancinki ko tace" gaskia yaya ya iya kiwo kiga yanda kikayi fresh gaskia cikin nan ya miki kyau nace" da kyau likita harkin gano ciki ne dani ni aimana allah sauwake nandai yasira tai ta tsokanata ta nace kedai kika sani karfe biyar nayi mami tace inxo na tafi haka suka rakoni wajen motata na shiga.
Chapter 7 · 0% Book details