← Book details Daga Taimako Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 11

Sashe 5

Daga Taimako Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ware ido Maryam tayi tana "bangane mai kike nufi ba,taya ya kika taimakawa Aljana"? Muhibba share hawayen fuskarta tayi tafara bata labarin abinda ya faru,sallati maryam ta ringayi bayan ta gama jin labarin abinda ya faru,"muhibba mai ya kai ki bud'ewa aljana k'ofa har ta Shiga band'akinki? Mai yasa kika b'oyewa mijinki gaskiyar abinda ya faru ai dole yak'i yarda dake ya d'auka karya kike" oooo ni maryam daga taimako kin janyo wa kanki,Allah ya kareki daga sharrinta,bari babanku ya dawo ya kira mijin naki awaya ya fad'a masa abinda ya faru Idan addua za adage da yi kafin ki koma gidan dan hatsarine komawarki gidan yanzu, wuce kije d'akinku ki kwanta tunda kince jiya bakiyi barci ba" mik'ewa Muhibba tayi ta nufi d'akinsu dan barcine a idonta sosai,tana kwanciya barci yayi awon gaba da ita.

K'arfe biyar da rabi Abdulmajeed ya dawo gida,mamaki ne ya rufeshi daya ga k'ofar gidansa a kulle,parking d'in lifan d'insa yayi ya nufi k'ofar gidan Surayya dan yana kyautata zaton Muhibba a gidan take,aransa kuma yana ayyana irin rashin da zai yiwa Muhibba wato shi zai ce ko k'ofar gida kar ta fita,amma sabida bata jin magana shine zata tafi gidan makota har da kulle gida,buga k'ofar yyi da k'arfi,Surayya da bata dade da koma wa gida ba sabida tsabar tsoron da take ji,ganin biyar tayi ne yasa ta nufi gida dan ta d'ora girki,tana cikin jajjage taji an buga k'ofa wurgar da tabaryar hanunta tayi ta shige d'akinta da gudu ta rufe k'ofa jikinta sai rawa yake,jin da tayi an k'ara buga k'ofar ne yasa ta fara" wa innahu sulaimanu wa innahu bismillahi ku kuke ganin Mu, ba mu muke ganinku ba"duk adduar daya zo bakinta karantawa kawai take in banda gumi babu abinda ta keyi,Abdulmajeed jin shiru ba amsa bane yasa yayi tunanin ko basa gidan,suna gidan Hadiza d'aya makociyar tasu da wanan tunanin ya nufi gidan Hadizan yana shirin kwankwansa,ta bud'e k'ofar ta fito da alama wani wajen zata,da sauri ta gaishe shi,ya amsa yana tambayarta ko su Muhibba na nan,ce mishi tayi,Muhibba bata nan amma Surayya bata Dade da barin gidanta ba,ta tafi ta d'ora girki,godiya ya mata ya nufi gidan Surayya yana mamakin inda Muhibba taje,k'ara kwankwasa gidan yayi,Surayya da tun lokacin tana jikin labule sai addua take,jin an k'ara buga k'ofar ne yasa ta saki fitsarin daya matseta,dan duk a tunaninta aljanar ce take buga gidan tunda taga Muhibba bata nan,Abdulmajeed gajiya yayi da buga k'ofar ya koma kan lifan d'insa ya zauna ,zuciyarsa sai tafarfasa take, Yana zama da minti biyar,Ayuba shima ya k'aryo kwana parking yayi a k'ofar a gidansa ya sauk'o daga machine d'insa ya nufi wajen Abdulmajeed dake karkada k'afa hannu ya mik'a mishi suka yi musabiha yana kallon k'ofar gidansu Abdulmajeed,tambayarsa yayi Muhibba bata nan,cikin tsananin Bacin rai Abdulmajeed yace masa bata nan shima bai San Inda ta tafi ba ya ma d'auka tana gidansa Ashe itama surayyar bata nan,Ayuba juyawa yayi ya kalli k'ofar gidansa,ganin babu padlock daga waje ne yasa yace mishi Surayya ta nan k'ofar gidan ya nufa shima ya fara kwankwasa k'ofar,ganin ya kwankwasa sau hud'u ba a bud'e bane yasa yayi yayi amfani da mukullin gurinsa ya bud'e k'ofar,Surayya kuwa tana jin an bud'e k'ofar ta saki ihu tana " wayyo Allahna kiyimin rai Ku kuke ganinmu bamu muke ganinku ba,Allahu la illah ha illa huwa Al hayul al qayyum,inna anzalnahu fi lailatul kadir,wa shamsu wa duhaha,kowane sura kamowa kawai take jikinta na rawa,Mamakine ya rufe Ayuba yace " Surayya kina da hankali kuwa mai yake damunki,"?shiru Surayya tayi da taji muryar Ayuba lek'a wa tayi ta windown d'akin sai da ta tabbata shine tafito daga bayan labulen ta bud'e k'ofa ta fito,Ayuba jikakken skirt d'inta yafara bi da kallo,ya dawo da kallonsa kan fuskarta da ta had'a gumi,sai muzurai take,"Surayya lafiyarki kuwa? Ayuba yace yana k'ara binta da kallo,"ina fa lafiya ayuba aljana ta sako Mu agaba tun dazu take buga min gida,Muhibba ma ta tafi gida tace bazata iya ba ta tafi gidansu,Ayuba mamaki ne ya rufe shi yace "bangane mai kike nufi ta da tafi gidansu ba"? Surayya kwashe komai tayi ta fad'awa Ayuba,girgiza kai yayi yace mata Abdulmajeed na waje bari ya fad'a masa Muhibba ta tafi gidansu,Surayya Hijabinta ta zura ta bishi suka yi waje dan tace tsoro take ji,Ayuba bayani yayi wa Abdulmajeed,Surayya itama ta bashi labarin yanda aljanar ta ringa tsorata su tana ita bata San tsautsayin da ya kai Muhibba ta bari aljana ta shigar mata band'aki ba,Ayuba Shawara ya hau bawa Abdulmajeed akan yasa ayi mishi sauk'ar Qurani,tunda suka fara mishi magana ya saki Baki yana kallonsu dan ba haka Muhibba ta ce mishi ba,kenan karya muhibba take mishi data ce Almajira ce tayi bara,aljana ta bud'ewa gida ta shigar musu band'aki,wani irin tafasa yaji zuciyarsa nayi yana ganin Muhibba ta gama rainashi duk gargadin da ya mata Ashe bata ji ba, godiya yayi wa Ayuba ya k'arbi mukullin padlock d'in daga hanun surayya ya bud'e gidan ya shigar da lifan d'in sa
[9/22, 12:18] Sadnaf: 🙆🙆 *D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO*😭😭

*Written by*
💅💅 *SADNAF*💞

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l

*TRUE LIFE STORY*

🙆🙆 *D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO*😭😭

*Written by*
💅💅 *SADNAF*💞

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l

*TRUE LIFE STORY*

*#[email protected]*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*

PAGE 6

Abdulmajeed ransa a mutuk'ar bace ya zauna a Palo sai karkad'a k'afa yake yana tunanin matakin da zai d'auka akan Muhibba,ga yunwan da ya koro shi,gashi bai iya girki ba,tsaki yayi a fili yace "zaki gane kurenki bazan je gidan naku ba,in kin gaji zaki dawo da kanki" kwanciya yayi akan dogon kujeran yana jin yanda cikinsa ke k'ugin yunwa.

B'angaren Muhibba kuwa sai wajen k'arfe 2:30 ta tashi daga barci wanka ta farayi,tayi sallah abincin da Nafeesa ta zubo mata ta jawo taci ta koshi,ta nufi d'akin Mahaifiyarta,ganin bata d'akin ne yasa ta koma d'akinsu ta zauna ta rafka tagumi tana kallon Nafeesa dake shirin tafiya islamiyya,tunanin Abdulmajeed ta fara yi tana tunanin ko ya zai ji idan ya dawo ya tarar ba ta nan,tunani tayi na ta kirashi a waya, ta fad'a mishi da kanta,wayar Nafeesa ta k'arba tayi dailing Number Abdulmajeed,taji switchoff,mik'awa Nafeesa wayarta tayi ta cigaba da tunaninta,ta rasa mai yasa aljanar data taimaka wa take bibiyarta,Muhibba ahaka ta wuni tana tunanin sai wajen k'arfe shidda Mallam Hashimu Mahaifinta ya dawo daga kasuwa,sai da yayi sallar isha yaci abinci Maryam take bashi labarin abinda ya faru da Muhibba,sallati yayi yasa aka kira mishi Muhibba,ya k'ara tambayar ta abinda ya faru ta k'ara bashi labarin abinda ya faru,ba k'aramin firgita Mallam Hashimu yayi ba daya ji abinda Muhibba tace dak'ewa yayi bai nuna mata ba ya rufe ta da fad'a yana mai ya kai ta ta bud'e k'ofa ai gashi nan D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO ta janyo wa kanta fad'a ya ringa mata sosai yana kar ta sake irin wanan gangancin,gobe zai bata adduoi ta koma gidanta insha Allahu,Allah zai kareta daga sharrin aljanar,jin abinda yace ne yasa Maryam tayi magana tana "bai kamata Muhibba ta koma gidanan ba tare da anyi saukar Qurani ba ita ganinta a kira Abdulmajeed awaya ace masa yazo inyaso sai su bashi shawaran yasa ayi saukan,da wanan shawarar suka yanke zasu nemi Abdulmajeed,Muhibba ta tashi ta nufi d'akinsu tana tunanin Abdulmajeed.
Chapter 5 · 0% Book details