Sashe 10
Daga Taimako Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
K'arar fad'uwar Abdulmajeed dasu Mallam isah suka ji ne yasa suka yo hanyar waje dagudu,abakin k'ofa suka ga Abdulmajeed akwance,sallati suka yi Mallam Isah yayi Sauri ya d'agoshi yana k'iran sunansa,Hafsa da sabida gigicewar da tayi bokitin ruwa ta kinkimo,ta fara watsa mishi,dogon ajiyan zuciya Abdulmajeed yaja ya bud'e idonsa ahankali,kuka ya fashe dashi yana " na shiga uku na lalace Abba aljanar nan tana so ta zautar dani,ni da mai tab'in hankali babu maraba,tace na mata wulak'anci haka zata yi ta bibiyata Abba Dan Allah Ku taimaka min Ku rabani da ita " Abdulmajeed yace yana k'ara fashewa da kuka,Hafsa da tunda Abdulmajeed ya fara magana itama take kukan Dan Tausayin d'anta take ji jarumi irin Abdulmajeed yabi ya rame ya susuce kamar bashi ba, Magana ta fara yi tana " Mallam Dan Allah mu kai Abdulmajeed gun wani Mallamin ba sai mun jira dawowar Mallam Saminu mai Rukiyya ba, idan muka ce zamu yi ta jiransa bamu San ranar dawowarsa ba gashi aljanar nan kullum sai ta tsorata shi,ba dama ya fita sai ya dawo da gudu,in bai suma ba zai tafi band'aki,wanan Masifar da mai tayi kama," Hafsa tace tana k'ara fashewa da kuka,
"Hafsa bazaki gane ba,Mallam Saminu mai Rukiyya shi kadai ne zai iya raba Abdulmajeed da Aljanar dake bibiyansa Dan yana aiki da aljanu,amma duk inda zamu je sai dai aci kud'inmu yanzu kinga Mallam Jamilu da ya zo cemin yayi na kawo dubu ashirin ya rabashi da aljanar Dan ta aureshi,kiji fa,amma idan wajen Mallam Saminu mai Rukiyya muka kai shi kud'in sadaka kawai zamu bashi,ya kuma rabashi da aljanar,tunda kinsan shi yayi wa Ainau addu'a ta samu sauki" Mallam Isah yace cikin tsanin damuwa
" Hafsa share hawayen da ya zubo mata tayi tace " to shikenan Mallam yanzu yaushe zaka koma Gidan Mallam Saminu mai rukiyyar,ka duba kaga ko ya dawo"?
"Ai basai naje gidansa ba inada Numbers zan kirashi naji yaushe zai dawo,Abdul tashi mu Shiga ciki kaji Insha Allahu,zamu rabaka da aljanar",Mallam Isah yace yana mik'awa Abdulmajeed Hannu daya yi Shame shame akasa yana zubar hawaye,Abdulmajeed Mik'ewa yayi,suka shiga ciki,jin ana kiraye kirayen sallah ne yasa yaje yayi alwala ya nufi massallaci Dan tun daga lokacin da aljana ta sako shi agaba ya daina wasa da sallah
Muhibba kuwa tundaga lokacin da Abdulmajeed yazo gidansu ya tafi take ta kuka gabad'aya ta rasa mai ke mata dadi,ta rasa mai yasa aljana take bibiyar ita da Abdulmajeed,laifin ne Dan ta taimaka mata,ahaka Muhibba ta wuni tana kuka,sai da ta ga ba kukan shine Mafita agare ta ba,addua ya kamata ta dage ta ringa yi Na Allah ya rabasu da aljanar ya karesu daga sharrinta,Da wanan tunanin Muhibba ta dage da addua ba dare ba rana akan Allah ya rabasu da Aljana dake bibiyarsu,ayau kwana hud'u kenan rabonta da Abdulmajeed ko awaya bata samunsa,hakan kuwa ba k'aramin damunta yake ba,shawara ta yanke zata je gidansu taji ko Lafiya.
K'arfe uku na rana ta nufi band'aki tayi wanka ta d'aura alwala,tafito tazo gaban mudubi ta fara shiryawa Dan so take tana idar da sallar la'asar ta tafi gidansu Abdulmajeed,tana cikin shafa hoda ta hango wanan aljanar abayanta ta zuba mata ido tana kallonta,Muhibba duk da ta tsorata adduoi ta ringa yi azuciyarta ta d'aure ta fara magana Dan ta sha alwashin indai aljanar ta k'ara bayyana bazata gudu ba,zata tsaya ta tambayeta mai takeso awajensu take bibbiyarsu,cikin jarumta da rashin tsoro Muhibba bakinta d'auke da ayatul kursiyyu ta juya abun mamaki bata ga aljanar ba amma da ta juya ta kalli Mudubin aljanar na nan a tsaye,bata tsorata ba ,tace "mai yasa kike bibiyar ni da mijina? Mai muka miki ? Laifine Dan na taimakeki?
murmushi aljanar tayi da ya k'ara sa ta zama abun tsoro hak'oranta mai kama da na allura ya bayyana cikin Muryar da tafi kama da sauk'ar aradu ta fara magana " baki min komai ba Muhibba,laifin mijinki ne ya shafeki,banida niyyar in cutar dake,hasali ma sanki nake yi,Dan gashinki na burgeni,wak'ok'in da kike sawa awaya yana sani nishadi,Dan abinda ke kawoni gidanki kenan,ba abinda yafi burgeni dake kamar in kika shigo band'aki naga kina d'an wak'a gashinki a bud'e ,ni sanki nake yi ,Mijinki ne dai ya min laifin domin ya wulak'antani,ya mareni akan nace ina sansa ,ya koreni Dan naje bara,ya zageni Dan naje gidansu neman taimako ,Dan haka sai na rama abinda yamin,"
Muhibba da jikinta ke rawa sabida muryarta ba k'aramn tsoro ya bata ba,tambayarta ta ke so tayi mai Abdulmajeed ya mata ta b'ace,addua tayi,ta cigaba da kwalliyarta,k'arfe hud'u saura ta fito daga gida ta nufi gidansu Abdulmajeed.
Atsakar gida ta samesu a zaune Abdulmajeed na kwance akan tabarma,yana jin karatun Qurani,Mallam Isah da Hafsa na daga gefensa,sallamar da tayi suka amsa,Abdulmajeed ya d'ago yana kallonta,Dan ayanzu haka ita yake tunani Dan yayi missing d'inta sosai amma ba dama yaje gidansu Dan yana fita aljanar zata kunya ta shi ta sa shi gudu abakin titi ko ta sa shi sakin fitsari a wando,Muhibba durk'usawa tayi tana gaishe da su Mallam Isah idonta akan Abdulmajeed da ya tsura mata ido,gani tayi yabi ya rame kamar ba shi ba ,take taji hawaye na Neman zubo mata sabida tausayinsa da ya rufeta,Wai Abdulmajeed d'inta da baya tsoro ba yasan wargi,shine ya zama haka abun tausayi,amsa gaisuwarta su Mallam Isah sukayi suna tambayarta ya mutanen gidan,ce musu tayi lafiyarsu kalau,dama taji Abdulmajeed shiru ne kwana biyu shine tace bari tazo taga ko Lafiya,ashe ma bashi da Lafiya,Dan duk a tunaninta Abdulmajeed bashi da Lafiya,Hafsa cewa tayi ina fa lafiya Aljana ta sako Abdulmajeed agaba tana Neman zautar dashi,bashi da aikin da wuce gudu, da zuwa band'aki,tausayin Abdulmajeed ne ya k'ara rufe Muhibba tace musu ba abanza Aljanar ke bibiyar Abdulmajeed ba,laifi yayi mata,zaro ido suka yi suna kallonta, Abdulmajeed yayi sauri ya zauna yana tambayarta wane laifi yayiwa Aljanar da zata sako shi agaba,ajiyar zuciya ta sauke ta fara basu labarin abinda Aljanar ta gaya mata,ak'arshe tace " Abdulmajeed zaka iya tuna wacce ka mara Dan tace tana sanka,zaka iya tuna wacce tazo bara gidanku ka koreta?zaka iya tuna wacce tazo Neman taimako ka zageta"? Shiru Abdul majeed yayi,yana tunanin wa ya tab'a Mara dan tace tana San shi,sai da yayi tunani mai zurfi kafin ya tuna,ya tab'a zabgawa wata mari da ta dage tana sanshi,
*WAIWAYE*
Lokacin da Abdulmajeed ke zuwa high institution ,Dan gayu ne na k'arshe yana mugun ji da kansa gani yake yafi k'arfin ,yan matan makarantar,Dan aganinsa babu ajinsa a cikinsu,Dan ba laifi 'yan mata suna sanshi, hakan ne yasa ya d'orawa kansa Girman kai yake wulak'anta 'yanmata,abokanansa suyi ta mishi wa'azi,watarana suna zaune ak'arkashin bishiya suna hira da abokanansa,d'aya daga cikinsu yake basu labarin yarinya da yakeso a ajinsu,Abdulmajeed dogon tsaki yaja yace wa abokin na shi, yayi asara ya rasa wacce zaiso sai wanan bak'ar hallitar mumuna, Aljana da tafito shawaginta tana saman bishiya tana jinsu,jin abinda Abdulmajeed yace ne yasa ta rikid'e ta koma mutum, a mumuna siffa,Wanda sabida muninta bazaka so ka k'ara ganinta ba,gata bak'a wuluk,taho wa tayi daga nesa ta nufi inda suke,abokanan sa kuwa dama suna da kallon mata,hangota da suka yi daga nesa ne yasa suka fara gulmarta suna cewa basu tab'a ganin mai muninta ba,duk abinan da suke Abdulmajeed bai d'ago ba yana dai jinsu,ganin da suka yi wajensu ta nufa yasa suka ja bakinsu su kayi shiru suna mamakin wajen wa zata zo,tana isa wajensu ta saki murmushi tana gaishe su kasa amsawa sukayi sakamakon tozali da suka yi da hakoranta jajjaye da ya k'arawa fuskarta muni,Sagir ne yayi k'arfin hali ya amsa gaisuwarta yana tambayarta mai take nema awajensu,murmushi ta k'ara yi tace wajen Abdulmajeed tazo,Abdulmajeed d'agowa yayi da sauri Dan duk abinda ake kansa a sunkuye yake,tozali da yayi da fuskarta ne yasa yaji wani zafi a zuciyarsa,Dan arayuwarsa ya tsani munana,gani yayi ma ta raina mishi hankali yama zaayi tace wajensa ta zo,cikin had'e rai yace mata lafiya tak e nemanshi,batare da wani b'ata lokaci ba tace mishi sanshi take yi,abokanan Abdulmajeed k'yalk'yale wa suka yi da dariya da suka ji abinda tace,Dan sun San Abdulmajeed ya tsani mumunar mace,dariyar da suka yi ne ya tunzura Abdulmajeed ya zabga mata lafiyayyun mari guda biyu,yace shi sa'arta ne da zata ce tana sanshi,in taga level d'inta bata sani ba,zagi ya rufeta dashi,Aljana ta durk'ushe akasa tana kuka,zaginta ya cigaba da yi kamar zai daketa Dan ma abokanansa na rikeshi,mik'ewa tayi ta goge hawayenta ta ce Dan ta ce tana sanshi shine zai mareta,d'aga hannu zai k'ara marinta su sagir suka yi sauri suka rik'e mishi hannu,girgiza kai tayi tace yaje zai gani,da zagi ya bita har tabar gurin,tun daga lokacin Aljanar nan ta ringa zuwar wa Abdulmajeed a siffar mutane,yana wulak'anta ta,a almajira taje gidansu,yana tsakar gida yana cin abinci,Almijira ta ringa zabga bara tana a taimaketa Dana abinci yunwa take ji,sai da ta kai minti talatin tana bara,Abdulmajeed ko d'agowa bai yi ya kalleta ba,ganin da yayi ta cika mishi kunne da bara ne yasa ya mik'e afusace ya koreta yana ce mata mayya sai kace dole,Aljana kuwa ta k'ara zuwa gidansu daddare yana zaune a k'ofar gida wata tazo Neman taimako wai bata da kaya ataimaka mata,ganin Abdulmajeed bai kulata bane yasa ta fara k'ok'arin shiga gidan,tsawa ya daka mata yace mata ajiya ta bawa mutanen gidan zagi ya rufeta dashi na uwa na uba ya koreta,Aljana kuwa tana tafiya ta sha alwashin sai ta rama abinda Abdulmajeed ya mata itama ta zautar dashi,wanan kenan.
Da sauri Abdulmajeed yace ya tuna wacce ya tab'a zabgawa mari,girgiza kai Muhibba tayi tace mishi
"To ba mutum bace Aljana ce,sallati su Mallam Isah suka yi suna sun shiga uku Abdulmajeed kuwa jikinsa ya fara rawa Dan ya tuna tace yaje zai gani,
Muhibba k'ara tambayarshi tayi ko ya tuna almajirar da tazo bara da kuma wacce tazo Neman taimako,?Abdulmajeed sai da yayi tunani mai zurfi yace ya tuna,nan ma Muhibba tace mishi Aljanar ce,,