← Book details Babban Yaro Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 23

Sashe 9

Babban Yaro Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Granny tace"Dama ganganci ne yasa ka karbeta kasan yanzu hannunta yayi ido komai kamawa take yi."
Wasa yake da baby din bama ya sauraran abunda granny take fad'a.

Duk hankalinsa na kan 'yar tashi.
*****
A ranar kiran gaggawa ya samu governor dashi da Amjadu daga fadar shugaban kasa, hankalin shi ya kai k'oluluwar tashi yasan halin mai girma shugaban kasa da zafi da daukar Serious ba tare da b'ata lokaci ba ya nufi babban birnin tarraya abuja, cike da ta tsantsar tashin hankali da nadama....

Lokacin da sak'on shugaban kasa ya samu Amjadu sam ba nuna wata fargaba ko tashin hankali ba, tabbas yasan gurin da zasu je ba gurin wasa bane dole yaje da shirin sa duk wasu matakan kare kansa ya tanade su hade da shaidu, yana jin jiki ya kira doh-doh a waya Wanda yake can asibitin malam Aminu yana kula da Rambo yace." Yazo yana Neman sa, a daran aka kira Ali wannan d'an jaridar shima Dole zai zama shaida a gurin duk da ba kutu zasu shiga ba amma yana ganin tafiya dasu tana da amfani......

Nan parlor muka kwana ni dashi da baby domin babu yanda banyi dashi ba kan ya tashi mu koma daki yak'i hakanan na zaune kasan kafet shi yana saman kujera a kwance baby gefan hannun shi inda babu ciwon ko kadan ban rintsa ba kamar yanda bai rintsa ba.

K'arfe hudu na asubah ya mike yana kokarin dauke baby a jikinsa mik'ewa zaune nayi da sauri na dauke baby na kwantar kan kujera, ya mike zaune, hannun shi na rike hade da tsira masa ido...

A dake yace." Menene.

"!?

Hawaye ne suka fara sintiri a idona nace" Wallahi ina jin tsoron zuwan ka abuja nan."
Tsaki ya ja k'asa-k'asa yace." Jiya kin kwana kina kuka ga rashin barci kan abunda bai shafe ki ba, na fad'a miki tun jiya wannan kukan da kike yi bashi da amfani Sam na tsane shi."
Hannunsa na saki na hade kaina da gwiwa sosai nake zubar da hawaye ni kadai nasan irin fargaba da take damuna akan wannan al'amarin gani nake yi idan ya tafi kamar yanda ya fada jiya za' muji mummanan labari!!!

Shashshekar kukan ta ne ya dame shi!

Dafe kansa yayi ya yunk'ura ya mike tsaye cikin k'arfin hali ya tsuguna gabanta tare da d'ago kanta suka fuskanci juna.....

Kallon-kallo muke ni dashi!!

Ga hawaye shab'e-shab'e a fuskata....

Fuskarsa yake matsowa da ita, nayi saurin rintse idona hawaye suka zubo, harshen shi naji kan kuncina yana lashe ruwan hawayen.

Nayi saurin bude idona ina kallonsa shima ni yake kallo kuma bai fasa lashar fuskata ba.

Naji wani irin Abu a jikina lokacin babu abunda nake so illah in jini a jikinsa babu hali da babu ciwo da babun abunda zai hana na rungume shi.

Sai da ya lashe ruwan hawaye na tas!

Sannan ya mike a nutse ya shiga toilet din parlor.

Jiki a mace na bishi da kallo har ya shige dakin , kwanciya nayi a gurin ina zubar da hawaye ni kaina kukan da nake yi ya ishe ni.....

Alwala ya dauro a gurguje ya futa k'arfe biyar da rabi ya dawo gidan kai tsaye dakin shi ya shiga ya sanya Riga da dogon wando jins shart din mai botira ce kuma bata da nauyi sosai saboda ciwon sa, a gurguje yake yin komai har ya kammala ya futo hannunsa rike da wayoyinsa yaji dad'i da ya futo ya tadda Asma'u ba tashi daga parlor baby dake bacci kan kujera ya mannawa kiss a kumatu yayi saurin futa saboda jin tsoron rigimar granny..

Yana futa Doh-doh da Ali na tsaye, take Ali ya bude masa mota ya shiga shima ya zauna kusa da doh-doh yaja motar suka futa daga gidan.

Kai tsaye airport suka nufa.
[12/9, 11:02 AM] .: *BABBAN YARO*
*79*
Gabakid'aya wad'anda suke fad'a aji k'asar najeria sun hallara a d'akin meeting na fadar mai girma shugaban k'asa, Amjadu ne kawai mai k'ananun shekaru a cikinsu, duk sun girmeshi nesa ba kusa kai harda wandanda suka girmi mahaifin sa a cikinsu kuma dayawa daga cikin su k'abilu ne saboda haka suke komai cikin hikima da nutsuwa, duk wani bunkice mai girma shugaban kasa ya gama yi kuma ya tabbatar governor Alkanawi shine bashi da gaskiya duk wani dauki ba dad'i da ake da a jahar kano ya sani kuma shine ya haddasa ta, bayan yayi rantsuwa da alkur'ani gaban bainar jama'a zai yi kula da jahar sa zaiyi mulki tsakani da Allah amma ya karya doka, babu shakka a abunda yayi ba k'aramin Abu bane ya wuce gona da iri ta inda mai girma shugaban kasa yake ganin dole a hukunta shi, kuma mulki ya bar shi har abada domin a doka ta siyasar kasa duk governor da aka samu da cin amanar kasa za'a hukunta shi kuma ya bar siyasa har abada don haka 'yan majalisa da hukumomin zab'e suka yanke shawarar juyin mulki ga mai girma governor Alkanawi domin su nawa jama'ar kano damar zab'o Wanda suke so ya mulke su daga nan zuwa wata biyu lokacin zab'e kenan....

Bayan nan kuma mai girima shugaban k'asa ya sanya dole hukumar Efcc ta tsaurara bunkice a kansa domin alamun rashin gaskiya sun bayyana a fuskarsa.

Wannan shine hukunci da aka yanke ga mai girma governor Alkanawi...

Bayan nan kuma Mai girma shugaban kasa da shauran k'ososhin k'asa suka jinjinawa Amjadu *Young millionaire* bisa ga NAMIJIN kokarin sa bisa kawo wa k'asar shi cigaba da jikinsa da kud'in sa da lafiya hak'ika idan k'asar najeria tana alfahari dashi da wannan aikin nasa.

Nan mai girma shugaba ya sanya hannu a wata ta karda dake gaban shi, ya mik'awa na kusa dashi shima ya sanya hannu haka har sai dai mutum goma suka sanya hannu a wannan takarda kana takadar tazo gaban Amjadu shima ya karb'a ya sanya hannu ba tare da ya fahimci me takardar mecece ba....

K'arshe ta kardar ta koma gaban governor Alkanawi, hannu na rawa ya sanya hannu zufa suk ta jika jikinsa shaddar jikinsa duk ta jik'e yana sanya hannu wani soja dake tsaye kusa da shugaban kasa ya dauki takardar ya ajeta kusa da shugaba shi kuma ya had'ata da wasu takkadu ya rufe!!!

Ambassador Aminu Ahli shine ya kalli Amjadu cikin turanci yace." Duk wani Abu da zaka yi a jahar kano Wanda kake ganin zai kawo cigaban kasa da talakawa mu zamu mara maka baya kaje kayi kanka tsaye zamu tallafa maka ni cikin asusuna na cire 50 Million's na baka domin kaje ka k'ara farfad'o da harkokinka da company ka da suka rusa, take jama'ar gurin suka dinga ma Amjadu kyautar ta bangirma Shi kanshi shugaban kasa sai da ya bashi 50 Millions.....*Innalillahi wa'ina ilahi raji'un* wanin hanin ga Allah baiwa ne *Amjadu Young millionaire* Ni Binta na taya ka murna hak'ika babu abunda yafi gaskiya a duniya dad'i wani lokacin akan yi maka Abu domin a kuntata maka amma daga k'arshe sai ya zame maka alkairi, Fad'ar irin mak'udan kud'in da Amjadu ya samu a gurin b'ata lokacine.

Mai girma governor Alkanawi kamar ya mace saboda bakin ciki.Take Sojoji suka tasa k'eyar Alkanawi suka futo dashi 'yan jarida da suke zaune a reception suka mik'e dama duk abunda yake faruwa suna kallo ta CCTV Camera aikuwa suka yi caaaa!

Kan alkanawi suna so suji ta bakinsa, ido jazur yace." Sharrin shad'ain ne kawai da zugar mutane gashi sun kaini sun baro da k'arshe ina Neman afuwa ga al'umar jahar kano bisa ga abunda ya faru."!!

Daga haka yayi shiru idonsa yayi wani irin jaaa sojoji suka tasa shi a gaba.

To hakace ta kasance kan Amjadu manya manyan 'yan jarida suka sanya shi a gaba dole sai yayi magana , babu yanda ya iya cikin turanci yace." *Hak'ika wannan ranar bani da kamar ta a duniya saboda Allah ya nuna min gaskiya ga gaskiya CE, Allah ya wanke ni bisa ga zargin da jama'a suke min Na tabbata ubangiji baya bacci kuma shi sharri d'an aike ne sunyi nufin cutata ubangji ya mayar da abun kansu saboda bani da hakki a Kansu nagode wa Allah da na tsalle ke wannan sharrin nasu kuma ina jinjina ga me girma shugaban kasa tare da mataikan sa hak'ika sun cancanci yabo da godiya a gare ni nagode k'warai da hallancin su a kaina."*
Abunda ya iya fada kenan ya wuce masaukin sa tare dasu doh-doh da Ali da yake cikin farin ciki da murna domin yana ganin dole ma ayi masa Karin girma gurin aikinsu saboda namjin kokarin da yayi.

Kafin kace kwabo garin kano ya hargitse da Sowa da murna gari ya hautsine da hayaniya kowa na fad'ar ra'ayin sa kan abunda ya faru, matasa dattijai duk sunji dadin wannan hukunci da shugaban kasa ya dauka dama sun gaji da mulkin Alkanawi don haka sai suka yanke shawarar tsayar da Amjadu a matsayin mai mulkar jahar su, take wasu suka futar da hoton shi a matsayin governor mai jiran gado nan da wata biyu suka dinga bin jikin gidaje da kan titina suna manna kasuwanni da shagunan mutane suka dinga manna hotonan amjadu a matsayin governor.

Duk abunda yake faruwa mun gani labarai Ya Aminu ya kirani a waya yana fad'amin min wai nasan abunda yake faruwa kuwa nace"Gani a labarai Ya Aminu ni bana son siyasa nan fa." !

Yace." Kiyi hakuri ki taya shi addu'a kinji ko."!

Ni dai shiru nayi kawai hankalina duk a tashe burina kawai ya dawo gida gashi na kira wayarsa ya kai sau ashirin bai d'aga ba.....

Daki na shiga nayi kuka na mai isata na futo na tadda Granny ta jurawa TV ido inda suka nuno Amjadu lokacin da yake bayanin godiya a fadar me girima shugaban kasa.

Ta kalleni idonta ya Tara k'walla tace"Zo kiyi min bayani me suke cewa ne naga sojoji sun kewaye shi, ga mutanan masu nacin tsiya sun kewaye shi da na'ura fadamin me yake ce musu jikina duk yayi sanyi.."!
Chapter 9 · 0% Book details