← Book details Daga Taimako Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 11

Sashe 7

Daga Taimako Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abdulmajeed dake kwance a kasa a sume,ji yayi an yayyafa mishi ruwa ahankali ya bud'e idonsa,ganin bai ga kowa bane yasa ya mik'e aguje yana bubbuga gidan Ayuba,Surayya da Ayuba da jikinsu tun a lokacin bai bar rawa ba,suna dunkulle awaje d'aya,jin da suka yi an k'ara bubbuga gidan ne yasa suka wage baki suna adduoi Ayuba na karanta Laqadjaakum,Surayya na karanta Fatiha Dan ba k'aramin tsorata suka yi ba Dan har a lokacin suna jin guje guje asaman kwanu,Abdulmajeed da shima a mugun firgice yake ganin babu alamar za a bud'e k'ofar ne yasa ya hau k'wallawa Ayuba kira yana yazo ya bud'e masa shine Abdulmajeed,cak Ayuba ya tsaya da karatun da yake,ya kasa kunne Dan kamar sunansa yaji ana kira,muryar Abdulmajeed ya jiyo yana Kiran sunansa,da sauri ya raba jikinsa Dana Surayya ya mik'e yayi waje Surayya sai kiranshi take ya dawo,Abdulmajeed
kuwa waige waige kawai yake yana kiran sunan Ayuba ga tsanin tsoro ga wani gudawar da yake ji,Ayuba na bud'e gidan ya shige da gudu,Ayuba kuwa yayi sauri ya rufe gidan,a tsakar gida ya sameshi yana kai da kawowa, " Abdulmajeed Lafiya kuwa daddaren nan waye ya koro ka"? Ayuba yace yana kallon gajeran wandansa dake Neman sub'alewa daga jikinsa "Ayuba bani touchlight na Shiga band'aki tukuna kashi nake ji" Ayuba d'akinsa ya shige ya tarar da Surayya a zaune akan gado duk ta had'a zufa sai ajiyar zuciya take Dan sai da ta jiyo muryar Abdulmajeed hankalinta ya kwanta,Touch light d'in dake gaban mudubi ya d'auka yayi waje da sauri Abdulmajeed ya k'arbi touch light d'in daga hanun Ayuba ya shige band'akin Dan ginin Gidansu iri d'aya ne kasancewar haya duk saka kama,yana hawa kan Masan yafara sukurkuta gudawan,Ayuba ciki ya koma ya zauna a gefen Surayya aikuwa suka jiyo karar sauk'ar gudawan Abdulmajeed ji kake "buut bubut" Surayya mai zata yi in ba dariya ba har da rik'e ciki,Ayuba shima duk yanda yaso ya gintse dariyar da ta taho masa kasawa yayi sai da ya saki dariyan,Surayya kasa tayi da murya tafara maganar " Ayuba duk yanda akayi Aljanar nan ce ta tsorata Abdulmajeed shi yasa kaganshi daddaren nan gashi sabida tsorata da yayi bar da su gudawa Ashe Muhibba ma ta fishi jarumtaka"Surayya tace tana k'ara kyalkyalewa da dariya,Ayuba shima kasa yayi da murya yace " aikuwa inaga aljanar ce ta koro shi Dan babu Riga a jikinsa da gashi sai gajeran wando" Abdulmajeed Sai da yayi minti goma sha Biyar a band'akin kafin ya fito,yana sauke ajiyar zuciya,Ayuba mik'ewa yayi, ya yi hanyar waje,palo ya bud'e yace wa Abdulmajeed bismillah,tare suka shiga palon, Abdulmajeed ya ajiye touch light d'in hanunsa yacewa ya Ayuba taimaka masa da Riga ya sa,Ayuba d'akinsa ya koma ya d'auko masa doguwar Riga Surayya kuwa ta biyoshi Dan tace bazata iya zama ita kadai ba,zura rigar yayi ya zauna,Ayuba yace "Abdulmajeed ina jinka mai ya faru,"

" Ayuba Allah ne yayi ina da sauran numfashi agaba da tuni kaji labarin na mutu tun k'arfe 11 Aljana ta sako ni agaba ina zaman zama na Muhibba ta janyo min" ba irin gargadin da ban mata ba akan tasan irin wayanda Zata na taimakawa tana Sanin irin wayanda zasu na na shigar min gida Sai gashi ta janyo min masifa D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO,"Subhanallahi kace abinda ya faru kenan,Allah ya tsare mu da tsarewarsa ya kare mu daga sharrinta" " Ameen kai dai ai naga masifa wlh har k'ofar gidanan ta biyoni Allah Ayuba ba Dan ina da dauriya ba da tuni na mutu," "innalillahi wa inna ilaihi rajiun Allah ya tsare mu kace ba k'aramin tashin hankali Muhibba tagani ba" Ayuba yace yana girgiza kai,"yanzu ya zaka yi Abdulmajeed? "Ai Ayuba barin gidanan ya kamani ana iddar da sallahr asuba zanje gidanmu in fad'awa Mahafina bazan iya zama agidanan ba gaskiya"Katse shi Ayuba yayi yace " aa ba haka zaayi ba dudu watanku biyar a gidanan Sauk'ar Qur'ani za'ayi a gidan insha Allahu aljanar zata bar gidan," "hmm Ayuba kenan Dan ba Kai ne kaga aljanar ba da wallahi kai ma barin gidan zaka yi.

Ana idar da sallar asuba Abdumajeed ya k'arbi kud'i awajen Ayuba Dan yace babu abinda zai sa ya k'ara shiga gidansa babu yanda Ayuba bai yi ba akan ya Shiga gidan zai raka shi ya d'auko machine d'insa ya hau bai kamata ace yana da machine yaje ya hau adaidata sahu ba,fir Abdulmajeed yak'i da gashi sai doguwar rigar da Ayuba ya bashi da Dari biyar d'in da ya k'arba awajen Ayuba ya dau hanyar bakin titi,sai da ya samu awa d'aya abakin titi bai samu abun hawa ba,Dan gari bai gama waye ba,wani adaidaita Sahu ya hango daga nesa ya taho ta inda yake,hannu biyu ya d'aga yana "wait wait ",adaidaita sahun sai da ya d'an wuce shi Kafin ya tsaya ,da sauri ya k'arasa inda adaidaita sahun yake yahau yacewa mai adaidaita Sahun " kofar nassarawa zaka kaini,"mai adaidata sahun bai ce komai ba ya ja suka tafi,juyawa yayi ahankali ya kalli gefensa,wata matashiyar buduruwa ce a zaune agafensa faraa ce tas Dan farinta har d'aukan ido yake,bak'ak'en kaya ne ajikinta,babu abinda kake gani sai hannyenta Dan kanta ma anad'e yake, ta kau da kanta tana kallon gefe, ,Abdulmajeed gabansa ne yayi wani irin fad'uwa tsoro ya rufeshi yana tunani ko aljanar ce ta biyoshi,matsawa yayi nesa sosai da ita gabansa na fad'uwa ahankali ya lek'a k'afarta yaga shima arufe,har a lokacin tana kallon gefe bata juyo ba,Abdulmajeed madubin adaidaita sahun ya kalla dake , saitin ta, Aljanar nan ya hango ta mudubi ta sakar mishi murmushi hakoranta amadadin jajjaye bak'ak'e ne ma su tsini Kamar allura,"wait wait anan zan sauk'a," Abdulmajeed yace agigice adaidaita sahun bai gama tsayawa ba ya duro daga adaidaita sahun ya sa gudu,mai adaidata sahun aguje shima ya bishi ya rik'e mishi Riga yana "ya zaka gudu kabani iya kud'in Dana kawo ka nan"Abdulmajeed doke hanunsa yayi yace " cikani Dan ubanka aljana ce acikin adaidaita sahun ka""Al me"? "Aljana" Abdulmajeed yace yana k'ara dibawa aguje,abin mamaki Mai adaidaita sahu ne gaban Abdulmajeed yana ta zuba gudu,duk Wanda ya tambayesu akan mai suke gudu,suna cewa aljana ce shima zai diba aguje.😂😂😂😂😂😂😂
[9/22, 12:18] Sadnaf: 🙆🙆 *D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO*😭😭

*Written by*
💅💅 *SADNAF*💞

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l

*TRUE LIFE STORY*

🙆🙆 *D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO*😭😭

*Written by*
💅💅 *SADNAF*💞

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l

*TRUE LIFE STORY*

Aunty Fannah kisa

*#[email protected]*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*

PAGE 8

*wanan shafin naki ne ke kadai Auntyna (Aunty sis* 💞) tnx for your love and support

*Jinjinar ban girma gareku*,

*Zauren* *Adda Bena*
*MieMiebee* 👄 *Novels 2*
*Musha karatu na Ybk inasan yanda kuke comment Kuna yi ina jin dadi dafatan babu wacce ta saki fitsari awando garin dariya*

😂😂😂😂😂😂😂

Wani dake zaune a can gefe da duk abinda yake faruwa yana gani adai daita sahun ya fara lek'awa Dan yaga ko wani abun ne aciki shi yasa suke gudu, babu abinda ya gani acikin adaidaita sahun ,da gudu ya bi su Abdulmajeed,ya kamo Mai daidaita sahun da tsabar gudu kamar ya tuntsira,Mai adaidaita sahun juyowa yayi afirgice, mutumin ya tambayeshi mai ya faru suke gudu,da sauri mai adaidaita sahun ya gaya mishi yana Neman kwace rigarsa daga hanun mutumin Dan tunda ga lokacin da ya tab'a mak'ala earpiece a kunensa ya shiga band'aki yana jin waka,yaji an sharara masa mari,yake tsoron aljanu ko sunansu yaji sai ya tsorata,mutumin kwantar masa da hankali yayi yace ya kwantar da hankalinsa ya lek'a adaidaita sahu babu komai,mai adaidaita sahun mukulin adaidaita sahun ya bashi yace masa Dan Allah ya taimaka masa ya d'auko mishi adaidaita sahun shi dai tsoro yake ji.

Abdulmajeed sai da yayi nisa sosai ya tsaya gabad'aya ya gama tsorata,bus ya Tara ya hau Dan bazai iya kuma hawa adaidaita sahu ba,hankalinsa ne ya kwanta da yaga bus d'in acike,ajiyar zuciya ya ringa saukewa yana bin mutanen cikin bus d'in da kallo in banda zare ido babu abinda yake yi.

Muhibba kuwa aranar barci bai ga idonta ba dan kasa barci tayi,tunda tayi aure bata tab'a raba shimfid'a da Abdulmajeed ba,gashi yau sabida tashin hankalin da masifa da Aljanar da ta taimakawa ta sata yasa ta zo cikin kanenta ta kwanta,kewar Abdulmajeed ne yabi ya dameta tana tunanin yau ko mai yaci,tasan tunda bai zo ba,bai kuma kira awaya ba tasan bak'aramin fushi yake da ita ba,dan ya d'auka karya take yi babu wata aljanar da take tsorata ta, agogo ta duba taga k'arfe biyun dare,wayar Nafeesa ta d'auko ta kuna, tayi dailing number Abdulmajeed,ji tayi yanata ringing bai d'auka ba,ahaka ta cigaba da kiransa,sai da ta gaji Dan kan ta ta ajiye wayar,kuka ta fashe dashi tana tunanin yana ganin kiran kin d'auka yayi,sabida Fushin da yake yi da ita,Dan tasan halin Abdulmajeed ya tsani yaga ya bata umarni ta tsallake,to ya zata yi, zuwa gidan shine mafita agareta Dan in ta cigaba da zama agidan aljanar Zata iya zautar da ita, ga Abdulmajeed yaki yarda da ita, dana sani ta ringa yi na Taimaka aljanar da tayi,yanzu Surayya da ta rufe k'ofarta bata bari aljanar ta shigar mata gida ba tana can hankalinta kwance babu abinda ya raba ta da mijinta,ahaka Muhibba ta zauna tana kuka tana tunani,sai da aka fara kiraye kirayen sallah ta mik'e ta nufi band'aki Dan tayi alwala.
Chapter 7 · 0% Book details