Sashe 3
Daga Taimako Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
K'aro suka yi da Abdulmajeed daya taho band'akin a guje,kankameshi tayi sosai tana nuna band'akin in banda rawa babu abinda jikinta ke yi,"ke Wai mai yake damunki ne menene acikin band'akin? Abdulmajeed yace yana k'ok'arin raba jikinsa da nata,k'ara kankameshi tayi tana nuna band'akin,gaba d'aya ta firgice,tsaki yayi yace " wlh wani sain idan kika yi Abu kamar a rufeki da duka,ni cikani inga abinda yake cikin band'akin,yace yana k'ok'arin raba jikinsa da nata,ina ai k'ara rungumeshi tayi gam tana kuka sai gumi take,haushi ne ya rufe Abdulmajeed daya ga taki magana sai nuna mishi band'aki take,yakice ta yayi da k'arfi daga jikinsa ya nufi band'akin Muhibba ta saki wani k'ara ta bishi aguje ta k'ara rungumeshi,adai dai lokacin daya bud'e band'akin yana k'arewa koina kallo,babu abinda yagani daya wuce butocin data dura Ruwa aciki,sai mudubin dake jikin bango,tsaki yayi ya d'auki bokitin wankan,Muhibba kuwa tana mak'ale abayansa,janyota yayi ta dawo gabansa yace " Muhibba Wai yau mai yake damunki ne ko dai gamo kika yi?Yanzu menene a cikin band'akin nan daya baki tsoro,banasan irin wanan wasan Sam ya kamata ki sani,idan ina cikin mode din wasa kin sani, idan bana cikin mode d'in wasa ma kinsani,dan haka in wasa ma kike min ki daina banaso"magana take sanyi amma inta tuna murd'adden Halin Abdulmajeed sai ta fasa dan ita kanta wani sain tsoronshi take ji dan har mamakin yanda akayi ta aureshi take,duk da yana da wuyan sha'ani wani sa'in dan akwai shi da tsare gida,wuceta yayi yaje ya debo ruwan wankan yakai band'akin,ganin yana k'ok'arin rufo k'ofar ne yasa tayi sauri ta k'arasa band'akin dan wani irin tsoro ne ya rufeta,had'e rai yayi yace " menene?" Hawaye ne ya hau zubo mata tace "dan Allah bari na jiraka a band'akin kayi wankan tsoro nakeji wlh" ayanayin da tayi maganar ne yasa yaji tausayinta yace to "k'aro mana ruwan wankan sai muyi wankan tare dan dama bakiyi wanka ba,ni yau bansan mai yake damunki ba" da Sauri ta kinkinmo bokitin ruwan ta shiga band'akin dashi,jikinta sai rawa yake Kalle kalle tafara yi dan gani take zata iya ganin wanan matar,Abdulmajeed brush ya farayi,hakan data gani ne yasa itama ta matsa jikin mad'ubin dake rataye aband'akin ta zura hannu a d'an kwandon dake mak'ale ajikin mudubin dan ta d'auko brush d'inta da MacLean itama tayi brush,kamar cewa akayi ta kalli madubin,matar nan ta hango a mudubi tana tsaya ajikin bango tana mata murmushi hakoranta amadadin farare jajaye ne,wani irin gigitacen k'ara ta saki ta zube a band'akin a sume,sallati Abdulmajeed yayi ya kinkimeta yayi waje da ita, a d'aki ya kwantar da ita, ya debo ruwa yazo yana yayyafa mata,ajiyar zuciyar tayi ta bud'e idonta ahankali,kuka ta fashe dashi ta rungume Abdulmajeed tana "Abdul na shiga uku na lalace D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO na janyo wa kaina masifa laifine dan na taimaketa,meyesa take San cutar dani" duk maganar da take kuka take jikinta na rawa,Abdulmajeed d'agota yayi yana share mata hawaye yace " Muhibba mai ya faru wa kika taimakawa? Ki fad'amin gaskiyar abinda ya faru dan ni ina dawowa nasan ba dai dai kike ba,dan gabad'aya a firgice kike" tunanin Muhibba ta fara yi na ta fad'a mishi gaskiyar abinda ya faru,wani tunani tayi kwanakin baya wasu 'yan mata sun zo lokacin Abdulmajeed yana nan, 'yan matan suka ce ta taimaka musu da ruwan sha,shigowa tace suyi tayi musu jagora har palo,ta debo musu ruwan suka sha daga nan kuma hira ta b'arke musu kasancewar mata akwai saurin sabo,suna cikin hirar Abdulmajeed ya shigo yace su fita su bar mishi gida,jiki na rawa suka bar gidan,aranar Abdulmajeed kwana yayi yana mata fad'a kamar ya daketa,Ya kuma ce mata duk lokacin da ta k'ara barin bakon mutum ya shigo masa gida,sai ya d'auki mumunan mataki akanta,da wanan tunanin tak'i gayawa Abdulmajeed gaskiyar abinda ya faru,Abdulmajeed ganin tayi shiru tak'i magana ne yasa yaji ransa na b'aci wani irin tsawa ya daka mata yana " ina tambayarki kin yi shiru wa kika taimakawa yake Neman cutar dake" jikinta ne ya hau rawa tsoron Abdulmajeed ya rufeta magana tafara yi tana kuka "wata tsohuwa ce dazu tazo bara tace na taimaka mata da sadakar abinci,shine na bata,ta tafi,tunda ta tafi take tsoratani duk Inda nayi sai na ganta"wani mugun tsaki yayi ya mik'e "Dana San abinda kika yi kenan wlh ko saurarenki ba zanyi ba badai bakya jin magana ba ki cigaba watak'ila ma aljana kika taimakawa,ke gaki uban yan San taimako,hanyar waje yayi ta bishi da gudu,tana tsaye a band'akin yayi wankansa ko kallonta bai yi ba,itama cire kayanta tayi dasauri ta watsa ruwan duk abinda take yi idonta a rufe dan gani take inta bud'e idonta zata iya ganinta,a tsakar gida ta k'arasa sa towel dan Abdulmajeed fitowa yayi ya barta a band'akin,alwala tayi tabi bayan Abdulmajeed daya shige d'akinsa yana shimfid'a sallaya,doguwar Riga tasa ta zura hijabinta ta tsaya daga bayansa,sai da suka yi sallar magriba kafin suka yi isha,Muhibba addua ta ringayi a sujadar karshe tana addua'r Allah ya rabata da sharrin matar da ta taimaka wa,Abdulmajeed Palo ya nufa bayan sun shafa,biyo shi tayi da sauri ko hijabin jikinta bata cire ba, a tsakiyar palon ya zauna inda ta jera abincinsa,zama tayi ta ta d'auki plate tafara zuba abincin jikinta sai rawa yake dan har yanzu tana ganin fuskar matar a idonta,ajiye plate d'in tayi a gabansa bayan ta zuba mai abincin,bismllah yayi,yafara cin abincinsa Muhibba kuma ta zauna tayi tagumi tana hawaye,"ke bazaki ci abincin ba kenan"? Abdulmajeed yace batare da ya d'ago ya kalleta ba,Share hawayen daya zubo mata tayi tace " a koshe nake bana jin yunwa" Abdulmajeed d'agowa yayi ya kalleta ya ajiye cokalin Hanunsa,yace," Wai Muhibba kukan mai kike yine,wani ne ya aike ki bawa tsohuwa abinci,ke kika fi kowa San kiyi taimako,haka kika ga sauran makotanki nayi,ban hanaki taimako ba amma na fad'a miki kinsan irin wayanda zaki na taimakawa dan tun daga lokacin da Aunty Ainau (yayarsa) ta bawa Almajiri sadaka ta kamu da rashin lafiya mai tsanani sai da akayi dagaske aka gano Ashe almajirin nan ba mutum bane Aljani ne,Ashe kud'in nan da ta bashi sadaqa dashi ya ringa cutarta sai da aka runga adduoi ana sauk'ar qurani kafin ta samu lafiya,wlh tunda ga lokacin nake tsoron in taimakawa Wanda bansani ba,dan kai da zuciya d'aya za kayi taimakon amma akarshe Wanda ka taimakawa ne yake cutarka shiyasa nake hanaki kwashe kwashe," tunda ya fara magana taji wani tsoro ya kuma rufeta,matsawa tayi kusa dashi da sauri tana " Abdul yanzu ya zanyi wlh bansan ba mutum bace"tace tana fashe da kuka,"ki kwantar da hankalinki kiyi Addu'a insha Allahu,Allah bazai bata ikon cutar dake ba,this would serve you a lesson next time zaki San irin wayanda zaki ringa taimaka wa,yanzu dai ki zuba abincin nan kici sai na raka ki kiyi alwala kizo ki kwanta,"Abdulmajeed yace yana bud'e kular abincin,dak'yar taci cokali uku ta ce mishi ta koshi,kwashe kwanukan yayi da kansa ya kai kitchen, yace mata tazo tayi alwalar,alwala tayi a tsakar gidan kanta a sunkuye dan gani take inta d'ago zata iya ganin Matan nan,d'akinsa ta nufa dasauri ta rufo k'ofar,dan Abdulmajeed har ya kwanta,shiryawa tayi cikin kayan barci,ta fesa turare ta kwanta agefensa kamar zata shige jikinsa sabida har yanzun a tsorace take,tashi yayi zai kashe fitilar d'akin tayi sauri ta rik'o shi "dan Allah Abdul karka kashe wutan d'akin wlh tsoro nake ji" wani kallo ya watsa mata yace " kin tab'a ganin nayi barci fitila a kune,kashewa zanyi dan bazan iya barci ba ina barshi a kune,ke kika sa tsoro aranki amma ina gefenki mai zai tsorata ki,"sauk'a yayi ya kashe fitilar d'akin tayi sauri ta runtse idonta da k'arfi dan tuni duhu ya mamaye d'akin,yana kwanciya ta rungumeshi gam,shi kuwa ya lalubo bakinta ya fara kissing d'inta,duk abinda yake idonta a rufe yake gam,ko kwakwaran motsi bata yi,shi kadai yayi kidansa yayi rawansa,sai wajen k'arfe biyu ya k'yalleta aikuwa nan da nan barci yayi awon gaba da ita, wajen k'arfe hud'u ta juya da zumar ta gyara kwanciyarta,ji tayi hanunta ya sauk'a akan Abu kamar gashi,shafawa tayi dan ta gaskata gashin ne,ji tayi gashi ne mai tsayin gaske,bud'e idonta tayi a hankali tayi tozali da wanan matar a kwance a gefenta ta kura mata ido bakinta a bud'e jajjayen hakoranta kuwa awaje, wani mugun ihu ta saki ta rufe idonta gam.b
[9/22, 12:18] Sadnaf: 🙆🙆 *D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO*😭😭
*Written by*
💅💅 *SADNAF*💞
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l
*TRUE LIFE STORY*
🙆🙆 *D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO*😭😭
*Written by*
💅💅 *SADNAF*💞
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l
*TRUE LIFE STORY*
*#[email protected]*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*
PAGE 4
[9/22, 12:18] Sadnaf: 🙆🙆 *D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO*😭😭
*Written by*
💅💅 *SADNAF*💞
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l
*TRUE LIFE STORY*
🙆🙆 *D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO*😭😭
*Written by*
💅💅 *SADNAF*💞
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l
*TRUE LIFE STORY*
*#[email protected]*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*
PAGE 4