← Book details Dan Shaye Shaye Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 29

Sashe 2

Dan Shaye Shaye Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Futa tai tanata masifarta ita kad'ai
Sai wajen 7:30 sannan Dr Tahir yafara dudduba marasa lpyr dasuka kwana, nan yashiga danya dubata yaga tana bacci.

Mamakine yakama sa dan yakamata ace yanzu tafarka, duba record d'in baya yay yaga an'kara mata allurar baccine, nan yatambayi waye yayi mata, Nurses d'in dasuke wajen sukace basu bane.
Dubawa yay yaga babu ingozi
Tambayarsu yay tana ina..
Sukace tana emergency room.
Sawa yay safeeya takirata sannan yafara duba wasu nad'ayan d'akin lokacin dasuka iso harya gama zai koma.

Tambaya yafara jefo mata..
"Who assign you to inject her...?
" Sir, sheee...e.....e.

Maganar tace tafara rawa dan babu alamar wasa akan face d'in sa.

"Sir" she start asking me about fruit "
"But I don't know which fruit she is asking for. "
" I tried my best to explain her"
"But she couldn't understand"
"this is the reason why I inject her "
Da'kar ta iya gaya masa hakan

"is this the reason"
"Yes sir"
"Last warning "
"Okay 👌 Sir "
"Leave"

Futa tai tana 'kun'kuni ranta duk ya 6aci
Dubata yayi sai yaga bama mai 'karfi tai mataba dan haka yabar wasu nurses din anan shikuma yacigaba da duba sauran d'akunan na marasa lpyr.

Saida yagama sanann yashiga d'akin dayabar Fawass akwance.
Zuwa yay yasamesa yana karatun Al'kur'ani mai girma.

Girgiza kai yayi yazauna kusa dashi saida yakai aya sannan yace masa kasan meka aikata jiya kuwa...?

'Dago kansa yay cikin alamar neman sani🤔 yace Menai kuma nidai naga abubuwa suna dawomun kamar a........ ✍🏻✍🏻✍🏻

*Keep waiting my fan's....* 🠠񚐾񬀊 *Mr's Hallsad ce....💖*
*Omh teemerh_🌹*

*Gamasu san sufara biya da wuri saiku tun tu6i wannan number 08032762588*
*_Idan kuma ta account ne_*
*_Acc 0110015052_*
*_SADIYA ABDULLAHI UMAR_*
*_ECOBANK_*

```Idan kuma katin wayane na
#400 ne kachal```
```Comment section kuma
#200 ne kachal wannan sau'kine agareku
My special group kuma
Da```
*'Dan shaye shaye ne* 🍾
*Am 16 years old* 💃🏻
*Sanadi* 😭
```Duka #400 ne zaku biya wannan kyautar girmamawatace agareku saboda comment d'inku mai sharhi yana burgeni, yana sani nishad'i wlh, Idan banga comment dinku ba harjina nake wani iri, inayinku wlh🥰🥰.
```
[01/10, 8:51 PM] Omh Teemerh 🥰😘🥰: _*📲 TYPING📲*_
_*"🍾DAN SHAYE SHAYE NE🍾*_
_*paid book #300 only*_
_*By*_
_*OMH TEEMERH*_
_*👑THE QUEEN OF THE WRITER'S👑*_

🤍🤍🤍🤍⚜️⚜️⚜️🤍🤍🤍🤍
_*DASHEN🌲ALLAH*_
_*WRITER'S 📖 ASSOCIATION*_
******************************
*'KUNGIYAR DASHEN🍃ALLAH* _'kungiyace tajajur tattun marubuta kuma tsayayyu masu aiki da ilimi wajen rubutunsu_
*Dan ganin sun kawo muku labari wanda zai wa'azantar daku ilimantar daku, fad'akar daku, kuma ya nishad'antar daku*
*AL'KALAMI✍🏻 YAFI TAKOBI🗡*
******************************
🤍🤍🤍🤍⚜️⚜️⚜️🤍🤍🤍🤍

_*WANNAN BOOK TUN DAGA FARKONSA HAR 'KARSHE SADAUKARWACE AGAREKI AUNTY ZAHRAH*_
_*FATIMA ZARAH*_
_*BLOODY NAH*_
_*🥰🤍🥰*_

5️⃣⏹️⏹️6️⃣

.............Mena aikata kuma nidai naga abubuwa suna dawomun kamar amafarki...!?
" OMG.... "
FAWASS......!!! yafad'a da 'karfi, yana had'e rai, Kallonsa Fawass ya'karayi yana jiran mezaice masa.

Jiya Menene yasameka harka shagiya sosai kaje kabuge yarinyar mutane tasuma, ri'ke kansa yay yana tunano abubuwan dasuka faru....

"Yasalammm" yace cikin sanyin murya "mena aikata.....?
Tahir gaya masa komai yayi sannan yagaya masa halin da yarinyar take ciki yanzu....

"Ya rahaman...... "
"Tashi muje....! "
Tashi Tahir yay suka futa, direct d'akin da aka kwantar da yarinyar suka shiga, har lokacin tana bacci bata farkaba, dubata suka 'karayi sannan suka zauna can d'ayan gadon da babu kowa akansa.

Tahir ne yakallesa yace meyasaka kasha giya jiya nasan dai ka kwana biyu bakashaba, amman ya akai jiya kasha....

Runtse idansa yay yana tuno abunda yafaru, badan Tahir bane ba dabazai fad'awa kowaba amman babu yadda ya iya zaigaya masa dan shid'in kamar d'an uwa yake agaresa.....

Lumshe rikirkitattun idanunsa yay yacije tattausan 💋 lips d'insa na'kasa sanan yace "Jiya da yamma bayan nabar Hospital d'in nan kasan naje gida...?
"Ummm"
"Sai nai part d'ina batare danaje wajen part d'in hjy Hindatu ba...!!!

" Ina shiga nafara rage kayan jikina dan inasan inyi wanka indawo dawuri sbd munyi waya da Dr Mu'azz zaituromun sa'kon Alluran danai oder, to nasan yanayin lokaci kana taka Allah na nasa saina kirasa nace idan bai sameniba yabaka, komai yayi maka bayani inkuma mun had'u shikenan..
"Yace too..!
"Ina gamawa nayi bathroom danyin wanka sainaji motsi a bedroom d'ina, naji mamaki sosai dan nasan babu wanda yakeda key d'in part d'ina, koda masu aiki basa dashi dagani sai NASMA itama sbd itace take gyaramun shiyasa, dan haka nagyara zaman towel d'in dayake d'aure a 'kuguna na murd'a handle d'in d'akin nashiga..

"Inna lillahi wa inna ilaihi raju'un, abunda nafurta kenan ganin IKILIMA da wani 'katon saurayi suna aikata alfasha akan bed d'ina wannan abun yayi matu'kar gigitamun 'kwa'kwalwa, dan haka najuya nafuta, tunda har lokacin basu san nashigoba...

Futa nai nazauna akan 1sitter ina runtse idona,na jingina kaina akan kujerar bayan kamar 9m dafutowata sai naji suna 'kyal'kyala dariya suna fad'in komai yayi dai² suna tafawa.....

Jinai tace "Gobema kadawo kaji, wannan shasha Shan d'an shaye²ⁿ bazai gane anshigoba zan gyara masa komai kafun nafuta, kaga mun huta da zuwa hotel ma nan ya ishemu kohhh...!!!!

"Kwarai kuwa tunda tsawon 3week’s kenan muna zuwa ba'a ta6a kama muba kinga kud'ina ma yahuta nakama d'akin da nake kullum a hotel....!!!!

"Aikam baby saikana bani kud'in kooooo.....?
Hakane kam yanzuma zan yimiki transfer d'insu dan kin cancanci hakan harma fiye da hakan.......

Dariya suka saka suna shewa, hakan yasani jin zafin abunda naji tana fad'a, kenan wannan bashine nafarkoba, sannan kuma nine shasha shan d'an shaye²....

Tashi nai nabanka d'akin rai a6ace, abun takaicin har lokacin, ita bata saka kayaba, amman shi yasaka komai nasa kamar basuyi komai ba....!!

Duka nafara kai masa saiya kauce, na'kara kai masa duka sai taja towel ta d'aura, tanayo inda muke tsakiya tashiga tana fad'in wlh ka'kara dukan sa saina d'au *MATAKI* ...!!!

Kallon tanai cikin mamaki nace " *MATAKI KUMA..!!?*
Tabbass ko kana tunanin bazan iyaba...!!
"Matakin me zaki d'auka dan ina dukan wanan d'an iskan shine zaki d'auki mataki, to bisimillah...

Hhhh tasa dariya tana fad'in d'an iskaaaa... Kace fa.....
Aigwara shi kaida kahad'a biyu ga bin matan banza ga shaye sheyen d.......

Ban bari ta 'karasaba cikin zafin nama, wlh bansan lokacin dana d'auketa damariba...
Fad'uwa tai, sai ta tashi tace wlh zakai nadamar wanan marin dakai mun...

Kiran kwarton nata tai tabud'e sirrin tacciyar 'kofata tacikin d'akin tace yagudu....

Nikam mamaki nakeji dan bansan ya akai tasan da wanan 'kofar ba...
Ina cikin wanannmamakin ma yasa banje nabisuba.....
Ina tsaya dan jiran tadawo sama da minti 10 amman shiru zama nai abakin kujerar dressing mirror na inajiran dawowarta...!

Dan nai alkawarin dukan ta yau sosai, koda hakan zaisa Hjy Hindatu tazageni.
"Dan basau d'aya ba, basau biyu ba, ansha zuwa ana gayamun Ikilima nabin maza, idan nagayawa Hjy bata yadda saitace naiwa 'yarta sharri.

Ko kuma idan naje gayawa Abbie tace yau ma ansha an bugune za'aiwa "yata sharrin da'aka saba, tunda tafad'a maka 'karya ko....
Muna fiki kawai, wlh Alhaji 'karya yakeyi, haka zata 'karyatani agabansa, shima Abbie saiya yadda yace ba'a yadda dazancen d'an shaye²....

Wanan shine kalaminta da zarar nafad'i wata kalma akan yaranta...
Kuma Abbie ya yadda...

Ina cikin tunanin nan sai naji ana nocking sosai da 'karfin gaske, yadda kasan za'a ciremun 'kofar parloun, futa nai dasauri ko itace tadawo tanan, amman sai naga Abbie da Hjy Hindatu ina bud'ewa, ganin fuskar Abbie babu annuri shida Hjy Hindatu yasani shiga cikin kokonto.....

'Daukeni da mari Abbie yafarayi yana cewa tana ina....!!!!!!!
Tana inaaaaa nace maka.....!!!!!!
"Janyomun kwalata Hjy Hindatu tai tace dan ubanka ina "yata take, ina fatan baka keta mata haddiba dai kooo........?????

"Haddi kuma.......?
"Au tambaya kake, kajimun mara kunyar 'karya, shegen yaro, d'an shaye² kawai......!!!
Wani abu naji yadakarmin 'kirji sosai nad'ago idanuna dan tambayar wasuke nema, amman banyi auneba naji wani saukar Marin, dafe wajen nai ina sake d'ago kaina danyin mgn..
Wani saukar marin na'karaji, kafun nayi wani motsi naji wani.....

Ba magana nake makaba Fawass ina Ikilima take dan uwarka....
"Tunda bata baka tarbiyyaba shine zaka 'ketara 'kanwarka ubanku d'aya da ita...

"Kenan bayan shaye² harda zina ka had'a, kai fasi'kine dama, ina ganin wanann 'kaddarace Allah yajarrabeni da ita na fara shaye²ⁿ nan naka ashe kace harda zinama zaka fara..
wa'iyazubillahi Abunda nafurta kenan.....!!
Au kajimun d'an iskan yaro Alhaji mune shed'anun kenan ina kakaita nacee......!!!

Kuka Abbie yasaka yana 'kara shararamun mari yace ina kakaimun yarinyata.....
Bari inje induba tunda nagakai bazaka ganeba danba kaine kad'auki cikin nataba tsawon wata 9 dazafi da sanyi da damuna duk ban gajiyaba, nai mata tarbiyya tsawon shekara 22 amman yanzu ka kasa magana ma wanan d'an iskan d'an shaye²ⁿ yanuna maka Ina yasa ta tunda yayi mata fyaden, da Nasma ce ai bazaka bisa ahankaliba amman dayake "yatace shiyasa kakebinsa sannu sannu...

Shiga tafarayi tana dubata, d'akina tashiga shikuma yajawoni yayi wajen d'akin dani yana kaimun naushi yana cewa ita take....!!

Har bakina yafara futar da jini amman nakasa koda motsine dan nakasa gane kan komai wlh.....

Muna shiga d'akin muka tarar da Ikilima akwance akan gado gawani jan abu yana zubowa ta'kafarta tana kuka sosai kamar nagaske.....

Inna lillahi wa inna ilaihi raju'un....
Nashiga uku Alhaji yayi mata fyad'e zokagani....
Wayyooo Allah naaaa wlh yacutar mun da yarinyata, yagama illata mata rayuwa......

Wayyooo Allah naaaa...
Yanzu waye zai aureta yakashe mata rayuwa
"Dan uwanka ya illataka wannan ai masiface wlh, najikinka yacutar dakai....

Allah ya isa tsakanina dakai, duk halaccin danai maka nari'keka tsawon shekara 11 amman da wanan zaka sakamun.....

Ita tambad'ad'd'iyar uwar taka tuda ta tafi aiharyanzu bata dawoba haka tabarku kaida Nasma inashan wahalarku, amman karasa dame zaka sakamun saida wanann kooo, Allah yatsine maka Albarka, daman menene amfanin ajiye d'an shaye² acikin gidan ma'aurata, wata ranama aisainima yace zai ketamun haddin...

Kama Ikilima tai tana cewa tashi muje kigyara jikin ki akira doctor yazo yadubaki yaga idan kina da ciki azubar dashi dan wlh bazan lamuntaba, abarni da wannan kayan ba'kin cikin ma, naketa miki haddi dayay, wlh da da aure tsakaninku saika aureta, mema zanyi da shegen d'an shaye² kawai ...

Alhaji ka kira Doctor yazo yadubamun yarinya, Tunda ba'asan tun yaushe yake mata hakan ba, yaunedai Allah yabata sa'a ta tona masa asiri.....

Shikuwa Abbie mutuwar tsaye yayi yana fad'in kacuceni wlh kacuceni Fawass Allah yasaka miki Ikilima...
Chapter 2 · 0% Book details