← Book details Babban Yaro Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 23

Sashe 15

Babban Yaro Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amjad yayi sallama cikin dakakkiyar muryar shi ya gaida jama'ar jahar kano sosai kana d'an jaridar ya d'ora da fad'in" Yallab'ai jama'ar jahar kano suna 'bukatar ka zama shugaban su kamar yanda maigirma shugaban kasa ya basu damar za'bar governor su saboda abunda ya faru, d'umbin masoyan ka suna so suji ta bakin ka suna so suni ra'ayin ka kan hakan."
Amjad yayi gyaran murya a nutse yace." Alhmdullahi Allah ne abun godiya hak'ika babu abunda zance da masoya da jama'ar jahar kano babu shakka sun nuna mun 'kauna ta hak'ika ta inda nake ganin bazan ta'ba bujerewa bukatar su ba, babu shakka na karba kuma zan tsaya ra'ayin daka kan jahar kano domin in kawo cigaba mutukar na zama shugaba a cikinta duk wani 'k'aramin ma'aikici zai samu promotion zan dauki sabbin ma'aikata da suka dace masu bukatar tallafi da kowa ne b'angare gwamnati na zata tallafa musu , zamu yiwa matasa aure zamu basu sana'ar yi kana zamu ya'ki da 'yan daba gami da 'yan Sara suka zamu sanya ido sosai a jahar kano zamu sanya jami'an tsaro ta ko wane fanni zamu kula da marasa lafiya gami da nakassasu zamu yi yak'i da cin hanci da rashawa mutukar Allah ya bamu mulki zamu tsaya mu kula da hakkin Al'umma da izinin Ubangiji.

"
Cikin nutsuwa ya 'k'arashe maganar sa.

Jama'ar hajar kano suna ma'kale da redio mussaman matasa sai ihu suke yi jin cewar za'ayi musu aure ayi musu lefe kuma a basu abunyi babu shakka baza su taba mancewa da guy nan ba, ma'aikata kuwa babu Wanda ya kaisu murna jin abunda amjad din yace, wadanda suka aje takkadun su tuni suka fara murna zasu samu aiki da basu samu ba Kai yara da manya dattaija har da mata na cikin gida murna suke yi jin cewar Amjad din yace." Suma zai basu tallafi na sana'oi iri-iri.....

Tambayar 'karshe da ta bawa kowa mamaki har shi Amjadu din inda d'an jarida yake tambayar sa da cewar"Yallab'ai munji wani labari daga majiya me tushe shine muke so muji daga bakin ka shin hakane ko ba haka bane ko kuma sharrin magauta ne wai da gaske ne Matar da kake aure a yanzu cikin gidan haya ta 'kare rayuwar ta har ka aure sannan a halin da ake ciki yanzu Wanda suke hayar a cikin gidan ya basu notis domin su tashi su bar gidan hak'ika wannan labari da muka samu ya bamu d'umbun mamaki ta inda muka k'aryar ta hakan saboda sanin da makayu maka cewar kai mutum ne mai taimako da tallafawa Wanda yake dashi hakikanin gaskiya baza ka bar iyayen matar ka cikin gidan yaya ba, yallab'ai muna so muji komai daga bakin ka, sannan muna Neman afuwa a gurina saboda mun San dole ranka ya 'baci dalilin wannan tambayar."
Amjad yayi shiru na tsawon mintina biyar kana ya sauke ajiyar zuciya yace." Wannan maganar da kayi ba gaskiya bace, babu shakka akwai abunda yake rufe Wanda ni dakai da su da kuma ita wife dina bamu sani ba, So nasan dai gidan da suke ciki cikin unguwar Gigiginyu na company ne Wanda ya mallakawa mahaifin ta tun yana raye had'e da shaidu da sa hannu yau shekara goma sha hudu kenan da rasuwar sa wannan shine abunda na sani, amma dole zan bukince kan maganar taka."
'Dan jaridar yace." To babu komai Yallab'ai mungode mutuka da samun damar hallatar mu da kayi muna maka fatan alkairi a rayuwan ka Allah yayi maka jagora ya taya ka rik'o." Amjad yace." Amin suma amin."
Nan D'an jaridar yayi sallama kana ya rufe kayan aikinsa........

Amjadu tun a mota zuciyarsa take masa wani irin c
iwo ranshi ya gama 'abaci da abunda Asma'u tayi masa domin shi yana ganin duk laifin ta ne har akazo wannan jalli tabbas ya Dade da sanin mecece siyasa a rayuwa babu sauki a al'amarin duk inda zaka wa mutum baza ka futa ba dole sai ya San yanda yayi ya bata maka rai!

Yana mamakin Gidan haya Asma'u suke zaune amma bata ta'ba fada masa ba dole ya nuna mata 'bacin ransa..
*12/12/2019*
[12/11, 10:37 PM] .: *BABBAN YARO*
*84*
Sai wajan 'karfe goma ya isa gida, Parlor babu kowa duk sun gaji sun tashi mussaman Hafsa da akaci Uwar kwalliya kamar matar gida ana jiran sa ya dawo ya gani k'arshe sai ta 'buge da gyangyadi, gefe guda kuma 'konar ta na yi mata zugi da rad'ad'i!

Babu arziki taje ta kwanta, Inna ta bita a baya tana mita......granny kuwa Dariya take musu tare da fad'in kwaji dashi haka kurrum saboda daukar dala ba gammo Ku gayyato jiki Ku dawo gidan mutane nima barin gidan zanyi sai ku 'k'arata Ku kad'ai."
Asma'u kuwa komai cikin d'aki Tayi shi saboda yanayin da take tafiya babu sauki shiyasa ta kulle kanta Har baby ta gaji da kukan ta ta ha'kura....

Yini tayi babu abunda yake cikinta sai yughot da granny ta tilas ta mata dole tasha kwata-kwata bata jin test a bakin ta....

Sallah ma da k'yar!

Tayi ta jikinta ciwo kawai yake yi cikin wannan halin ya shigo ya same ta.

Tana kwance kan dadduma da ta idar da sallahr Isha'i ya shigo ya same ta, sama-sama taji muryar shi ta bud'e idonta da suke cike da bacci....

Mik'ewa tayi zaune tana mutsike ido zatayi magana ya Riga ta ta hanyar fad'in.

"Tashi zamu yi magana." Yanayin yanda ya fad'i maganar ne yasa ta bud'e idonta sosai tana kallon fuskarsa taga ya wani murtuke fuska, gabanta ya fad'i sunkuyar da kanta tayi 'kasa.

A hasale yace." A rayuwata na tsani rufa-rufa Asma'u a yanda na d'auke ki a zuciyata Sam bai kamata ki rufe min sirrin cikin gidan Ku ba yau da tun farko kin Sanar dani cewar gidan da kuke ciki ba naku bane ni mai mallaka mu gidane tun kafin azo ga jallin tonan asiri!

Ina fatan kin saurari hirar da akayi dani a tashar freedom redio."
Cikin rashin fahimta nace"Abban baby ban fahimci maganar ka nifa tunda ka futa ina kwance ina bacci in banda yanzu da na tashi nayi sallahr Isha'i wallahi ban saurari komai ba, kuma naji kana wata magana kamar ta cikin gidanmu ka Sanar dani kome ye."!?

Baba walwala a fuskar shi yace." E maganar cikin gidanku ce ko bata shafe ni bane."!?

Ya fad'i maganar cikin gatse!

Kallonsa nayi naga ya tsura min ido cike kamar wacce tayi masa sata!!!

Gyada kaina kurrum nayi takaicin halayen sa ya soma damuna Sam shi baya daukar Abu da sauki!

Sai yayi dakawa mutane tsawa!

Mik'ewa nayi ba tare da nace masa komai ba.

Na cire hijab jikina toilet na nufa cikin yanayin tafiya kamar me koyo.....

Muryar shi a sama!

Yace." Ko bakya ji ne wato ina miki magana kina tafiya kamar wani sa'an ki, ki bar ganin jiya na kwanta dake Wallahi kika raina ni sai na baki mamaki."!

Cikin fada yake maganar
Hawayen dake kokarin zubo min nake mayar wa a zuciya nace wai dame zanji ne Da bala'in sa ko da haibaicin da Innah sa ta yini tana yi min ko kuma da ciwon jikina zanji....

"Abban baby Allah ya baka hakuri maganar da kake wallahi ban San da ita ba." Toilet din na shige ban San saurari abunda zai ce min ba...

Ruwan zafi na hada na kara shiga tsawon minti goma sha biyar na futo daga ciki, wanka nayi tsaf na futo daure da towel na rofu jikina da wani jin wani irin sanyi na shiga ta Nasan zazzab'i ne har yanzu bai tafi ba.

Yana zaune inda yake na jikina babu kwari na lalubo kayan bacci cikin Kayana gaban dressing mirror na tsaya na shafa mai sama-sama humrar gurin aunt Hauwa na shafe jikina da ita sannan na zura kayan baccin masu Riga da wando rigar mai siririn hannu ce shi kuma wando iya gwiwa yaje gashin kaina na tubke sai na d'aura d'ankwalin abaya a kaina...

Kai tsaye bed din na nufa....

Amjad da tunda ta futo daga toilet yake binta da wani irin kallo sai da yaga ta juyo ne yasa ya dauke kansa da sauri hade da kara hade fuskar sa, sai da ya bari ta kusa karasowa ya sanya k'afarsa ya tade tata ta fado kansa
'Dankwanlin a bayar ya cire ya jefar kasa ya rike tarin gashin ta da tayi parking dinshi tsakiyar ka, jansa yayi da k'arfi yace." Ina a matsayin mjinki kina kin daukar magana ta da muhimamci Asma'u magana ta dake ta farko ta k'arshe shine ki kira Yayan ki Aminu cewar insha Allah gobe yazo ina Neman sa maganar zaman gidan haya ta 'kare in dai ina Raye a duniya."
Cikin kuka nace"A rayuwata na tsani mutum mai saurin daukar zafi da rashin fahimta nifa Wannan maganganun naka Sam ban fahimce su ba kamata yayi daga shigo sai ka warware min kome cikin ruwan sanyi amma kazo kana tayi min masifa ko tunanin halin da nake ciki baka yi."
Sassauta rik'on gashin yayi yace." Kece kika jawa kanki da ki'ki tsayawa ki saurari maganata." Nace'ta yaya zan saurare ka kazo kana yimin hayaniya.!" Duk ina hawaye nake maganar tsira min idonsa yayi yana kallona yace." Kiyi kokarin hana hawayen ki zubowa bana son ganin su." Jikina na fuzge da k'arfi nace"Ni ka k'yaleni ko waye yace maka haya muke yi a gidanmu karya yake yi."
Yace." Nine makaryaci kenan." Banza nayi masa na shiga cikin bargon ina share hawaye....

Mik'ewa yayi ya futa daga d'akin, ni kuma na shiga tunanin maganganun shi.

Amjad na futa parlor ya tadda Hafsa a zaune ta k'urawa kofar dakin Asma'u ido, cikin mamaki yace." Ke Lafiya me kike yi bakiyi bacci ba."?

Furgitt Hafsa ta dawo hayyacin ta.

Sai ta hau ya 'ke da kame-kame yace." Tashi kije ki kwanta dallah." Cikin tsare gira yayi maganar!

Hafsa ta mike simi-simi ta shige daki gwiwar ta duk ta sage, Amjad yana yi mata mugun kwarjini a rayuwar ta ta inda ko muryar shi taji sai taji gabanta ya fad'i kusa da mahaifiyar ta ta kwanta cikin sarewa d
al'amarin shi ta fashe da kuka me cin zuciya.
Chapter 15 · 0% Book details