← Book details Daga Taimako Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 11

Sashe 11

Daga Taimako Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Abdulmajeed hankalinsa ba k'aramin tashi yayi ba,ya ringa kuka yana Dana sani,Mallam Isah kuwa jin fad'a ne tsakanin mutum da aljan ne yasa ya suri wayarsa ya k'ira Mallam Saminu mai Rukiyya,Mallam Saminu mai Rukiyya yace mishi dawowarsa kenan daga kauye,ai da sauri Mallam Isah ya ajiye wayarsa yace musu su zo su tafi wajen Mallam Saminu mai Rukiyya basu ga ta zama ba,ahaka suka dunguma suka nufi gidan Mallam Saminu mai Rukiyya ,basu samu ganinsa ba sai wajen Magriba,suna zama,yace suje suyi alwala su dawo,dukansu Alwala suka yi Muhibba kuwa sai addua take Allah yasa ya iya masu tsakani da Aljanar,bayan sun zauna yabi Abdulmajeed da kallo,gyaran murya yayi yace yasan mai ke tafe dasu, Dan Aljanar tariga su isowa wajensa ta gaya mishi duk abinda yafaru,Dan haka tace ya cire hanunsa a lamarin,Dan sai ta d'au fansar wulak'ancin daya yi mata,Sallati Suka yi gabad'aya Abdulmajeed kuwa ya saki tusa,kuka yasa yana ya taimaka ya bata hakuri ya daina ya tuba bazai sake ba,Mallam Isah da Muhibba ma rokon Mallam Saminu mai Rukiyya suka ringayi suna ya taimaka musu,ya bata hakuri,Mallam Saminu bai ce komai ba ya tashi ya shige d'akin sai da ya samu minti arbain kafin ya fito,ce musu yayi ya samu ta hakura dak'yar amma tace bata hakura gaba d'aya ba,zata rama nan gaba yanda masu hali irin nashi zasu daina,amma tace insha Allahu bazata k'ara bibiyarsu ba,Abdulmajeed hankalinsa ba k'aramin tashi yayi ba daya ji abinda Mallam Saminu yace,magana yake so yayi,Mallam Saminu ya dakatar dashi yace ya yi iya yinsa Dan haka yaje su dage da addua wanan kuma ya zame masa darasi,adduoi ya basu da shawarwari na hanyar da zasu bi su nisan ci kansu da aljanu,Godiya Mallam Isah ya mishi ya bashi sadaka suka fito.

A takaice washegari Abdulmajeed yaje gidansu Muhibba ya d'auketa bayan dogon nasihan da iyayen Muhibba suka musu,Dan Muhibba ta gaya musu komai suka nufi gidansu,suna isa Muhibba ta duro daga kan machine ta nufi gidan Surayya Dan tayi missing d'inta sosai,Surayya dake band'aki tana wanka ta bar k'ofar band'akin a bud'e dan tunda daga lokacin da su Muhibba suka tafi gidansu take cikin matsancin tsoro ko an kwankwasa k'ofa bata bud'ewa sai kayi magana tasan wanda ke kwankwasa k'ofa da yake Muhibba ta kagu taga Surayya buga gidan ta ringa yi da k'arfi, tuni Surayya ta wurgar da soson hanunta ta diba aguje,tayi d'aki ta ma manta tsirara take ta fara wa innahu Sulaimanu,sai da taji muryar Muhibba tana ta bud'e mata sanan ta d'aura zani taje ta bud'e k'ofar,rungume juna suka yi,suna murnar ganin juna atsaitsaye Surayya ta ringa bata labarin abubuwan da suka faru da bata nan,da irin gudawan da Abdulmajeed yazo yayi a gidansu, Muhibba in banda dariya babu abinda ta ringa yi tana rik'e ciki,anan itama ta bata labarin abinda yasa Aljanar take bibiyarsu,Surayya tsoro ne ya kamata tana Allah ya karesu daga sharrinsu.

A Daren Abdulmajeed a ango yake sak, Dan ya dirje Muhibba kamar kayan wanki to an kwana biyu ba ahadu ba, tun daga lokacin Abdulmajeed baya wasa da sallah da tashin dare,Muhibba kuwa kullum kanta a d'aure tana jin karatun Qurani.

Bayan shekara biyu Muhibba na asibiti tana nakuda,Abdulmajeed hankalinsa yabi ya tashi,sai kai da kawowa yake Dan tun cikin Muhibba na karami Allah ya jarrabce shi da San cikin,bayan awa d'aya da rabi da aka shigar da Muhibba nurse ta lek'o tace Abdulmajeed yazo yaga jaririya matarsa ta sauka lafiya,da saurinsa ya nufi d'akin,har yana Neman yayi tuntub'e Surayya na biye dashi abaya,Gani yayi Muhibba ta kau da kanta, bata kallon inda jaririyar ke kwance,bai kawo komai aransa ba,ya nufi inda aka kwantar da jaririyar,abinda yagani ne yasa yaja da baya,jaririyar bak'a ce irin k'irin d'inan,gata katon kai ne da ita, muni iya muni wanan jaririyar ta had'a,cikin tashin hankali,ya d'ago zai yi magana,Muhibba tayi sauri ta ce yayi shiru,anan ta tuna mishi abinda Aljanar tace na zata rama,shiru yayi bai ce komai ba.

A takaice duk Wanda yaga jaririyar da Muhibba ta Haifa sai ya girgiza,ahaka aka lallaba akayi suna Muhibba ta cigaba da kula da jaririyarta Dan ita bata k'i jaririyar ba,Abdulmajeed kuwa shima haka ya ringa ririta jaririyar Dan yasan abinda ya shuka shi ya girba.

Ahaka Muhibba ta k'ara haihuwar yara hud'u amma kyawawa Zainab ce dai ta banbanta acikinsu wato ta farin, Dan muni kamar ayanka a b'oye,Abdulmajeed kuwa tunda ga lokacin ya daina wulak'anta mutane,duk wanan zafin kan babu.

Anan na kawo karshen daga taimako kuskuren Dana yi aciki Allah ya yafemin.
Chapter 11 · 0% Book details