← Book details Bakar Akida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 14

Sashe 13

Bakar Akida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hakane Sa'adatu ni yanzu komai ya kwance min,Yanzu ace ni da yar uwata uwa da uba daya munyi kare jini biri jini!"Ku abin da sauki tunda ku tobasanmu ne!"Ni fa Har marina sai da tayi akan auren nan!"Shiyasa naso minal ta hakura amma son salman ya hanata ta barshi tare da goyon bayan mahaifinta!"Domin ya ce aure ba fashi sai anyi!"

"To yanzu ita minal auren nan zatayi inji Hafsa cikin mamaki!"Tana duban Aunty zainab!"

"Ya zanyi Hafsa tunda sun ce sunji sun gani zasu iyah! nikam nace ba ruwana da auren....!Haba Yaya zainab kuyi hakuri mana idan kince ba ruwanki da auren ai kamar kin zuba fetur ne awuta kina jiran ta tashi da rayuwar minal!" saboda bazata taba ganin haske a auren ba matukar babu yardar ki alamarin!"Dan Allah kiyi hakura ki saka musu ALBARKA.!"Inji saudat cikin sanyin murya.!"

"Mtwsssssssss!!!"Hafsa ta ce kana ta dubi yaya Sa'adatu da zainab ta ce kunji wannan santobola!"To idan bata nunawa minal ranta ya baci ba ta ina zata gane kurenta ai gatane da yanci ake nema mata!"Ace kamar minal mai ji da kanta da ilimi da kudi zatayi rayuwa da kishiya ko banzar ma 'yar matsiyatw da batasan arziki ba!?"

"Yaya Hafsa ina son ku ajiye wannan *BAK'AR AK'IDA* Kuma ku ajiyeta agefe saboda ba addini bace al'adace irin ta marasa ilimi ba dole sai anyi auren kwarya tabi kwarya ba kowa zabi nagari ya kamata ya nema awurin ubangiji sann.......!"

"Dakata alaramiyya shehiya munji mu jahilai ne!"Kina ganin ke wata mai ilimin addini ce dan kawai kinga ke ce kinka taba sauke alqur'ani mai girma acikinmu!"Shi ne zaki taramu kina mana wa'azi ko said at.!"To Alhamdulilah dan muma mun san wasu surori!"Wallahi idan na karajin bakinki acikin maganar mu sai ranki yayi mummunan baci!"Inji Hajiya sa'adatu cikin takaici!"

"Ta kalli Yaya zainab tace kiyi hakuri kinsan iyayinta da nuna ita takwarai ce!"

"Dan Alllah yaya kuyi hakuri dukan ku!"Inji saudat!"

"Ba komai ya wuce malama sauda!"Inji hjia zainab."

"Daga nan cigaba sukayi da tufka da warwara akan maganar da yadda zasu bullowa al'amarin Hajiya maigado,Minal,da salman da kuma Abban minal!."

BAKAR AKIDA!

© TASKAR NABEELA DIKKO

® PEN WRITERS ASSOCIATION

Page 96/100

LAIFIN DADI KAREWA

ALHAMDULILLAH!

_WANNAN SHAFIN KYAUTA CE GAREKU_ 👌🏼

_'YAN UWA DA ABOKAN ARZIKI INA MUKU FATAN ALHERI_

_MASOYAN LITTAFAI NA BANSAN ME ZANCE DA KU BA A DALILIN SO DA KAUNA KUNA CIKIN ZUCIYATA KWANCE,NI DA KU SAI DAI FATAN ALHERI ALLAH YA BAR ZUMUNCHI MAI DOREWA ATSAKANIN MU AMIN,SO DA QAUNA NI DA KU YANZU AKA FARA, ANA TARE_ 🤝🏻

🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚

"A yau Jumma'a 22/2/2019 ne aka daura Auren Dr.salman Tahir Galadima da Barrister minal Maina akan sadaki naira dubu dari da hamsin."

"Sai kuma na Malama Salma Abu Sufyan akan sadaki naira dubu hamshin."Daurin auren da aka gudanar a sheikh Abbakar gumi Mosque bayan an kammala sallar jumma'a, Auren na su ya samu halarta dinbim manyan mutane da yan boko, kama kan gwamnan Jihar Kebbi manyan yan siyasa har ma abokan marigayi Tahir da justice maina da Jama'ar kauyen su Malam Abu Sufyan da sauran yan uwa da abokan arziki sunzou sun kuma sanya albarka abin ya qayatar,Musamman Abokan Dr.salman na India da U.s duk sun zo,Da sauran likitocin da ke jahohin nigeria,Shi da abokinsa Dr.jameel sunyi kyau matuka domin shigar su irin daya ce,Bama za'a banbamce waye angon mace biyu acikinsu ba,Sai an cinka saboda sun hadu karshen haduwa acikin tsadaddar shigarsu ta alfarma."An kammala lafiya daga nan suka wuce grand fishing park da ke garin na Argungu domin cin abincin liyafar angwaye da aka shirya ta musamman."

"Gefen Hajiya Mai gado sai dai San barkah domin alheri ne ke kwaranyo mata ta ko'ina."Gidanta ya cika maqil da abokan arziki da makota saboda Hajiya mai gado na kyautatawa makotanta."Abin dai ba'a cewa komai HAjiya Raliya uwar kirjin buki sai hadahadar fama da jama'a takeyi cikin shigA ta alfarma domin sunyi kyau matuka ita da Hajiya mai gado cikin shadda gizna kalar ruwan hoda da tasha pent work mai kyau,Gold masu tsada ne awuyan su hannu da kunne sai dai masha Allah Dan sun sha light make-up,Duk falon cike yake manyan mata yan kasuwa ma'aikatan gwamnati sai faman tande-tande abinci da abin sha kala-kala akeyi domin babu ce kawai babu agidan Hajiya Bilkis(Mai gado)."Wacce tuni ta manta da danginta da *BAK'AR* *AK'IDA* Ta hanasu halartar auren ko ba komai abokanta yau sun share mata hawaye!"Domin dimbin jama'ar da ke buki budiri a gidanta said dai ta ce"Alhamdulillah."

"Gidan Malam Abu Sufyan mai walda ne cike tinjim da jama'ar binni da kauye sai kidin kwarya akeyi da gud'a mata na raqashewa."Karime ce tsakar fili da su luba da hure harma umaima sai kwasar rawa akeyi ana kakkaryawa cikin murna da farinciki yan uwa sai liqin goma ashirin sukeyi!."

"Salma an sha make-up mai kyau cikin rantsattsen Material dinta maroon da silver head tasha adon sarka da yan kunne silver masu kyaun gaske takalminta Hill's da yar qaramar jakarta duk silver color."Fadan irin kyaun da salma tayi ma bazai fadou ba."Duk gidan sai faman qamshi yakeyi,"Inna baraka ma ta hade cikin swiss less dinta mai kyau kamar ba ita ba."Baba larai ko tana sashenta kunshe tana taunar bakin ciki kamar ta hadiye zuciyarta ta mutu!"Duk da taso kange yaranta kar sutafi gurin amma INA!"Dukkan su sun wuce suna shan shagali ita kadai suka bari kamar mayya!"

"Yan uwa da abokan arziki sunyi bajinta domin kuwa sun bayarda gudun muwarsu sun inna sun samu alherai da damage."Kowa ya CI ya sha anyi hani'an sai bararrajewa sukeyi cikin jin dadi."

"Gidan Justice Maina cike yake da jama'a maza da mata."A sashensa manyan mutane abokansa da yan uwansa sai fira ake ana raha abinci da abin sha ne ajiye firjit a katafaren falon nasa sai taya shi murnar auren minal akeyi mashi kuma yanata godiya da nuna jin dadin sa."

"Barrister minal maina ce zaune tsakar qawayenta ta sha kyau har ta gaji!"Da ganinta kasan cewa dalolin naira ne kwance ajikinta domin "ance ido mudu ne" ko da ba'a fada ba zai auna."Haka ma Nidal da Ilhaam sunyi kyau sosai da sauran abokan su duk sun zo."Sai ciye-ciyen kayan dadi sukeyi kafin time din dinner yayi da abokan Dr.salman suka shirya musu."

"Hajiya Zainab Maina zaune cikin matan abokan mijnta da danginta su Sa'adatu hannatu hafsatu da sauda dai sauran yan uwa da abokan arziki."Sai faman hidima sukeyi cikin jin dadi yayinda Hajiya Zainab ke boye damuwarta kada mutane su fahimta domin akan dole ne ta aminta ba dan ranta ya so ba!"

"Hakan dai ta faru akowane bangare shagalin buki buduri sukeyi."

"Kawu Bala sai kwasar wasa wasar buki akeyi yana d'aga kwalbar fanta sama..."Bakinsa kamar zai tabo kunne kan dadi saboda ya samu kudi sosai wurin su Salman."

"A gefen salman din ma sai san barkah domin abokan sa sai tsiya suke masa suna kiransa da mijin Mace biyu."Shirin sukeyi sosai domin zuwa daukar amaren aje dinner."

*8:33 PM*

"Salma ce gurfa ne agaban Babanta da inna suna yi mata huduba mai ratsa jiki da zuciya!"Ba abinda takeyi sai rera kuka!"Mai tsuma zuciyar mai sauraro!"Inna ce ta katse mata tunani!"Da ta ce kin ji duk abinda mukace da ke salma ina so ki rike su kuma ki Santa su azuciyarki kada ki dauki Munanan halaye da *BAKAR AKIDA* wadanda ba irin naki ba!"Kin ga dai salmanu yayi miki komai a rayuwa ba abinda bai saya miki ba agidanki duk da ba hakan mukaso ba,Amma ya hana muyi maki komai ,dan hakan kiyi biyayya Allah ya Baku zaman lafiya Ameen."

"Baba ya ce yanzu kuje bala da larai suyi mata nasiha da gwagwanninta da iyayenta Kinji Baraka kuma zan tsaya abakin kofar gida no zan kai ki salma gidanki da kaina ba wani wuri na Bidi'a da zakije dan bazan aminta da ayimaki walima dazu da Yamma sannan yanzu ace zakije wurin kidi sam ba zai sabo ba!"

"Inna Baraka ta ce"To Malam za ayi yadda kace tashi muje salma."Tallafota tayi tana share mata hawaye suka wuce!"

"Sashen Kawu bala Gwaggo Hanne ta wuce da salma yayi mata huduba sosai"Daga nan ne tace to larai ga salma ta zo neman gafararki"A dakile tace Amara Allah ya raki taki gona ya yafe mana!"Larai tace tare da shigewa dakinta!"Kawu Bala yace ke hanne Ku tafi abinku Allah ya ba su zaman lafiya kubarni da ja'ira mai baqin hali!"Hanne tace to Yaya Habu mungode Allah ya nuna manager nasu karime."Ya ce,"To Amin Sai kun dawo."Tuni suka dauki haramar barin gidan bayan nasihohin da yan uwa da abokan arziki sukeyi ma salma."

"Babu yadda abokan salman basuyi da babanta ba! amma fir yaqi!"Yace bazataje dinner ba dole suka hakura suka kai salma a Katafaren gidanta."

"Gefen ango Dr.salman ko sai faman bude ido yake domin yaga ta ina zai ga sarauniyar mata salma zata fitou."Sai dai kash!Minal ya hango kamar wata queen da abokanta suna biye da sauran danginsu abayanta haka Hajiya mai gado da abokanta sun sha ado da gwalagwalai da gani ba sai an fada ba kasan cewa wannan Bukin na 'yan gata ne masu arziki ."

"An gyara wurin ya sha kyau wato Dancing Arina Argungu,"Kujeru ne na alfarma aka ajiye,Domin zaman manyan mutane maza da mata kayan makulashe ne ajiye agaban su."A kan higher table ko zance bai faduwa domin wurin ya sha kyau da ado,"Dr.salman ne atsakiya gefen daman kujerar da aka tanada domin salma ne abokinsa Dr.jameel ya zauna gefen hagun shi minal ce zaune sai wani shan qamshi takeyi tana jin dadin labarin da suka samu akan salma bazata zo ba!"
Chapter 13 · 0% Book details