Sashe 14
Babban Yaro Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
" mik'ewa yayi zai wuce ta dakatar dashi ta hanyar fad'in"Nace dama ai mun dawo kusa dakai da zama duk inda zaka shiga muna 'kungun ka ko da ko gidan gwamnatin ne, arzikin mu ne."
Dariya Ta bashi don haka sai da ya dara tukkuna sannan yace." K'warai kuwa innah amma fa ni wannan mulkin ba son shi nake ba, don dai jama'ar gari sun matsa ne." Tace" A'a mu kam muna so zamu yi ta taya ka da addu'a.
" yace." Nagode Innah.''
Yana 'kokarin shiga d'akinsa tace" baka tambayi 'yar Uwar taka ba." Ajiyar zuciya ya sauke al'amarin Innah ya soma bashi haushi yace." Tana ina."?
Tsaki ta buga tace"Tana cikin d'aki kwance jiya daga zuwan mu matar ka ta 'kona ta da soyayya man 'kuli.''
Juyowa yayi cike da mamaki yana kallon Innahr tasa.
Granny tace"Haba Suwaiba a dinga Sara ana duban bakin gatari mana, ki bar shi yaje ya kwanta ya huta tukkuna kome sai a ayi ki duba da kyau ki gani yana tare da gajiya ga bacci jiya ya kwana yana ibadar aure."!
Ya'ke Innah tayi tace"K'warai zance ki haka yake ka shiga ka kwanta ka huta Idan yaso in ka tashi sai muyi maganar dole ka jawa matar kunne ta ga mutumcin mu domin mune kai baza ka tab'a janza mu ba."
Amjad ya 'bude dakinsa ya shiga yana mamakin maganganun Innah Suwaiba idan ya fahimci maganar ta tana nufin sun dawo gidan shi da zama kuma tana so ta cusa masa 'yar ta bayan haka kuma yanda ya fahimta tana so ta tayar masa da hankali a cikin gida, sai babban abunda ya d'aga masa hankali shine wai Asma'u ta 'kona Hafsa da mai a gaban granny Tayi maganar yaga bata musa ba tabbas zancan haka yake yi, dole ya sanya ido kuma ya tsawatar matsayin matar shi daban matsayin dangin sa daban amma Sam bazai lamunci zaman Innah Suwaiba cikin gidan shi ba yasan halin matar muguwar 'yar rigima ce.
[12/11, 10:30 AM] BintuUm@rAbb@le: Wayoyin shi dake kan drwoar ciki ya d'auki guda ya kunna tun jiya suke a kashe saboda yasan mutukar ya barshu a kunne babu shakka jama'a zasu dame shi shiyasa ya kashe su, yana kunnawa messages suka dinga shigowa ya aje ta kan bed d'in bathroom ya shiga ya had'a ruwa sosai yayi wanka ya futo daure da towel a kungun shi, ya zauna yana duba sa'konni mutane wasu ma Sam bai San su ba, suna yi masa fatan alkairi, sa'ko har daga Garin mahaifin sa Chadi ya duba iya Wanda zai iya ya aje wayar kwanciya yayi rigingine yana tunanin ta yaya za'ayi ya sallami Innah domin gaskiyar magana sun ta kura masa da sa ido mussaman granny yanzu da babu kowa cikin gidan yasan suna tare da matar shi amma parlor d'aya duk abunda zai yi idonsu na kai.
Tsaki kawai yake ja.....
Kira ne ya shigo wayar sa, yana dubawa ya numbar Ali 'Dan jaridar nan Ali ya wuce komai a gurin sa ya d'auki wayar had'e da sallama.
Suka gaisa cikin girmama juna Ali yace." Yallab'ai muna Neman alfarma a gurin ka idan zamu samu." Yace." Ali fad'i kome ye."!
Ali yace." Muna so zamu yi hira dakai a gidan redion mu yau da misalin 'karfe takwas na dare."
Jim!
Yayi yana tunani yace." Babu damuwa insha Allahu zan amsa gayyatar Ku.
" Ali yayi mamakin saurin amincewar sa, murna ya yi sosai yayi masa godiya kana suka yi sallama.
Aje wayar yayi gefan sa yana lumshe ido, minti biyu tsakani kira ya 'kara shigowa ya bude idonsa had'e da kallon fuskar wayar.....Hibbah sunan da ya gani yana yawo kan screen din wayar, tsaki yaja kawai ya share wayar har ta katse.
Wani kiran ya 'kara shigo .....
Dauka yayi ya k'ara a kunnesa ba tare da yace." Kome ba, ita kuma jin ya d'auka yasa ta ma'ke Muryar ta tana fad'in"Zumana ka ya dani ko."?
Yana sane yace." Wacece ke."?
Hibbah takaici ya ishe ta tace." Nice Hibbah mayar ka, duk wulakancin da zaka mun bazan yi zuciya ba ina sonka ina 'kaunar ka." Idonsa ya 'bude sosai yace." Ke baki da hankali ko bakin San abunda ubanki yayi min ba ne." ?
Take tace" Nasan kome zumana, kuma mahaifina a halin yanzu yana cikin tsananin tashin hankali da nadama shine dalilin ma da yasa na kira ka a waya ina me baka hakuri ko don darajar son da nake maka ka YAFE masa domin yana cikin halin damuwa.
Amjad yaji zuciyar sa nayi masa zafi da maganganun da take yi masa na shirme yo shi ina ruwan sa da Alhaji Hashimu mai citta can gasu gada kuma Allah ya raka taki gona, don haka a kaurare yace." Hibbah kike ko meye?
Ki kula ki kama kanki daga yau sai yau kar ki kara yimin magana makamanciyar wannan duk wata ukuba da mahaifin ki ya shiga shine ya jawa kanshi, ki dauka a rayuwar ki kamar baki ta'ba sanin Amjadu ba a rayuwar ki kuma ki fad'awa ubanki cewa ko da wasa kar ka kuskura ya shiga hurumi na idan bai wasa ba wallahi sai na d'aure shi."!
Hibbah ta fashe da kuka tace"Ni kaka fadawa wad'annan kausasan maganganun naka don kayi sabon aure kuma zaka zama governor shine kake min wulakanci kar ka manta da cewar Kaine ka fara keta min rigar mutumci na wallahi Idan bakayi wasa ba sai na tona maka asiri domin duk abunda ya faru a tsakanin mu dakai INA da pictures d'insa a waya ta."
Yace."Hibbah Idan baki fasa tona min asiri ba bakya 'kaunar Allah da manzon sa kije duk inda zakije ki fad'a cewa ni fasi'ki ne kuma nine na fara sanin ki 'ya mace wannan ba damuwa ta bace taki ce duk abunda zaka yi kije kiyi kanki zaki 'batawa suna a duniya."!!
Yana gama fad'in maganar shi ya kashe wayar zuciyar sa na yi masa mugun zafi haka kurrum yana cikin farin ciki da annushuwa Hibbah ta 'bata masa rai da Safiyar Allah.
******
Aunt Hauwa ce tayi sallama cikin gidan su.
Umma na zaune a rumfa tana lissafin 'kudi tace." Kece da yamman nan." Aunt Hauwa ta zauna kusa da mahaifiyar ta suna gaisawa tace"Wallahi daga kasuwa nake sai da na fara zuwa gida na aje kaya san nayo nan."
Umma tace"Hakan yayi kyau ai....
Aunt Hauwa tace"Jiya Aminu yaje min da wata magana wacce ta d'aga mun hankali mutuka." Umma tace" Humm al'amarin mutane na da ban mamaki wallahi mutuwa she kara goma sha biyar amma saboda rashin imani da tada zaune tsaye suka 'bullo mana da wannan maganar."
Aunt Hauwa tace"Ni wallahi abun yayi mugun daure min kai ayi abun nan tare da sanin shaidu da sanya hannun kowa amma daga baya a sanja magana."
Umma tace"Duk Ku kwantar da hankalin Ku insha Allahu kamar yanda suka buk'ata din zamu tashi mu bar musu gidan su ko hayane mu kama ai Shikkenan.
"
Aunt tace"Insha Allah ba zamuyi haya ba Umma zanje gurin Kawu Yunusa tunda akwai gurare cikin gidan shi ko d'aki guda ne ya baki ki zauna a ciki kafin mu San abun yi."
Umma tace"A'a ni bazan je gidan Yunusa ba kun San halinsa nayi sa dashi ma ban tsira ba balle INA kusa dashi ai har dukana ma sai yayi, Aminu yace." Inje gidan shi in zauna dakin nam na tsakar gida ni kam bana sha'awar zama da suruka gwara inje in biya 'kudina in San na biya babu me yi min wulakanci." Umma ta 'k'arashe maganar ta tana goge hawaye
Aunt taji zuciyar ta nayi mata zafi sosai tace"Umma me za'ayi da rashi talauci baiyi ba a rayuwa amma dole ne in Sanar da Asma'u halin da ake ciki a halin yanzu itace take da dama a hannu kuma mijinta yana da rufin asiri ko sa wani taimako da zata yi mana."
Umma tace"Kul!
Kar ki fara domin yin hakan zai zama kamar ro'ko me Asma'u take dashi da zata taimaka Idan ba so kike yi ki koya mata ro'ko ba zamu tashi daga gidanan ba tare da ta sani ba, Shikkenan daga baya sai taji kome ye."
Aunt Hauwa tace"Umma nifa bana sha'awar ki zauna gidan haya wallahi ki bari ayi wa Asma'u magana nasan insha Allahu a siri zai rufo." Umma ta futtuke bata so Dole aunt Hauwa ta hak'ura amma ji take kamar taje ta ciwo bashi ta siyawa Ummsn su gida su huta da ganin wannan bakin cikin.
To 'bangaran Ya Aminu ma tun da ya futa da safe take fafutukar gurin ganin ya samu gurin da Ummansu zata zauna abun ya fassakara da kyar wani abokinsa ya samo masa gida a kurna shima daki daya ne gidan mutum uku ne Umma ce ta hudu tace"Taji ta gani haka zata zauna.
Aunt Hauwa kamar ta mutu don bakin ciki haka ta tattara yana ta yana ta ta bar gidan zuciyar ta nayi mata suya.
****
*Assalamu alaikum jama'a kamar yanda muka shaida muku tun da safe cewa yau zamu yi hira da shararran kuma sanannen mutumin nan da kuka sani a jahar kano wato Amjadu AbulAbbas mainasara Wanda kuka fi sani da Young millionaire gamu tare dashi a yau zai fad'e mana biri har bindinsa zamu ji komai daga bakinsa."* d'an jaridar ya 'kare maganar sa yana gyara wa Amjadu Abun magana dake ma'kale a jikin rigar shi.