← Book details Bakar Akida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 14

Sashe 5

Bakar Akida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To mummy zan fada mata bye!"Minal tace tare da daukar keys din motarta da glass dinta ta wuce."

"Hajiya Zainab ko tashi tayi tabar part din minal da tuni 'yan aikinta suka fara gyarawa ta wuce nata sashen cikin jin dadin ganin minal ta sake sosai."

"Salma ta shirya tsaf acikin wata yar kodaddiyar atamafar ta super java orange da hijab dinta har qasa tayi kyau matuka"Kayanta ta ke cusawa acikin wata jikka(Gari yayi zafi)Babanta kawai ta ke jira suyi sallama ta wuce Filende."Inna Baraka ko sai faman sakon gaisuwa ta ke ba salma zuwa ga yan uwanta da dan tarkacen kayan yaji da tsintsiyar sharar daki tace akaiwa qannanta."

"Da kwantancen da Akayiwa Nidal har suka karaso kofar gidan bayan tayi parking ne ta kalli Nidal fuskarta dauke da mamaki tace Anya Nidal bakiyi batan kai ba!"Kin ko gane gidan sosai nifa tunda muka shigo unguwar nan nake kwankwanton da gaske ne Danbasaja yayi miki aikin kwarai kar dai address din sa na karya ne dan kawai yaci kudin Mu ne."Minal ta fada cikin mamaki!"

"Hmnnnn....kawata kenan wallahi Danbasaja bai min hakan duk iskancinsa yana tsoron nawa dan yasan banda mutunci zanyi masa wankin babban bargo nan ne dai gidan da mukasa shi aiki akai Minal !"

"Mtwsssss nan ne gida ai ko mahaukata ba zasu iya rayuwa anan ba!"Ni kinga ki fara shiga daga ciki idan nan ne kiyi flash dina!"Bazan iya shiga wannan banzan gidan ba Kada ma mu dauki wata cuta aciki!"In ji minal cikin jin haushi!Da takaicin abnda take tunani!"Azuciyarta!"

"Okay bara ni na Shiga din nagani ko nan ne ." Nidal tace ta fita motar ta zarce zuwa hanyar shiga cikin dan akulkin gidan."

"Inna Baraka na cikin daka taji motsin mutum batare da ta dago kanta ba, tace haba salma ba dai har kin gaji da jiran Malam din ba kiyi hakuri tunda yace ki jirasa mana kila Ma wani dan abu ne zai saya yabaki ki qara ga tsaraba!"

"Mtwssssss duk da gidan naku kamar na mahaukata hakan ashe har abubuwan da ke ciki suna da cutar hauka!Ba zanyi mamaki ba dan naji kina magana ke kadai dan na karanta tun akofar gidan naku "Nidal ta ce cikin gadara."

"Inna Baraka tabarya ta fitar cikin turmin tace baiwar Allah daga ina cikin mamaki da tsoro?"

"Ke malama kiyi min shiru ba wurin ki Nazo ba nan gidan su Salma sufyanu mai walda!?"

"Eh!"Nan ne ni ce Innarta kar dai laifi tai miki?"Inna tace cikin sanyin murya saboda daga ganin shigar Nidal tasan batada mutunci dan kamar ba yar hausawa ba."

"Fine good tsohowa ki kirata batayi min laifi ba magana kawai zanyi da ita in ji Nidal sannan ne ta dannawa qawarta minal kira ta ce ki shigo nan ne gidan nasu ta maida wayarta ajaka!"

" Inna Baraka tace bari in kira maki salma, jikinta na tsuma ta fara kiran sunan Salma ."

"Hankali salma ta amsa tare da kinkimo jakarta saboda taji magana awaje ta dauka Ko Baba ne ya dawo tafiyarta ta tashi."Sai dai me wata mai kama da kabila ta gani tsakar gidan tsaye!"A jiye Jakarta tayi a gefe."

"A hankali ta qarasa wurin da Innarta ta ke tsaye ta ce Inna lafiya!?"

"Lafiyar ce zata kawo mu wannan makararran gida a bahagon tunaninki na dabbobi ko ban tambaya nasan ke ce Salma!"Sannu 'Yar matsiyaci da matsiyaciya!"A Jere ta zubo wadannan magangannu kafin ta karaso!"Minal Kenan."

"Haba malama ya zaki shigo mana gida ko sallama babu kuma cike da magana maras dadin ji bare sauraro!"In ji Salma cikin bacin rai tana kallon su!"

"Dariya Minal tayi tare da karewa gidan kallo tace wannan ne gidan!?Aini wallahi na dauka ma gidan ajiye gawar mahaukata ne!"To bazamuyi sallamar ba bamu iyaba sai ki koya mana!"

"Inna ta ce kuyi hakuri bayin Allah kunga bai kamata ku shigo har gidanmu ba sallama ba maganarki sannan kuce zaku ci zarafin mu shin daga ina kuke?Me ke tafe da Ku?"

"Minal cire glass din idonta tayi ta kalli inna da salma da ke tsaye ta watsar sannan ta maida glass din mazauninsa tace Ashe dai tsohowar nan kina da sauran hankali da kinka iya tambaya wadda ta dace!"

Sunana Minal ni ce Matar da Dr.Salman zai aura nan da sati biyu nazo in muku kashedi ke da yarki ance min Ku mayu ne idan kun kama Baku saki!"To kusani kurwar yayanah Salma tafi madacci daci!"Daga yau babu ke ba mijina idan ba haka wallahi zansa a batarda ke a duniya!"Kisani salma nafi karfinki haka ma Yaya salman yafi karfin 'Yar tsiya Ahlil kwakwaf irinki!"Kije ki nemi dan talakawa kamar ke ki Aura!"Ni minal nice zabin salman kuma ajinsa ba ke ba banza ballagaza!"Narasa me ya gani yake so in banda kaddara an magancesa daga talla watakil!"

"Tabbas haka yake qawata inji Nidal sannan ta karasa wurin Salma ta dafata ta ce"Malama Salma wannan umurni muke baki ba shawara ba!"Wane karambani ya kaiki ga mannewa dan masu Arziki saboda kwadayin abin duniya!"Ki duba acikin fadin qasar nan tamu ta Nigeria gaba daya atarihin auren 'ya'yan mayan mutane duk auren bani gishiri in baka manja akeyi haka gefen talaka sai talaka to akanki kike son afara auren kunya da takaici!"Auren da ba za'a iya wani abun azo agani ba!"Gwara tun wuri ki kama gabanki kije can ki nemo mudi ko tanko ki aura dan Dr.Salman na Brr.Minal ne ita kadai idan ba haka ba daga ke har iyayenki zaku hadu da Bala'i da cin mutuncin da zai iya zama ajalinku.....!"

"Hannu Salma tasa ta kabe hannun Nidal da ta aza a kafadarta cikin fushi ta ce Wallahi kunyi kadan kuma ta Allah ba taku ba!"Kusani kunyi kadan Ku shigo gidanmu kuyimana abinda kukaga dama!"Ni ban damu Salman ba ku ya dama da har zaku zo fada da rashin mutunci akan shi kuma shi ke bibiyata !"Shi ke so na!"Kuje Ku masa fada ya daina sona!"Sannan kisani ke Minal dukan da nayi maki yafi wanda zakiyi min har abada!"Ni zuciyata kika daka saboda ki gayamin magana mai zafi!"Amma ni rayuwarki na daka inda baki ganin ciwo bare ki magani!"Na lura son maso wani kikeyi to kisani sona da kaunata sun riga da sun zama jinin jikin Salman."Duk da kasan cewar ina diyar talakawa amma a hakan nayi tagomashi da farinjini awurin shi duk dukiyarsa yace yana sona!"kuma Ina da masoya ban taba maular masoyi ba bare tada harshe na akan shi, nagode Allah!"Kuma har gobe ina qara gode masa da baiyi min kwakwalwa irin ta jahilan dabbobi ba, da bazan iya bambance tsakanin Kaddara mai kyau da marar kyau ba, Alhamdulillah mu talakawa ne kuma muna alfahari da jarabawar ubangiji kuje diyan masu arziki da za'a saku kabari da arzikin Ku....!"

"Taaataasss!!taas!Salma taji saukar marin da minal ta yi mata cikin fushi!"Har ta daga hannu ta rama tayi daidai shigowar Babnta sai ta fasa!" da sauri ya qaraso yace subhanallahi!"Baraka lafiya?Me salma tayi musu!?"Salma ban yadda ki daki kowa ba acikin su kiyi hakuri!"

"Salma da ke dafe da kuncinta tana zubda hawaye ta ce toh Baba!"

"Dariya sukayi suka tafa minal tace haba tsoho ai idan yarka ta tabani to da baki dayanku sai kun mutu agidan kaso dan ba wanda ya isa ya fito da Ku!"

"Ke kuma kashedi zan miki na karshe kisani idan ina magana ba'a mayar min da martani ko martani masu zafi ki kiyaye ni, kuma ba ke ba mijina, banza! mai bin maza! 'Yar iska! matsiyaciyar banza!"Minal tacewa Salma." ta kalli Baba da Inna da ke zugum suna sauraren su tace nadawo kan ku"Tsoho da tsohuwa nasan......."

"Da sAuri ya karaso wurin....Yaya Habu shin lafiya mukaji hayaniya na tashi inji kawu tare da su karime ko wanne lungu na gidan kowa ya fito yayi tsaye suna kallon minal da Nidal cikin shigar su ta rashin mutunci!"

"Minal cigaba tayi da maganarta ina son kujawa yarku kunne tafita da harkar mijina Dr. Salman nasan kuna sane yafi karfinta amma saboda kwadayi da son abin duniya kunka kyaleta!"

"Kawu Bala ya amshe maganar minal yace"Hakane wallahi sai da na fadawa yarinyar nan da Yaya habu ku fita harkar yaron nan mai kudi kun kace shi ke bin salma Ai ga irinta nan dama ance kwadayi mabudin wahala!Azo har gida aci mutuncin mu!""Dan Allah kuyi hakurii...!!!Dakata Bala suwa zaka ba hakuri wadan nan yara marasa tarbiyya da mutunci!"Kufita Ku bamu wuri marasa kirki yara!"Baba yace ranshi abace."

" Jakarta ta bude bandir din kudi yan dari biyar ta dauko da batasan yawansu ba ta jefawa Kawu Bala cikin gadara da sauri ya capke kada sukai kasa," Tace goronka ne na fadin gaskiya kai kuma tsoho meye acikin gidan ko dai kango ma," ai wannan baikai darajar akira shi da gida ba!"Zamu tafi amma kasani yarka ce marar mutunci ba mu ba!"Mu tafi Nidal tsaki Sukayi suka wuce su ka bar gidan."

Kawu Bala har yaso yabisu yacewa minal ya gode da wadannan dambun kudi da tabashi amma yana tsoron Yayansa saboda ya ga ranshi ya baci matuka!"saurin Barin wurin yayi kowa ya bishi saboda kudin da yasamu suma araba da su!"

"Salma barin wurin tayi tana kuka!"Dan anci mutuncinta da na iyayenta amma ta dauki alkawarin sai ta ramaabinda Minal tayi mata tunda har Salman na sonta to aikinta da kudurinta zaizo da sauqi!"

"Inna baraka ko kayan salma ta duka ta kwashe ta shiga cikin dakin tana share hawayenta!"

"Baba ko Alwala yayi yabar gidan zuwa masallaci saboda aduk sanda ranshi ya baci can ne wurin zuwansa sai ya huce ya dawo gida!"

BAKAR AKIDA

©TASKAR NABEELA DIKKO

® PEN WRITERS ASSOCIATION

Page 36/40

*"An karbou daga Abih sA'idul khuduriy (R.A)Ya ce,"Annabi Muh'd (SAW) ya ce"Hakika Mafi sharrin mutane,Masu mummunar masauki agurin Allah ranar Alkiyama sune wadanda mutane suka guje musu saboda yawan ayyukan su na Alfasha(Marasa kyau)."Bukhari ya ruwaito."*

________________________________

"A hanyar su ta komawa gida sai murna sukeyi suna shewa saboda sunyi abinda ransu ke so."

"Nidal ta ce,"Kin san Allah minal magangannun da kika yiwa baban salma sun min zafi saboda haka kawai naji ya bani tausayi!"
Chapter 5 · 0% Book details