← Book details Bakar Akida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 14

Sashe 8

Bakar Akida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Daman abinda muka zo yi shi ne ban hakuri da kuma Neman alfarma agurin Ku Maman Salma, Ga dai qawata nan Hajiya Bilkisu tayi nadama ta gane zabin danta shi ne farin cikinsa har ita kanta,To shi ne muka zo nemawa salman auren yarku salma kuma ashirye muke idan kun yarda a hade da na yar uwarsa minal ayi mai gabadaya."Hajiya Raliya tace cikin tausasa murya."

"Inna ta ce Dan Allah Ku rufa mana asiri ina d'an ku mai arziki ina salma yar matsiyata!"Ai ko gari ya watse ba'a kwashe daidai ba!" kuma ni agaskiya bazan iya hada 'yahtah da minal ba saboda ba rayuwar su daya ba,"bata da fitina da son fada kuma bana son a wulaqanta min yarinya akan wata *BAK'AR AK'IDA!."*

"Ai kowacce acikinsu da gidan ta daban kuma hakuri dai za ayi adaina tuna baya,Salman da Salma hadin Allah ne ,"kar mu cutar da yaran mu tunda suna son junan su! Dama can rashin sanin illar wannan *BAK'AR AK'IDAR* ne ayanzu mun gane gaskiya *BAK'AR AK'IDA* nan ta auren bani gishiri in baka manja Bakomai bace kuma batada wani amfani bare nasaba!"Kuma Akida ce ta wadanda suka jahilci meye gishirin zaman duniya!"Da Allah a qara hakuri Maman salma yanzu an zama daya komai ya wuce adaina tuna baya"In ji Hajiya Raliya."

"To ni ba zance komai ba sai dai idan Malam yazo zamuyi magana Inna ta ce atakaice."

"To mun gode ina Yar tamu salma bamu ganta ba har zamu koma."

"Dan Allah Ku tsaya ko ruwa baku sha ba fa,salma tayi tafiya taje garin mu sada zumunci."

"A'ah ba komai mun gode in Shaa Allah gobe zan dawo in ji kome kun ka yanke shawara akai."In ji Hajiya Raliya.

"Mun gode Hajiya mai gado tace,suka wuce yayinda inna tayi musu rakiya har zaure ta sannan ta koma daga ciki."

"Dr Salman da abokinsa
Dr.Jameel tsaye a bakin office dinsu tattaunawa sukeyi akan zancen auren sa anan yake fadawa Dr.jameel kudurinsa na auren salma a boye batare da Hajiya tasani ba saboda shi ita ya ke so ba minal ba."Kuma tuni ya gama shirin auren nasa abisa yarda da amincewar dangin babansa kuma ya samu nasarar saye kawun salma baban karime domin shi ne waliyyin salma ya ce zai tsaya masa ayi auren domun salma 'yarsa ce!" agefen dangin inna ma tuni suka yaba da hankalina kuma sunce sun bani salma ayi komai a felende na bukin, dAga baya a sanarwa iyayen mu su saka albarka tunda su *BAK'AR AK'IDA* irin tasu ta hana su fahimci halalcin auren mu da salma sai dai dinbim haramci da suke gani!"Dan haka kaji yadda muka shirya abin mu ni da salma kuma zanyi mata komai tun kan sutura har kayan daki."

"Ina Neman alfarmar ka taimaka min ka rufe min asirin nan kamar yadda muka saba!"Ka taimaka min domin samun cikar burina Salma!"Ka kuma tayamu da addu ah domin samun Nasara."In ji Salman da ya kare maganar yana kalon Dr jameel."

"Numfashi ya saki mai nauyi sannan yace tabbas wannan shi ake kira da gadar zare sai mai rabo zai fita "Ka ga laifin nan abokina har ni sai ya shafa bazan taba fita ba!"Shiyasa nikejin tsoro bana son rayuwar Hajiya ta baci akan mu!" Ba abinda zance Salman sai dai Allah yasa mudace yasa shi ne alheri saboda ina jin tsoron sabawa umurnin iyaye!"In ji Dr.Jameel."Fuskarsa dauke da damuwa!"

"Ba abinda zai faru Jameel,kawai ka tayani addu'a dan babu fargaba!"A zuciyata hakan na nuna min zanyi Nasara!"kasan dukkan mu daga ni har salma iyayen mu na sonmu bazasu iya fushi damu na tsawon lokaci ba, zasu yafe mana."

"Hmnnnn daga baya kenan."Inji jameel.

"Da hakan dai suka Wuce zuwa parking place na hospital din motocin su suka shiga suka wuce kowa da abin da yake tunani a ran sa!"

BAKAR AKIDA!

👸
©TASKAR NABEELA DIKKO

®PEN WRITERS ASSOCIATION

Page 51/60

*"THE VIRTUE OF REMEMBERING ALLAH*:" _Allah the all mighty has said:"Therefore remember me,I will remember you,Be grateful to me and never show me Ingratitude."Al baqara 2:152."_

_And He said:"O you who believe, remember Allah with much remembrance. Al-ahzab 33:41."_

*Subhanallahi wabi hamdihi*

*Alhamdulillahi Kaseeran*

*Allahu Akbar kabeeran*

________________________________

"Ilham da Hajiya mai gado zaune a cikin katafaren red and black din falon gidan nasu."A lokacin ne Hajiya ke sanarda Ilham duk abinda ke faruwa."

"Ilham ta ce"A gaskiya nima tuni na gane gaskiya na fara goyon bayan Yaya salman yanzu hakan ina zumunci da Yaya salma."Dan kuwa muna waya kuma gaskiya tana da kirki nima na goyi bayan abarshi ya auri zabinsa sai ya hada da naki zabin, kuma ina da tabbacin zai musu adalci!"Idan ma ansamu matsala Yaya minal ce kinsanta sarai ba tasan kimar mutane ba!"Kuma nayi faricikin amincewarki Ummana Allah ya qara maki lafiya."Ilham ta ce fuskarta a sake."

"Hajiya ta numfasa domin duk zancen autar ta gaskiya ne!"Sai yanzu ta gane rayuwar salman da minal ba daya ba!"Sai dai kaddara ta riga fata!"Ta ce "Ba komai Ilhaam Allah yasa hakan ne alheri!"

"Ameen Umma,yanzu kin sanarda Aunty Zainab din da minal?"Sun san da auren?"

"Ban fada musu ba!"Ni ina jin abin ba dadi ne!"Kishiya ba dadi!"amma kuma rayuwar salman nike dubi yana bani tausayi!"Sannan iyayen salma har yanzun ba su sanarda Mu
Ko sun amince sun yarda da auren duk da nasan Su na da fahimta!"

"Umma akwai damuwa a tattare da shi Dan fa tun kwanaki Baby (Dr.jameel)ke sanar min Yaya salman ya kamu da matsanacin ciwon zuciya!" yanzu hakan an daura shi akan magani duk akan ciwon son salma!"Da auren dole da ake son yi masa!"Ya ce kada afada miki ne, ko ni Yaya baisan cewa jameel ya sanarda ni ba!"Dan haka umma hakuri zamuyi dukkan mu, tun da kowa ba wani so yakeyi ba, minal dai jinin mu ce dole mu so ta fiye da salma, kawai a aura masa burin ran sa kowa yasamu kwanciyar hankali shi yafi dacewa!"Inji ilham."

"Hajiya mai gado ta ce ikon Allah yanzu shi baida lafiya ya boye min, abinda bai taba faruwa ba!"Duk kusancina da yarana ashe da kadan na rasa shi batare da nasan dalili ba sai dai inji labari a gari !"

"Wallahi Umma Allah kadai ya tsare akan wata can *BAK'AR AK'IDA* ta banza da ba amfani bare tushe!"Da mun rasa magajin Abbana Yaya salman shi ne garkuwan mu kiyi hakuri Umma ya auri zabinsa ni kaina banaso hakuri kawai zamuyi dan samun farincikinsa.!

"Ai bari kedai auta yanzu kam na gane gaskiya ashe talaka mutum ne,Mai hakuri da juriya,Duba fa duk rashin mutunci da cin zarafin da nayi musu akan salman, ashe minal da Nidal sunje sunyi musu ubansa har citta!"Amma matar nan bata wulaqanta Mu ba!"Sai yanzu na fahimci girman kai!Daukar kai! Da wulaqanci da fariya na ga wad'an su masu kudi kuma masu *BAK'AR AK'IDA* irin ta mu!"Allah ya yafe mana."

"Ameen umma gaskiya bamu kyauta musu ba!"Da masu saurin fushi ne bama zasu saurare ku ba!"Yanzu Ni zanje na karbo dinkin nan namu na dinner idan telan ya qare Umma."

"Kada kiyi yamma Auta!"

"Okay,Umma bazan jima ba!"

"Adawo lafiya Allah ya tsare min ke."Hajiya ta ce tare da shigewa bedrum."

"Malam a duba mana kuma a yafe mana mun san munyi ba daidai ba!" Amma ayi hakuri abar yaran nan su samu kwanciyar hankali."Hajiya Raliya ta ce cikin sanyin murya."

"Inna Baraka ta ce Hajiya da kin hakura domin shi malam idan ya hau yana da wuyar saukowa!"Saboda wallahi tun ranar da kuka zo na yi ta bashi baki amma fuuur!"Ya ce bazata sab'u ba!"Dan ya ce Yar sa bazata auri salman ana mata wulaqanci da cin fuska ba!"Kamar
Yadda kinkaji ya fada miki da bakinsa!"Dan haka maganin kar ayi kada afara!"

"Malam da ke gefen zaune yana jan carbin sa kallon Baraka da haj raliya kawai yakeyi domin shi ya qare magana idan sun gama cin kasuwar su zasu tashi a karshe!"Daga nan tashi yayi yama Haj Raliya sallama da ban hakuri kada taga kamar bai raga mata ba!"Ya wuce abinsa ya bar gidan zuwa majalisinsu na dattiban unguwa.'

"Itama sallama tayi da inna Baraka ta bar gidan tare da shaida mata!"Za dawo jibi kuma zataje felende abisa kwatancen da inna tayi mata domin dauko salma aji ta bakinta idan ta amince dole ne Baba ya barta ta auri shi salman din!"

"Inna Baraka tuni ta yarda da shawarar Hajiya Raliya domin tana da tabbas idan har ya lura salma har yanzun tana son salman zaiyi hakuri!"Duk da ta fahimci kamar salma ta bar salman din har abada ne!"

"Bayan fitar Hajiya Raliya daga gidan inna cigaba tayi da surfenta."

"Kawu Bala da matarsa Inna larai sai facaka sukeyi da kudi su karime har sababbin dinkuna akayi mata sai kuri ake acikin gida!"

"Larai ta ce shin malam har yau kudin da Hajiya melal ta bakane basu kare ba naga namu da ka bamu sun kare da dadewa?"

"Haba larai ana babbakar kura wa zai jiyo kaurin zomo."Ai salman ne ke bani kudi kuma yace min gidan sumunti zai gina min idan har na bashi auren salma."

"Hararar takaici ta watsawa kawu Bala ta ce lalle malam zuciyarka ba ta kishin kanka ba ce ta yaya ga karime nan gida batada mai kudi ko daya a ma nemanta!"Muna nema bamu samu ba!"Zaka bari salma ta auri salman mai kudi!"Kuma kana gani tun bata aure shi babu abinda baya yimasu har mu kan mu!"Meyasa baka watse maganar auren ba!"Ko ka mayarda zancen kan karime ni wallahi na tsani tauraruwar salma domin idan ta hasko na fahimci ta karime disashewa takeyi mtsssssww!Yarinya kamar aljana!"Inna larai ta karashe maganar cikin takaici!"

"Hahaha Larai ta malam Bala ikon Allah!"Ke meyasa tsabar son kanki rufe miki ido yakeyi ki kasa bude su ki gane waye gabanki nine naki bala fa larai kamar kin mantani da halina!"
Chapter 8 · 0% Book details