← Book details Daga Taimako Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 11

Sashe 6

Daga Taimako Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Abdulmajeed kuwa da k'yar yayi sallar magriba dan jikinsa har rawa yake sabida yunwar da yake ji,mik'ewa yayi daga kan sallayar ya d'auki mukullin lifan d'insa dan bakin titi yake so yaje ya siyo tsire yazo yaci,ji yayi ana kwankwansa gidan,hanyar waje yayi yana bud'ewa yaga Ayuba a tsaye da flask a hannu,Ayuba mik'a mishi flask d'in yayi yana cewa "ga abinci nan yaci tunda madam bata nan,da sauri ya k'arb'a yana mishi godiya,kulle k'ofar gidan yayi,ya ajiye flask d'in hanunsa sai da ya fara tada engine tukuna,ya nufi Palo, a tsakiyar Palon ya zauna ya bud'e flask d'in lafiyayyen jollof d'in shinkafa da yaji kayan had'in kayan lambu yayi tozali dashi,aikuwa da gudu ya nufi kitchen ya d'auko plate da spoon, yazo ya zauna ya zuba ya fara ci, sai da yaci ya koshi sosai yayi hamdala,dak'yar yayi sallah isha sabida koshin da yayi,plasma dake mak'ale a jikin bango ya kunna bayan ya idar da sallah ya fara kallo Dan ya rage dare,Dan ji yayi gidan ya mishi fad'i ya kuma rasa mai yake mai dadi,tsaki yayi a lokacin da ya dau remote Dan ya chanza tasha yana " gida idan babu mace tamkar kango ne" kallo yake amma tunanin
Muhibba yake ahaka ya ringa zuba tsaki shi kadai,wani irin tsoro ne ya rufeshi a lokacin da yaga horror film akeyi dan Inda aka nuno yanzu ba k'aramin tsorata yayi ba da sauri ya kashe kayan kallon,yayi waje band'aki ya nufa Dan ya d'auko bokiti ya zuba ruwa ya watsa Dan kwanciya ya keso yayi duk da bashi da tabbacin in zai iya baccin,ganin babu ruwa abokitan gidan ne yasa ya ja ruwa a rijiya,ya kai ruwan band'aki ya koma d'akinsa ya cire kayansa ya d'auro towel ya nufi band'akin brush ya farayi kafin yayi wankan Dan ya Riga ya saba,takun takalmi ya fara jiyowa daga tsakar gida,takalmin ma irin mai tsinin nan,"kwas kwas kwas " kawai yake jiyowa,gabansa wani irin fad'uwa yayi Dan yasan ya kulle k'ofar,towel d'insa ya janyo da sauri yayi waje yana "waye" waige waige ya fara yi yayi hanyar k'ofar gida yaga k'ofar na nan a kulle,ciki ya koma ya duba ko ina bai ga kowa ba,rufe ko ina yayi ya koma band'akin yana tunanin kunensa ne ya jiyo masa takun takalmi towel d'insa ya cire ya fara wanka,yana wanka yana kallon mudubi,duk'awa yayi Dan ya debo ruwa ya watsa yana d'agowa idansa ya sauka akan mudubin band'akin Matan nan ya hango abayansa ta zuba mishi ido tana kallonsa idonta jajaye kamar jini, dogwayen hak'oranta awaje,gashinta kuwa har kasa,wani mugun ihu Abdulmajeed yayi,yafita waje dagudu,cal cal cal ya shige d'akinsa ya kulle jikinsa na rawa, Numfashin sa kamar zai d'auke sabida tsabar tsoro,ahankali ya zauna akan gado yana mai da numfashi ya ma manta babu komai a jikinsa" adduoi yafara yi yana dafe da k'irjinsa ahankali ya fara samun nutsuwa,sai da kai Minti talatin azaune,ya mik'e ya d'auko gajeran wandonsa yasa,yana shirin sa vest yaji an bud'e k'ofar kitchen aguje ya hau kan gado ya janyo bargo ya rufe kansa jikinsa kuwa sai rawa yake,hawaye ya hau zubo mishi yana " Ashe Muhibba dagaske take da aljana a gidanan shi kenan tawa ta kare" ahaka ya cigaba da rawar d'ari yana adduoi ganin bai k'ara jin motsi ba yasa ya yaye bargon da ya rufe Kansa ya zauna akan gadon sai da yafara lek'a ko ina ya duro daga kan gadon,Touch light ya d'auko ya kuna,yasa agafen gadon,duk da engine a kunne yake fitilar d'akin a kunne yake,wayarsa ya d'auko ya kuna torchlight d'in Dan ba k'aramin tsoro yake jiba Dan in ya rufe idonsa aljanar nan yake hangowa,gadon ya hau ya kwanta yana kalle kalle,bakinsa d'auke da addua Dan babu yanda zai yi ne in ya fita zai iya ganin aljanar da ba abinda zai sa ya kwana a gidan,ahaka ya kwanta a tsorace said wajen k'arfe d'aya da rabi barci ya d'aukeshi,wajen k'arfe uku na dare yaji motsi a gefensa ahankali ya bud'e idonsa cikinsa wani irin murd'awa yayi gudawa mai k'arfi ya taho masa sakamakon tozali da yayi da aljanar nan azaune a gefensa tana murmushi idonta ya k'ara girma razanan ihu ya saki ya mik'e aguje ya bud'e k'ofa yafita waje,ganin zai iya kashi awando ne yasa ya nufi band'aki da gudu ya rufe k'ofa ya hau kan Masai ya hau sakin gudawa jikinsa na rawa rufe idonsa yayi gam,kirjinsa sai dukan goma goma yake,babu abinda kake ji sai sauk'ar gudawansa😂😂😂(readers Ashe dai Abdulmajeed matsoraci ne) ji yayi kamar an bud'e k'ofar band'akin,cikin tsananin tsoro da firgita ya fara ihu yana " kiyi min rai karki cutar dani kiyi hak'uri Dan Allah" ihu yake sosai jikinsa na rawa shirun da yaji ne yasa ya bud'e idonsa ahankali ganin bai ganta a band'akin bane yasa ya d'iba a guje ko tsarki bai tsaya yi ba,ballantana akai ga yasa wandonsa,k'ofar gida ya bud'e ya fita waje,kasancewar babu wuta garin duhu,wandonsa yasa da sauri ya nufi gidan Ayuba ya fara kwankwansa da sauri yana waige waige ,Surayyan dake rungume ajikin Ayuba tana barci,jin da yayi ana kwankwasa gidan ne yasa ta tashi a firgice ta hau kan Ayuba tana nuna mishi k'ofa.

Abdulmajeed buga gidan yake da sauri yaji an dafa bayansa fitsari mai zafi ya saki awando a juya ahankali aljanar nan ce ta da fashi tace da muryar yara "Abdulmajeed ina zaka ni Dana zo na ta yaka hira"Abdulmajeed zubewa yayi akasa sumame.
[9/22, 12:18] Sadnaf: 🙆🙆 *D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO*😭😭

*Written by*
💅💅 *SADNAF*💞

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l

*TRUE LIFE STORY*

🙆🙆 *D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO*😭😭

*Written by*
💅💅 *SADNAF*💞

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l

*TRUE LIFE STORY*

*#[email protected]*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*

PAGE 7

😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂 *Readers bari dai na rufe bakina kar ya yage garin dariya Ashe haka page 5 da 6 yake da abin dariya sai da na karanta nima Dana yi posting naci dariya na gode Allah bare wajen matuniyata Surayya mai karatu kala kala gaskiya naji dadi babu laifi duk inda na lek'a jiya dariya kawai ake,masoyana.burina a kullum na saku nishadi*😂😂😂😂😂

*Note*- *yar uwa maman mamy sorry for scaring you,i don't mean to scare you please,like serious wanan novel d'in ya faru agaske amma ba exactly yanda nake rubutawa ba na k'ara abubuwa sosai sabida kawai na nishadantar,zan iya cewa adaidaita Sahu na hau kunsan mata da hira naji wasu suna labarin wacce abun ya faru da ita Dan da dukan alamu 'yar uwarsu ce, labarin ya mutuk'ar tsumani Dan sabida naji karshen labarin har an wuce inda zan sauk'a kunsan marubuci da San kwasan rahoto tuni jikina ya fara rawa nafara tunanin yanda zan juya labarin ya zama novel,aikuwa ina zuwa gida na sungumi wayata na fara typing, Dan haka sis ban yi novel dinan Dan in in tsorata kowa ba,nayi ne Dan na nishad'antar kuma Alhamdulillah ba laifi Sadnaf sunsa mutane dariya in kika kwantar Da hankalinki gajeran novel ne ba mai tsayi ba stay blessed everyone love you oll* 😂😂😂

Ayuba tashi yayi ya zauna ya duba agogon wayansa yaga k'arfe hud'u saura shima jikinsa ne ya fara rawa tsoro ya rufeshi yana tunanin Wanda ke kwankwasa k'ofa uwar haka,Kallon Surayya yayi da ta jike da gumi sabida tsananin tsoro yace ta d'aga shi yaje ya duba Wanda ke kwankwasa k'ofar,kankameshi tayi tace kar yaje ko ina yasani ko aljanar ce take kwankwasa musu k'ofa,ce mata yayi ba bud'ewa zai yi ba zai lek'a ta ramin k'ofar ne yaga waye, Surayya kin cika shi tayi,suka mik'e tare Ayuba ya bud'e k'ofa ahankali suka fito suna dab da isa k'ofar suka jiyo guje gujen maguna asaman kwanu, taku biyu Surayya tayi ta shige d'aki,Ayuba ya rufa mata baya,karkashin gado Surayya tafara shirin shigewa,Ayuba ya rufe k'ofar har da Dan tusar sa.
Chapter 6 · 0% Book details