← Book details Bakar Akida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 14

Sashe 6

Bakar Akida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mtwsssss amma ke Nidal anyi sakarya shi talaka maras gata kuma uban makiyiyar ta wa!wadda na tsana aduniya zakice kin tausaya masa!"Kenan har salmar kina so kuma kina tausayi ko!? saboda naga so yana tare da tausayi!"Minal tace tana duban Nidal cikin tuhuma! tare da sauraren amsar da zata bata."

"Haba!Qawata ta yaya zan so salma?Kawai a lokacin da kike musu madifa ne sai naga kamar bamu kyautawa iyayenta ba!Domin ba laifin su ba ne,Laifin na Salma ne!"Amma ya wuce ai mun musu horo mai shiga zuciya bazasu manta da mu ba kuma bazasu qara Shiga gonar mu ba!"Ko ba komai Barazanar mu zata hori kwadayin su."

"Atou Ni har kinsa nafara jin haushin ki saboda na tsani salma da duk wani da zai so ta wallahi!"

"Ni kinga ma abin haushi da takaici da yafi tsaya min arai bai wuce wancan bagidajen ba wato Yaya salman shi kuwa wace bacewar basirace zata sa shi ya so wannan kucakar dabbar yarinya da bata wuce ko sa'ar Suhaima ba (Qanwar Nidal) ni duk na raina ajin shi da miskilancinsa!"Abin ban takaici!"Da ban haushi wai akanta ma ne yake wulaqanta yake cin zarafina!"Na dauki alkawarin illatah banzan nan matukar bai fidda ita a rayuwar sa ba!"Sai naga bayanta, Nidal!"Qarashe maganar minal tayi muryarta na rawa yayinda ta qara gudun motarta saboda bacin rai!"

"Kiyi hakuri qawata komai ya zo karshe ke da Salman mutu ka raba!"Ba wani banza dan banzah da zai raba ku!"Ai yar gata sai dan gata Tawan."

"Murmushin jin dadi Minal tayi,Domin maganar Nidal tasa taji sanyi aranta da hakan suka cigaba da firar su a hanya suka tsaya *Marhabah Super market* suka sayi ice cream da sauran kayan makwalashe suka wuce abin su zuwa gida cikin jin dadi."

"Salman ne zaune a office dinsa duk wunin ranar bai ayyana aikin komai ba, fa ce tunanin sahibar sa Salma, babu abinda yake kona masa zuciya, irin yadda Salma tai masa gatanga da gidan su."A hakan yayi zaune da dakon tunaninsa inda agefe ga patients na ta jiran sa amma ya ce anema musu wani doctor shi baya jin dadi da hakan yayi sallama da amininsa Dr.Jameel,"Shi kuma yayi haramar komawa gida har ya kama hanyar gidansu amma kasa jurewa yayi karya kwanar da zata sada shi da unguwar su Salma yayi domin bazai iya jure rashin ganin ta ba na tsawon mako biyu!."

"Tsaye yake a kofar gidan,"Bayan ya aika yaro a sallamo masa ita a zuciyarsa yana fargaba kar dai tace bazata fito ba!"Yana cikin zancen zucin ne sai ga yaro ya dawo"Wai tace bazata zo ba kuma kayi hakuri ka koma inda ka fito"Yaron ya ce yabar wurin!"Subhanallah!"ya fadi afili me na miki salma da zaki yi min wannan danyen hukunci... !"

"Ba salma kayiwa laifin ba Salman mahaifiyarka da matarka da dukkan danginka kayiwa laifi da kake neman dauko cuta ka kai acikin zuri'ar Ku!"Baba ne da tun fitar su minal da yaje masallaci bai dawo ba sai yanzu ya ba Salman amsa.!"

"Kamar daga sama Salman yaji zancen Baba abin yazou masa wani iri!"A ladabce ya durkusa ya gaida Baba cikin nutsuwa da sanyin jiki ya koma irin kalar tausayi nan!"

"Amsa masa Baba yayi kana ya ce"Ina fatan lafiya Salman saboda ina so ka fita hanyar 'yatah Salma kaje ka rike matar da zaka aura!"Ka bi umurnin mamanka ka cikawa danginka burin su domin *BAK'AR AK'IDAR* su bazata barsu ka auri wacce zuciyar ka ke so!"Domin haka bakai ba salma!" Kasan kafi karfin salma Mu talakawa ne ba masu arziki ba!"Kuma Salmata bazata iya zama acikin daula ba, saboda bata taso acikinta ba!"Abin da nikeso kaja motarka kabar mana kangon gidanmu yanzu matarka da qawarta suka zo har gidanmu sukaci mana zarafi bamuji bamu gani ba!"Tun farkon haduwarka da Salma na sanarda kai kafi karfin ta mu talakawa ne, ba mutane muke ba acikin duniyar masu arziki!"Dan haka ina maka fatan alheri kuma ina code maka abisa son diyata da kakeyi da zuciya daya batare da tsangwama da dubin *BAK'AR* *AK'IDA* irin ta ku masu hali ba!"Nasan kana da mutunci kuma ina ganin mutuncika da kimarka salman to ka rikesu dan Allah daga yau kar ka qara neman Salma!"Nagode ka iya tafiya."Baba yace wa salman da tuni duniyar sama ke masa yawo maganar Baba ta yamutsa masa kwakwalwa!"

"Ganin Baba da gaske gida zai wuce abinsa ne yasa yayi saurin dawo hankalinsa ya durgusa kasa ya ce"Dan Allah Baba kayi hakuri kada ka hukunta ni akan abinda bani na aikata wallahi ni kaina na tsani *BAK'AR AK'IDA* nan tasu da batada asali da amfani na yarda samu da rashi duk na Allah ne kuma da talaka da mai kudi duk daya ne babu banbamci domin duk bayi ne na Allah!"Baba karku rabani da salma ina sonta tana sona kawai akan *BAK'AR AK'IDA*"Baba nasan Minal ce tazo tayi muku rashin mutunci kuma zan dauki mataki Dan Allah kuyi hakuri!"Salman ya ce yana zubda hawaye!."

"Tausayinsa ya kama Baba tallafosa yayi ya tashi tsaye yace babu komai Salman mun yafe maka bakai mana laifi ba!"Kuma munyi hakuri zan fadawa Baraka da Salma nasan zasu hakura Allah shi maka Albarkah!"

"Amin Baba nagode."

"Babu komai ni zan shiga daga ciki."

"Baba dan Allah kaimin alfarmar inga salma in bata hakuri!"

"Ba yanzu ba!Salman nasan salma bazata Saurareka ba!dan nasan cewa ta tsani ganin Bacin ranmu!"Ga shi yau agabanta anci mutuncin mu kuma na hanata daukar duk wani mataki da taso dauka saboda gudun hayaniya!"Amma ka tafi zan fada mata!"

"To Baba ina gaida su zan dawo idan an kwana biyu ta huce nafiso nabata hakuri da kaina!"

"To Salman Baba yace,tare da murmushi saboda yagano lagon shi, Da kallon tausayi ya bi Salman da yayi wani zuruzuru kamar wanda ya kwanta ciwo"

"Sallama sukayi Baba ya Shiga gida Salman ko ya wuce Direct gidansu Aunty Zainab ya wuce saboda ya hasala da minal amma yasan ta ina zaiyi maganin iskancinta da rashin mutunci!"Shi zata rainawa hankali!"

"Hajiya Maigado ce zaune a bedrum dinta gefenta qawarta ce Hajiya Raliya zaune agefen gadon da aka cika da laces,super,materials da sauran kayan da zasu bukata na bukin saboda shiri ake yiwa Auren na musamman."

"Hajiya Raliya cikin kulawa ta dubi qawarta tace,Yanzu Hajiya Bilki kina nufin duk tulin kayan nan masu tsadar gaske kin saye su kenan?"

"Dariya tayi tace,sosai qawata wannan ma soman tabi ne sai munje Dubai."Karfa kin manta aure ne yan dangi yn gata wadanda suka gaji arziki kinga dole ne mu nunawa duniya naira ta zaunu."Har tana kuka da hawayenta!"

"Lalle kice min zamu sha mamaki, kuma mu kan mu muje mukara shiri kan wanda mukeyi, saboda na lura auren nan na fito na fito ne,"To kenan dole ne mu kure adaka,ka da ayake mu afimu wanka mai cizo zan sauya wani sabon shiri"Hajiya Raliya tace cikin dariya da raha."

"Murmushi wanda yafi kuka!Ciwo Hajiya mai gado tayi tace Bari Hajiya Raliya abu daya ne ke ci min tuwo a kwarya wanda idan na tuna sai naji farincikinah ya gushe!"Shi ne yaron nan da har yanzu yaqi yarda ya so minal!"A kan tilas ne zaiyi auren dan kawai na tashi tsaye ne akansa!"

"B'ata fuska Hajiya Raliya tayi cikin mamaki ta ce wai shin kina nufin Har yanzu Salman bai ce yana son minal ba!?Kuma a hakan zaki xuba ido ya aureta!?To meye ribarki dan kinyiwa danki Auren dole!?Ina iliminki da tunaninki ina wayewarki Hajiya mai gado!?"Salman danki ne mai miki biyayya idan har kin kayi masa hakan baki masa adalci ba d'a ne abin alfahari ga kowa!"

"Kiyi hakuri qawata nasan cewa Zainab qanwarki ce kuma jininki bazan iya bata alakar Ku ba kuma bada wata manufa zan fadi maganar nan ba sai domin ita ce gaskiya!"

"Shakka banayi Zainab bazata yiwa yarta minal auren dole ba!"matukar salman ke son yartah, batason sa." To Da tuni an wuce warin,"Kisani yanzu farinciki ne take nemawa minal." kuma tana sane da cewa shi fa bayaso!"Aini aganina dukkansu 'ya'yanta ne, da babu son kai aciki da ta hanaki tilastawa Salman dan ganin an masa adalci a rayuwa!"

"Shawarata ki so abinda danki ke so, ki kuma taya shi neman farin cikinsa!"Meye aibun ita wadda kinka taba fada min yana so kwanakin baya?"

"Hajiya mai gado da jikinta yayi likis tace Batada aibu face talauci da yayi musu katutu a rayuwa!"Gaba da bayansu talakawa ne kinga idan nabari ya aurota sai aitayi damu a dangi ya zama na farko da ya fara auro bare (Talaka)Acikin zuri'armu kuma kinsan irin su ance abin biyarsu yakeyi har gidan aure!"Shi nike gujewa Salman kada ya auro mai farar kafa asamu abin yayatamu a dangi."👸🏻👸🏻

BAKAR AKIDA

©TASKAR NABEELA DIKKO

® PEN WRITERS ASSOCIATION

Page 41/45

" *Wannan page na ku ne Dangi na Dikkon Kebbi and Madawakin Kebbi Family's Allah ya sanyawa zuriya ALBARKA Ameen.* "

_"3rd February 2019,Wannan ranar ta kasance daya daga cikin ranakun alfahari da bazan manta da ita ba a rayuwata Alhmdllh acikin matakai rayuwa na samu nasarar d'ane mataki na biyu Fatana Allah ya tabbatar mana da alheransa Amin Nagode 'yan uwa da Abokan arziki Allah ya sanyawa zuriya Albarka yabar mu tare Amin summa Ameen."_ 🤝🏻

________________________________
"Amma a gaskiya Hajiya Mai gado kin bani mamaki yanzu akan wannan *BAK'AR AK'IDA* ne da batada asali bare tushe maras kan gado kike son takurawa rayuwar Salman."A wane hadisi ko aya aka hana mai arziki auren talaka!Tabbas talauci bai da dadi domin Annabi(SAW) ya ce mu nemi tsari daga talauci!" Amma kuma ba'a hana auren talaka ba!"Domin mutum ne kamar kowa!"Samu da rashi duk na Allah ne!"Ki gyara imanin ki Hajiya Bilkisu ki gane cewa Ko ke baki wuce komawa talakar ba jarrabawa ce ta ubangiji!"Ki bar salman ya auri wacce yake so."Saboda shi talauci ba'a gadonsa kuma arziki na Allah ne!"Inji Hajiya Raliya cikin yanayin damuwa."

"To Hajiya naji zancen ki amma yanzu ta ina ma zan fara!"Yanzu ya zanyi da dangina da Minal!."Hajiya mai gado tace fuskarta dauke da danasani!"
Chapter 6 · 0% Book details