← Book details Babban Yaro Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 23

Sashe 18

Babban Yaro Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hamma!

Ta buga Muryar ta da alamun bacci tace"ta ina zanyi bacci ina jiran ka ka dawo muyi muhimiyar magana wannan yaron yazo ya matsamin da lallai sai nazo mun tafi sabon gida wai Kaine ka umarce shi yazo ya dauke mu." Amaj ya zauna cikin kujera cikin gajiya yace." Nine nace Yazo ya kaiku gidan tunda mun gama magana dake tun da safe."
Inna Suwaiba ta gyara zaman ta sosai tace"Har ka manta maganar da nace zamuyi da Kai ko." Sosa kansa yayi yace." Wallahi na manta Innah kin San abun da yawa kiyi hakuri."
Tace"Ai ya wuce kam har kullum muna yi maka fatan alkairi da zamowa shugaba me adalci." Yace." Godiya nake Inna."
Cikin kwantar da murya Innah tace"Dama Alfarma ce nake nema a gurin ka wacce nasan kana da damarta sai dai Idan baka yi NIYYA ba ko kuma matar ka ta hana ka amma abunda nake nema a gurinka Allah da manzon sa sun hallata maka shi kuma Kai kan ka zaka kara yin kwarjini ka zama cikkakan namiji mussaman yanzu da nauyi zai hau kanka yana da kyau ka amin cewa 'bukata ta "
Cikin.

"Kosawa sa maganar ta yace." Innah idan muna magana dake tsakanin mu ne don Allah ki daina sako iyalina a ciki Asma'u bata isa ta sani nayi abunda ban yi niyya ba wannan tsakanina dake ne ji fad'i ko wace irin alfarma kike so insha Allah idan da hali ni zan miki alfarma innah ke kin wuce ki nemi alfarma a gurina." Innah Suwaiba ta saki fuskarta sosai jin abunda Amjad din yace Tace." Dama ina so ka auri 'yar uwarka Hafsatu insha Allahu baka da matsala da ita nayi mata tarbiyya sosai zasu zauna lafiya da ita Asma'u mutukar wata futuna ta 'bullo to babu shakka daga 'bangaran ita Asma'u ne domin ni nasan yarinya ta me tarbiyya ce , bayan haka kuma Hafsa a kanka ta'ki sauraron d'imbun samarin ta da suke sonta da aure Tace dole kai take so, lokacin babu irin magiyar da banzo nayiwa kakar ka ba a kan mu hadaku aure ta bujere tare da fadin"Ita baza tayi maka dole ba katsaham!

Muka samu labarin auran ka da wannan yarinyar me rasuwa ina nufin mahaifiyar baby 'alamarin ya 'bata mana rai sosai ganin muna a matsayin iyayen ka, ka kasa zuwa ka sanar mana shiyasa muka yi fushi muka koma gefe guda hade da zuba muTo. ido sai bayan ta mutu kuma shima katsaham!

Muka ji auran ka da ita wannan d'in to da nayi bunkice sai na tabbatar da cewar kaima baka sani ba Allah ne ya nufin haka, to sai muka dauki abun a matsayin kaddara yanzu dukanin abunda ya faru a baya mun YAFE maka."!

Ta k'arashe maganar ta ta tana sauke ajiyar zuciya.

Dama tun kafin ta fad'i maganar ta ya fahimci inda ta dosa, don haka bai wani furgita ba yace." Innah idan muna magana dake a tsakaninmu ne don Allah ki daina sako sunan kowa ciki naji kina maganar cewa granny ta hanani auran Hafsa ki gafarce ni anan wallahi ba laifin ta bane granny tayi iya bakin kokarin ta gurin ganin ta 'kulla auramu Allah bai nufa ba, idan tuhuma zakiyi to ni zaki tuhuma domin ni na nuna bana ra'ayin yarinyar Sam bana sha'awar auran zumunci, kiyi hakuri don Allah ki bar zancan ni Hafsa a matsayin 'kanwa na dauke ta, insha Allah zan tsaya mata a kan kome idan ta samu miji zan yi mata aure kuma zan gantata amma maganar aure tsakanina da ita ki aje ta gefe.

Innah Suwaiba ta fashe da wani *Mashahurin* kuka tana fyace majina tace"Ta tabbata bani na dauki cikin ka ba yau tabbata ta bani ce na tsuguna na haifeka yau ta tabbata bani ce na shayar da Kai ba!

Yau ka nuna min *Aisha* ce uwarka domin nasan ita baza ta ta'ba umartarka da abu ka bujere wa bu'katar ta ba, Alhmdullahi Allah yasa nima na Haifa da yau nasha takaici."!

Cikin kuka me futar da sauti ta 'karasa maganar.
hankali a tashe yace." Innah!

Yi shiru don Allah ki daina wannan kukan da kike yi bana so, wallahi dukan abunda kika fada ba haka bane na fada miki a Yanzu bani da wata uwa da ta wuce ki kiyi hakuri kiyi shuru muyi maganar please."!!!

Inna Suwaiba ta fyace majina kamar ba dare ba sai d'aga murya take yi ta cigaba da cewa"Idan da ka dauke ni a matsayin uwa ai baza kayi min musu a kan magana ta ba hummm."!!

Amjad yace." To kiyi shuru muyi maganar kinga dare ne kar ki tashi mutan gidan kiyi shuru don Allah." Innah Suwaiba ta goge hawayen ta tana fad'in "To kai nake saurare."!?

Ajiyar zuciya ya sauke ya dafe kansa mintu biyu tsakani yace." Bukatar ki kawai in auri Hafsa ko.?

Ko numfasawa bata bari yayi ba tace" Shine bukata ta yaron kirki." Kallonta yayi idonsa yayi ja yace"Shikkenan Allah ya sanya alkairi.

" washe baki tayi tana zabga masa godiya tare da fad'in"Insha Allahu zaka yi alfahari da wannan auran tunda kayi min biyyaya."
Mik'ewa yayi yace." Innah ya kamata kije ki kwanta Shikkenan magana ta wuce na amunce.

" innah ta mike tana fadin "Allah ya tashe mu lafiya kaji yaron kirki gobe sai kara tusa maganar da tsayar da ranar d'aurin aure."
Wuce wa yayi ba tare da ya tanka mata ba yana mamaki ta sosai shi yanzu babu maganar aure a gabanshi sai bayan za'be tukkuna kome ye sai ayi ya amunce mata ne kawai domin a zauna lafiya sosai yake mamakin rigimar mata.

Ina jin motsin shigowar sa 'karamin Parlor na nayi saurin hayewa bed wasu masifaffun hawaye masu tsananin zafi suka kwaranyo min a fuskata.

Asma'u yini tayi cikin fargaba sanin da tayi cewar mijinta ya tafi yawon kafen dole tasan akwai ma'kiya da suka saka shi a gaba mafi a kasari ba'a futa a dawo Lafiya shiyasa ta yini tana yi masa addu'a samun nasara da dawo wa lafiya hankalin ta bai kwanta ba sai da taji shigowar motar sa gidan sannan ta saki ajiyar zuciya taje ta d'aga labulen window tana le'ken sa har sai da ya shigo sannan ta sauke ajiyar zuciya ta zauna tana jiran sa ya shigo shuru har kusan minti ashirin tayi tunani ko yana d'akinsa zai yi wanka mik'ewa tayi da nufin zuwa kawai ta zo bude kofa taji maganganun su da Innah Amjad yayi wa Innar sa alk'awarin auran Hafsa auran ta dashi tun baije ko ina ba zai yi mata kishiya ita kuma tata 'kaddarar kenan haka Mimi Tasha wahala akan shi itama gashi ko sati bata cika a gidan sa ba abubuwa sun cakud'e ta mata Innalillahi wa'ina ilahi raji'un.

"!

Cikin wannan hali ya shigo ya same ta fitalar dakin ya kunna yaganta zaune daram kan bed!

Asma'u duk kokarin ta na hana hawayen ta zubawa ta kasa zuba kawai suke yi sharrrrrr!

Zuciyar ta sa wani irin Tara tsatsin kishi take yi."!
[12/13, 9:32 AM] BintuUm@rAbb@le: Cikin yanayin tafiyar shi ya 'karaso kusa da ita sam bai fahimci kuka take ba sai da ya kusan ci jikinta sosai yaji shashshekar kukan ta....

Jikinshi na kyarma ya zube wayoyinshi gefen bed din ya rugumota jikinsa yana sauke ajiyar zuciya tare da tambayar ta kukan me take, shifa ya tsani ganin zubar haweyen ta.

'Kokarin kwace jikinta take shi kuma ya rike tam!

Yana rarrashin ta Sam baiyi tsammanin taji maganar su da Innah ba tambayar ta yake yi me ya same ta take kuka....

Cikin zafin zuciya ta gartsa masa cizo!

A hannu sosai yaji zafi a hannunsa ya ki sakinta duk ya rikice!

Da kyar ta samu ta bude bakinta tace"Ka k'yaleni ni, tunda na lura kai kan ka kawai ka san......

Katse ta Yayi ta sauri yana rawar jiki yace." Me nayi miki ne nifa bana son wannan kukan kiyi shuru ki min bayani ki daina magana kina kuka kinji."!

Yana maganar yana goga mata fuskar shi a tata wannan d'abi'ar shi ce da alama shu k'okari ma yake ya had'e bakin sa da nata.

Tace." Duk maganganun da kuka yi da Innah naji su Kai ko kunya baka ji ba har da amincewa zaka auri hafsa wallahi bari in fad'a maka abunda baka sani ba zaka mai da gidan ka sansanin ya'ki domin tuntuni bama zama inuwa d'aya da wannan kucakar yarinyar me warin hammata!

Ni kam na fad'a maka sai dai ka za'bi guda cikin mu ni ko ko ita domin wallahi bazan had'a miji da ita ba."!

Yanda take fad'an maganar zaka San da 'k'uruciya a tare da ita bayan nan Kuma tsananin kishi ya rufe mata ido Sam bata tunanin maganar da zata fad'a.

Maganar ta ta bashi dariya sosai amma sai ya dake baiyi ba sai ya sauya al'amarin ma ta wata sigar.......

Haushi ya turni'ke ta tana yi masa magana yana wani Abu daban, ture shi take daga jikinta shi kuma yana 'kara sakar mata nauyin sa har sai da yayi nasarar danne ta gaba d'aya ya tsira mata rukittatun idonsa masu kashe mata jiki.

Kauda fuskarta take yi ganin yana shirin yi mata abunda ya saba lallai ya raina mata hankali, sai ta fara ya kushe masa jiki tana turje-turje da 'kafafun ta duk ta turje bedshirt din......

Yaso ya sanya mata 'karfi kawai sai ya k'yaleta hade da sauka daga kanta...

Toilet ya nufa domin yin wanka yana mamakin t
sananin kishin ta a kansa.

Jikinsa daure da towel ya futo ya tsaya gaban dressing mirror ya feshe jikinsa da turare kana ya sanya Riga mai gajeran hannu.....

Asma'u har yanzu tana zaune ta hade kai da gwiwa tana kuka, bai CE mata komai ba ta futa daga d'akin...

Mintuna biyar yayi ya dawo hannunsa rike da 'karamin Cup Wanda yq had'o coffee a ciki ya zauna kusa da ita yana kurba yana latsa wayarsa.

Haushin sa kamar ya kashe ta wato ba zai rarrashe ta ba ma balle yayi mata musu akan maganar da ta kawo masa wayar shi ma yake dubawa ta tabbata kenan abunda kunnen ta yaji ye mata gaskiya ne.
Chapter 18 · 0% Book details