← Book details Bakar Akida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 14

Sashe 2

Bakar Akida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Watarana da salma tayi rashin lafiya ne sai innarta ta kaita asibiti sai Dr.salman ya duba salma sosai harda bata magani da yayi mata allura to irin yadda salma take kuka alokacin da yake mata alluran ne har yaji ta burgeshi daga nan ya sauke su gida kuma ya fara bibiyarta tun bata kula shi har tafara kula shi saboda yanda ya ke ba ta kulawa da tausayinsu tare da taimakonsu da yakeyi har dai soyayya mai karfi ta dunke atsakanin su."Ba yadda baban salma baiso ya raba salman da yarsa ba!" dan kuwa ruwa ba sa'an kwando ba ne" amma abin yaci tura domin salman baya jin kora da wulaqanci idan dai akan abinda yake so ne."A hankali tun salma bata nuna masa so har tafara saboda irin yanda ya ke nuna mata so da kulawa duk da alokacin tanada shekaru 20 ne aduniya amma tasan cewa salman ya ci akirashi da mai sonta na gaske Dan baya dubin yafi karfinsu kasancewarsu marasa hali."

(So ne hana ganin laifi inji yn mgn lol)

"Tun minal na yarinya qarama take son Yaya salman dinta,Dommin ada can baya gidansu take zama tana hutu,yana sonta tana sonsa irin na kurciyar nan to shi ne ita har xuwa girmanta bata daina ba tun iyayensu na daukar abin amatsayin kurciya har aka gano lalle son salman acikin jinin jiki minal ya ke."Hakan ne ya sa iyayensu mata suka shiga cikin zancen saboda masifar son da minal keyiwa salman."

"Amma shi sam da ita da iyayensu basa gabansa kan maganar hadasu auren! saboda shi halaye da dabi'un minal basu yi masa dan kuwa batada kamun kai bare ilimi da tarbiya ga ta sangarta da rashin kunya da yayiwa rayuwarta katutu."

"A rayuwar salman yana son mace mai tarbiya ilimi da alkunya ba watsatsiya kamar minal ba saboda yana son ya samawa yaran sa uwa tagari wacce zata kula da rayuwarsa da ta yaransa."

BAKAR AKIDA

©TASKAR NABEELA DIKKO

®PEN WRITERS ASSOCIATION

Page 11/15

_"Duk abinda ka raina, shi wani ke so aduniya, yi kokari kayi amfani da damarka, domin daya ce, idan ta wuce bazata dawo ba,Zama mai dubin na kasanka da wanda ka fi, domin kallon Wanda ya fika komai Babbar kasada ce."_

NASIHA CE!

"Inna Baraka ce zaune akan wata tsohowar tabarma da ta sha rana kuma ta ga duniya harta rarake!" ita da 'yartah Salma dubanta ta kai gareta ta ce"Salma a kullum ina maki fadan akan yawan tunanin nan da kikeyi!"

"Ina kara horonki da ki debe soyayyar Salman azuciyarki!"Hanyar jirgi daban da ta mota!"Duk kin wani ki rame!"kina damar da kanki kin sani ko Salman na sonki uwarsa ba sonki takeyi ba!"Har nan gidan ta zo kwanakin baya ta zazzaga mana rashin mutunci!"Tayi mana kashedi kuma ta riga ta gina katanga atsakaninki da Salman!"Ba ke ba shi!"

"Kinga ko salma dole ne ki hakura da salman ko kina so!"Ko ba ki so!"Masu kudin nan da kike gani auren kwarya tabi kwarya sukeyi bani gishiri in baka manja!"Kin ga ko gwara kowa ya tsaya inda Allah ya ajiye shi."Ki daure Mu mikawa Allah lamurran mu sai mu ga haske acikin su"Ni kaina ina jin zafi da tausayinki araina!" saboda nasan kin rasa mai sonki wanda baya dubin yafi karfinki Salman yaron kirki ne mai mutunci Wanda ya cancanci ayaba masa."Fatana Allah ya musanya maki da mafi alheri!"

"Salma hawayen da ke zuba tun a lokacin da Inna tafara maganar har yanzu ne ta share a fuskarta azuciyarta ko zafi ne ke ta fita."Ta nisa tace "Inna na hakura kuma In shaa Allah zan cigaba da addu'a Allah ya musaya min da Alheri."Zanbi umurninki!"Daman tsautsayi ne irin na so nasan cewa salman Dan masu kudi ne yafi karfina!"Allah ya yaye min damuwata!"

"Ameen,Salma hakan nike so kinji kiyi hakuri."Yanzu tashi muje mu fara surfen can!"Kar azo amsa ba mu karasa ba!"

"To inna muje!"Allah yasa mudace"

"Ameen."Wurin turmi da tabarya suka nufa dan karasa surfen su."

*********** "Na Shiga uku mummy na rasa me na yiwa Yaya salman!"Ya tsaneni baya sona!"Baya kaunata!"Idan nakira shi wulaqanta ni yakeyi!"Baya kula dani da sonsa da nikeyi!"kamar ni ba jininsa bace qanwarsa kamar Ilhaam !"Mummy Ku aura min ya salman ko da sonsa zai zamo ajalina!"Mummy ko gawata ce ku kai agidansa domin cikar burina!"Son sa zai kashe ni!"Minal ta qarasa zancen cikin kuka da karaji!"

"Mummy kara rungumo minal din tayi cikin jimami da bacin rai!"Ta ce"Kiyi hakuri minal aure tsakaninki da salman kamar anyi an gama!"Ki daina zancen mutuwa idan kin mutu ni da dadynki rayuwar mu taqare saboda son da muke maki bazamu jure rashinki ba!"Yanzun nan gidan Yaya mai gado zani na gaya mata!"Abinda salman ke maki da irin cin fuska da zarafinki da yakeyi yayi kadan ya wulakanta ki!"Dan kawai Allah ya jarabceki da sonsa!"To wallahi yau za'ayi ta takare!"share hawayenki bari kuka domin na marasa gata ne."

"Mummie Har kinsa naji dadi da sanyi araina shiyasa nike sonki!"Idan kinje Ki nuna mata ranki ya baci saboda harke baya girmamawa kar kibar gidan har sai an tsayar da maganar auren mu!"Kuma wallahi cikin satin nan sai na nemo ko yar gidan uban waye yake wulakanta ni akan ta zan shirya komai domin wulaqanta ko wacece!"

"Hakan yayi kyau minal!"Yanzu bari na wuce ki kira su lami su baki abinci ki ci ki koshi ki kwanta ki huta kinji Durlin."

"Okay mum sai kin dawo ki gaisheta."

"Zataji."Sai nadawo ko gobe idan mun hadu kinsan idan kina bacci ba a tashinki!"

"To sai dai naji ki, adawo lafiya."

"To mumy ta ce,"ta wuce abin ta."

"Salman ne da abokinsA Jameel tsaye jingine da motarsa Bugati (Brown colour)a kofar gidan su Salma wanda akalla sunyi 20min a tsayen suna jiran fitowar salma."

"A hankali da sanyin jiki ta ke tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki"Da sallama ta kara so wurinsu da hijab dinta har kasa."Cikin ladabi ta gaishe su."

"Jameel ne ya amsa mata."Dan kuwa tuni salman ya Shiga duniyar tunani ba abinda yake son gani kamar salma da take tsaye agaban sa Kallonta yakeyi kamar madubi."

"Sun dauki wani lokaci ita da jameel suna tattaunawa yana bata baki dangane da yanayin soyayyar su da salman da matsalolin da suke fuskanta." daga bisani bayanin irin son da salman ke mata yaqara jaddada mata."A karshe wuri yabasu domin waqa abakin mai ita tafi dadi."

"Sun dauki mintuna kafin salma ya yiwa salma magana."

"Ya ce salma kin daina so na yanzu!? kin daina kulawa da ni!"kin daina amsa kirana!"Meyasa!"Shin kinsan yadda hankalina ya tashi!"Na shiga tashin hankali mai yawa saboda duk wata kafar da zamu ga juna kin kulleta!"Ko yanzu nasan alfarma ce nasamu kika fito!"Me nayi maki ne?"Salman ya ce cikin kunar rai yana kallonta!"

"Idon ta yacika taf da hawaye ta daga idonta ta dube shi kana ta ce,Salman ba kai min komai ba amma *BAK'AR* *AK'IDA* ce tayi komai arayuwar mu!"Ita ce ke kokarin gina Katangar karfe atsakanin mu!"Muyi hakuri ka nemi zabin iyayenka daidai kai!"Nima na samu iri na talaka na aura, kwarya tabi kwarya kowa ya tsaya in da Allah ya ajiye shi!"Ko yanzu Inna ce tabani umurnin in zo in gayamaka kabi zabin mahaifiyarka da umurnin ta domin tazo har nan tayi mana kasheki akanka dan haka nima iyayenah sun Gina Katanga atsakaninmu dole mu bar junanmu domin bin umurnin iyayenmu!"Ba domin ranmu yaso ba!"Kai hakuri Salman ka fita harkata....Kuka ne mai tsanani ya kufcewa Salma da gudunta ta shige gidan su ta rufe kofa."

"Salman awurin da salma ta barshi ya durkushe yana kuka!"Da hanzari jameel ya zo wurin tare da taso shi zuwa cikin mota yana bashi hakuri duk da bai San dalilin kukan nasu ba!"Amma yasan tatsuniyar gizo bata wuce k'oki."Nan take suka bar unguwar."

"Hello Nidal.."Kina jina?
"Eh Minal ya kike?"

"Lafiya qalaw, wani aiki nake so muyi da ke gobe kizou ina neman ki."

"Okay,Sai nazo."Inji Nidal."

"Nagode sai na ganki minal tace tare da kashe wayar."Wallahi na dauki alkawarin illata ko wace mayya ce!Ko wace sakarai!Banza!Kucakar da Yaya salman ke wulakantani akanta!"Ko 'yar gidan uban wace kasheta zanyi!"Sai dai nima akashe ni!"Lami ce ta katse zantukan da minal keyi azahiri kamar mahaukaciya ta ce,"Anty minal na gama wankin toilet din zan iya tafiya?"

"Mari ta watsawa Lami tace,Har kin isa in sakaki aiki kizo kice min kin gama ni zaki nunawa lokacin wucewarki ya yi!? meye amfaninki?"Idan ba bauta ba?"To kisani ke baiwata ce bakida amfanin kanki sai nawa!" Kuma ki koma acan toilet din ki zauna har sai kinyi awa biyu ki fito."Mtwssss banza yar talakawa da basu da cikakken hankali!"Wuce kibani guri!"Ta fada tana huci!"

"Lami da ke dafe da kuncinta kwallah na zuba a idonta tace ayi hakuri Anty!"Allah ya huci zuciyarki nagode!"juyawa tayi zuwa toilet din shiga tayi ta zauna ciki tare da rufo kofa domin bin umurnin minal!"

"Wadda ko ba komai ta rage zafi da radadi takeji aranta!" tafara rage haushi da takaicinta akan lami da kaddara ta fadawa."

(Ni kuma na ce Allah ya shirya minal da masu rayuwa kamar irinta ta Amin)

BAKAR AKIDA

©TASKAR NABEELA DIKKO

®PEN WRITERS ASSOCIATION

Page 16/20

" _An karbou daga Abdullah d'an umar ,Yardar Allah ta tabbata agare su yace,"Manzon_ _Allah(SAW) ya ce,Kunya na daga cikin Imani."Bkhari da Muslim ne su ka ruwaito."_
_Allah ya sanya mu acikin bayinsa masu kunya Amin_ ."

"To kin dai ji dalilin zuwana Yaya mai gado dole sai mun tashi tsaye akan lamarin yaran nan!"In ji Hajia Zainab(Maman minal)."

"Ba komai mummyn Salman yadda kin ka ce haka za'ayi in ji Hajiya mai gado da ya ke hakan ta ke kiran Hajiya Zainab wato(Mummyn salman)"
Chapter 2 · 0% Book details