← Book details Babban Yaro Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 23

Sashe 21

Babban Yaro Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Iyami tasa dariya tana fad'in"Dole ne in goyi bayan ubangidana shugaba mai adalci ubangiji Allah ya taya shi ri'ko yayi rik'o da hannayen sa Allah ya bashi ikon d'aukar nauyin jama'a."
Granny taji dadin addu'ar Iyami shiyasa take sonta Iyami macace mai karamci da mutumci sun fi shekara goma a tare duk masu aikin da tayi tafi sha'kuwa da Granny kuma tafi sonta saboda tana kyautata mata, itama kuma tana kyauta ta mata gwargwadon iko idan Iyami zata je 'K'auyan su Shatara ta arzi'ki granny take had'a mata Iyami tayi buhu-buhu da kayan masarufi ta kaiwa 'yan uwanta na can da suke ganinta da daraja saboda tana mutukar taimaka musu.

Iyami kicin ta nufa domin had'a sanwar dare ita kuma granny tayi zaune a parlor tana jiran futowar masu gidan, Baby ce ta rarrafo tazo ta kama granny ta mike tsaye tana mata gwaranci Granny ta dauke ta tana fadin "Nasan Iyayen ki kike nema Yo idan suka ji kukan ki ai sa futo Dan dol...

Kafin ta rufe bakinta baby ta tsandare da ihu!

Tana nuna d'adin Asma'u da hannunta.

Rarrashin ta granny take yi fafur yarinyar ta'ki yin shiru sai ya zamana ma kamar 'kara ingiza ta take yi.

Iyami ta futo daga kicin da sauri tana fad'in" Baby rigima ai tunda ta fara wannan kukan nata komai zai tsaya." Granny tace"Tayi min dai-dai Wallahi ke dai je ki cigaba da aikin ki."
Iyami tace"Granny bari dai in tsaya in dama mata madarar ta kin san Abban ta baya son kukan ta abu komai a sannu dama Kuma yau ba abunci mai wahala zanyi ba."
Granny ta mi'ke tsaye da baby a hannun ta kai tsaye bedroom d'in Asma'u tq nufa tana fad'in"Iyami baza kiyi mana girkin dare ba mutukar kika tsaya rarrashin Wannan 'yar rigimar sai magariba tayi bakiyi komai ba, dole su futo haka." Iyami tabi Granny da kallo cike da mamaki.!

Granny kuwa dukan 'kofar d'akin take yi da hannunta tana fad'in"Kai d'an anace ka futo haka Haba!

Wannan jaraba dame tayi kama!

Ni kam na tsani wannan d'abiar taka, ku futo Ku d'auki 'yar ku ta cika wa mutane kunne da kuka." !

Baby ta 'kara tsandara Ihu!

Tana zillo dole sai ta sakko.

Asma'u da Tayi mutukar galabaita ta kalli Amjad din da yake ta kyarma jiki yana 'kokarin sanja mata kaya bayan yayi mata wanka da ruwan d'umi tace"Abban baby don Allah ka bud'e 'kofar nan haka wai baka jin kukan da baby take yi ne tun d'azu."
Shiru yayi mata kawai ya cigaba da sanya mata riga kamar yanda ya niyyata sai da ya shirya ta tsaf!

Sannan ya nufi kofar futa, yana jin haushin abunda granny take masa a gidan duk ta saka masa ido, shi da gidan sa da komai bai isa ya shiga daki da matar sa zata hau 'korafi fa surutai!

Cikin zuciyarsa yace ." Da ya sani ma lokacin da tace zata tafi ya barta tayi tafiyar ta ya huta da saka ido."
Yana bud'e kofar ya sha kunnu domin kar taga fuska ta kawo masa wata maganar....

Harara ta maka masa tace"Oho! dai ka futo kana muzurai da 'bata fuska bayan kagama turmshe 'yar mutane kagama iface-ifacen ka na rashin imani!

Irin naka baka gani yarinyar nan ciki ne da ita sai ka dinga hawanta kamar wani doki Haba!

Ina dalilin wannan abu." Ta 'karashe maganar tana mi'ka masa baby da take mik'a masa hannu.

Hannu yasa ya 'karbi baby yana fad'in"Wai ke don Allah granny ina ruwan ki ne?

Kin fiye sa'i do duk kin bi kin dame mu tun safe sai mita kike yi kin hanamu bacci sai kace an fad'a miki abunda kike tunani muka yi to ki shiga ki duba ki gani mana." Ya fada babu wasa
Granny taje "Oho!

Kai ka sani ni babu wani shiga da zanyi in duba domin ni ba yarinya bace, wai mutumin da zai dauki ragamar mutane sama da dubu d'ari shine yake ma'kale mace a jiki babu dare babu rana, itama Asma'u duk da laifin ta da take biye maka sai kaje ka baro ta tana fama da 'karamin ciki."
Dariya maganar ta ta bashi amma baiyi ba sai ma 'kara had'e fuska da yayi yace." Shikkenan kuma saboda zan ja ragamar jama'a sai in fasa more rayuwata kawai don in cutar da kaina bazai yiwu in takurawa kaina ba." Granny tace" Oh-oh!

Kaje kayi tayi 'kato Allah ya bada sa'a kadai kiyaye da 'karamin cikin ta." Tana 'kokarin barin gurun take maganar......

Yace." Kinji ki kuma da wani magana granny ciki dai nawa ne kuma nasan takan komai.

" Fad'ar haka da yayi sai ta fashe da kuka tana fad'in" Yanzu 'Kato ni kake wa wannan maganar?

Ni zaka yi wa gori akan d'an cikin ka." Amjad ya saki dariyar da yake 'b'oye wa yaja hannun granny d'in da take ta faman kuka tana fyace majina sai surutai take yi wai yayi mata gori.

Yace." Nifa ba haka nake nufi ba Kuma ba abunda kike nufi nake yi ba to idan ma hakane ai ba haramun bane tunda ke da kanki kike cawa dani kar in bi matan banza kin ga idan sha'awa ta kamani dole in zo ga iyalina kiyi hakuri kinji Uwar gidana." Granny ta share hawayen ta tana fad'in"Yanzu ina Asma'u take."?

Yace." Tana ciki bata jin dad'i amai ma ta gama yi yanzu." Tace"Ai kaji abunda nake fad'a maka ka 'karya tani Hummm!

Mik'ewa tayi ta nufi dakin Asma'u tana surutai kamar yanda ta saba.

Shi kuwa Amjadu kallo ya bita dashi har ta bud'e dakin ta shiga sai a lokacin ya saki dariyar da yake 'boyewa yana mamakin 'karfin halin tsohuwar.
******
Alhmdullahi dukanin abunda aka ce Allah a rayuwa to an gama komai kuma zakaran da Allah ya nufa da chara ko na muzuru ana shawo sai yayi, hausawa suka ce hassada ga me rabo taki ce, Amjadu ya sha gwagwar maya a rayuwar shi kafin Allah ya tabbatar da mulkin jahar kano a hannun shi, hak'ika yaga dumbin masoya kuma yaga dumbin ma'kiya dasuke ta caccakarsa gami da zaginsa a gidajan redio dukanin su maganar guda ce cewar shi d'in ba d'an gari bane babu yadda za'ayi yazo ya mulki 'kasa saboda gudun kada ya gama cin albarka cin "kasa ya gudu k'asarshi ta gado *Chadi* to dukanin wannan surutun da suke yi babu mai sauraran su domin jama'ar jahar kano sun gama yin nisa da 'kaunar Amjadu ta inda suke ganin zasu iya za'ben sa ya zama shugaban 'kasa mutukar yana nuna yana da ra'ayin haka su zasu Goya masa baya.
[12/14, 9:50 AM] .: Rayuwa kenan Asma'u a gidan gomnati lallai arzikin mutum a jikinsa yake Umma ko da wasa bata ta'ba tunanin zata haifi 'yar da zata auri kansila ba ma amma dake Allah Allah ne 'yarta Asma'u wacce take da 'karacin kyau a cikin 'yayanta itace take auran governor dole ta godewa Allah da wannan karamcin da yayi mata, Amjadu ya d'ora Aminu kan harkokinsa da yake yi a da kuma a halin yanzu ana shirye-shiryen farfad'o da company da ya ruguje shekaru biyu da suka wuce.

Umma kullum cikin sanya wa Amjadu albarka take yi saboda ya tsaya mata sosai su aunt Hauwa an samu abunda ake so kasuwanci ya k'ara bunkasa kudi ko ta ina suna shigo mata tunda yanzu Alhmdullahi jari ya fara k'arfi kuma Ya Aminu ya kama 'kasa duk ta dalilin Amjadu, Umma sai yanzu ta yarda da maganar hausawa da suke cewa sai kana dashi ake yi dakai ada idan ta shiga cikin dangin mijinta kallon arziki basa yi mata saboda bata da kudi bata da sutturar kirki yanzu kuwa har rububin gayyatar ta sabga suke yi shi kanshi Kawu Yunusa kamar yayi mata sujjada Saboda tsabar ladabi da yake mata kawai kallonsa take yi, saboda tsabar tsaurin ido irin nasa kuwa cewa yayi yana so ta auri Idiris Wanda ya kasance 'kani ga Baban su Asma'u Umma tayi mamakin jin Wannan maganar daga bakinsa kawai sai barshi da halinsa tasan da cewar duk kwadayi ne ya jawo haka, duk da cewar suma Amjadu din yana tsaye a Kansu yana bukata musu sosai amma sun dauki ido sun 'Dora mata.

'Bangaran granny kuwa bayan za'be da wata biyu tuburewa Amjadu din tayi kan dole sai taje taga 'yan uwa suma da hankalin su na kanta tunda suka ji Amjadu din ya zama governor a jahar kano suke murna da yi masa fatan alkairi....

Amjad da yaga rigimar granny ta'ki karewa sai yace ta shirya insha Allah zasu je ranar Monday gabad'ayan su har Asma'u da cikinta yayi nauyi ga wata Uwar 'kiba tayi ciki wata biyar amma da kyar take cire 'kafa duk yabi nonowan ta da kwankwason ta shiyasa ta bude sosai bayan haka kuma da samun Hutu da cima mai kyau ga Ac ko ta ina ga kulawar ogo domin cikin NATA baya hanasu su more rayuwar su 'ka'ida ne sai sunyi sex dare da asuba abun ya zame musu jiki.

Duk da tarin ayyukan da suke gaban shi haka ya tsalle ke ya bar komai a hannun mataimakin shi Injiniya Jabir Hamid yasan mutumin jajurtacce ne akan komai yayi masa fatan dawowa lafiya ya tattara iyalinsa suka nufi 'k'asar shi domin gaishe da 'yan uwa.

Satin sa d'aya yayi nufin komawa najeria saboda aikin da ya bari granny ta 'kekasa 'kasa tace ita ba yanzu zata koma ba tilas ya k'yaleta yace.
Chapter 21 · 0% Book details