← Book details Babban Yaro Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 60

Sashe 7

Babban Yaro Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bakin kofar na zauna ina kuka Mimi tazo ta tsaya a kaina tare da fadin "Bani waya ta,aikin kawai kin karar min da chaji a banza da hotunan ki, kin San ba wuta ake kawo wa ba"Wani irin kallo nayi mata ina gyad'a kai cike da takaici nace" Ki duba wayar ki cikin jakata gata can a tsakar gida. " tsallake ni tayi ta futa, daga dakin.
Chaji taje ta kai domin bai zama lallai su kawo mana wuta ba,
Ranar ko abuncin dare hanci ba, haka na kwana da cikina tsabar bakin ciki ya hanani bacci sai juyi nake.

*****
Kamar yanda ta kwana tana juyi to shima haka ya kwana yana murk'ususu zuciyarsa Sam! Babu dad'i ga uban zazzab'i da ya kwana dashi, ko da asubah ma a daddafe yayi sallah Yana jira gari ya waye musu a can , time din ko wace k'asa daban yake
K'arfe Biyar na asubah mun tashi Ya Aminu ne ya tsaya a kanmu har sai da yaga ko wacce ta mike tsaye sannan ya nufi massalaci, motsin Umma Naji a tsakar gida tana alwala da sauri na koma na zauna, domin bana son na futa mu had'u. Mimi ta futa ta barni,, ko minti biyu ba ayi ba kira ya shigo wayar Mimi, daga inda nake in hangowa *Heart beat* sunan da nagi kenan, cikin zafin zuciya na dauki wayar na kashe! A fili nace"Aikin banza da wofi asubar fari za'a damu mutane. " wani kiran ne ya kara shigowa na kashe da sauri,, A'a wani kiran ya kara shigowa na kashe, sai da ya kira sau bakwai ina kashewa, yana kiran na takwas din ne kawai na kashe wayar gaba d'aya.
Nashi b'angaran sakato yayi da wayar a hannu lokacin da ya kira suka fad'a masa cewar an kashe wayar ma gaba d'aya, tunani ya shiga yi anya Mimi zata kashe masa waya kuwa? Why!!! Me yake faruwa ne.? Jefar da wayar yayi kan bed ya yunk'ura ya tashi zaune kwalin sigari ya dauko ya bata wuta ya fara fesawa cikinsa hayak'i da sanyi safiyar na, da sauri kuma ya dauko wayar tare da nemo numbar rambow bugu guda tayi ya dauka baki na rawa yace."good morning sir." Bai amsa ba yace." Meye labari ina fatan ka yi aikin da na sanya ka."? Rambow yace." Yes sir Ashe ma ba d'an gari bane yazo bak'unta ne dan barno ne wato mai duguri." Da babbar murya yace."kaje Sanar dashi cewar inji ya bar garin nan kafin in k'araso idan ba haka ba sai da uwarsa ta haifi wani Wallahi. "!!!! Rambo ya tsorata jin furucin oban gidan nasa, ta yaya zai iya zuwa ya fad'awa mutumi haka, amma duk Dan a zauna lafiya yace." Insha Allahu zani yanzu." Kashe wayar yayi yana huci!!!

Mimi ta shigo a tsanake ta shimfid'a dadduma ta tayar da sallah, futa nayi daga dakin nima domin dauro alwala. Bayan ta idar Da sallahr ne sai ta dauki wayar kawai ta ganta a kashe alhalin a kunne ta bar ta. Kunnawa tayi tana zargin Asma'u cewar ita ce zata kashe mata waya.
Aikuwa ko minti biyar ba ayi ba, kira ya shigo wayar tana dubawa taga *Heartbeat* wani murmushi ta saki had'e da kwanciya kan katifar tana lumshe ido ta d'aga wayar. Tare Da fad'in"Assalamu alaikum."
Sama-sama ya amsa murya a kaurare! Yace." Had'a ni da wannan yarinyar." Dai-dai lokacin dana shigo dakin kenan ina jin komai tunda a hands free wayar take.. Cikin tsawa yace." Ko ba kyaji ne."!! Mimi ta tsorata mutuka, muryar ta na rawa tace"Wace yarinyar."? Kai tsaye yace." Asma'u. " jin ya anbaci sunana yasa na zabga tsaki da k'arfi don yaji, aikuwa yaji lokacin da tayi tsaki! Sai ya mike da sauri jikinsa na wata irin tsuma! Kamar Wanda ya sha tsumin 'yan bori ya kwatsawa Mimi tsawa tare Da fad'in "Bata wayar naji ta a kusa dake."!!
Ganin yanda yake kurma wata irin tsawa ne yasa na fasa tada sallahr raina a mutukar b'ace na karb'i wayar da take Mik'o min murya sama-sama nace" ta bani wayar meye."!! Tsaye ya mik'e da sauri cikin hargagi yace." Budurwar 'yan daudu yarinya mai aji da kamun kai!! Budurwa me lasisi a jahar kano, duk naga abunda kikayi jiya, ki sani kamar a gabana komai ya faru! Wallahi-wallahi ki kiyayi haduwar mu dake sai kinyi mugun raina kanki!! Ni zaki zubar wa da mutumci...... Katse shi nayi kafin ya k'arasa maganar tashi nima cikin hayaniya nace" Kai!!!! Malam wai me ka dauki kanka ne? Meye ya shafe ka dani? Meye alakar ka dani da kake wannan ihun! To bari kaji naji dad'i da ka gani ka sani jikina ba irin na ko wane lusarin namiji bane irin ka mai aikata sab'on Allah yanzu nayi maka nisa! Kuma tab'a min jiki da kayi kwanakin baya na barka da Allah ehe!!! Ita ma Mimi addu'a nake mata Allah ya tsare ta daga sharrin k........."ShautUp Your dirty mouth."! A zafafe! Tsorata nayi amma saboda taurin kai yasa nace" Ank'iyin shiru d'in duk abunda na fad'a gaskiya ne ai Mtssss." Na buga wani irin tsaki had'e da jefawa Mimi wayar a cinyar ta. Ji nayi yana fad'i" Ok zamu had'u ne zaki San Wanda kike wannan rashin kunya wallahi sai kin maimata min duk abunda kika fad'a kuma, kiyi gaggawar korar wannan mummunar saurayin naki bak'i me kamar alade irin ki, idan ya sake Nazo sai na b'adda shi a duniyar nan."!!
Mimi tayi sakato da waya a hannu bayan ya kashe nu kuwa tada sallah ta nayi raina a mugun b'ace!
Wani irin tunani take a zuciyar ta, wannan tashin hankali da guy nan yake yi na lafiya ne kuwa? Anya ba son Asma'u yake ba? Take tambayar kanta, in kuwa hakane babu shakka rayuwar ta tana cikin garari domin baza ta iya had'a miji da Asama ba, gashi duk duniyar nan babu namijin da take so kamar sa, tana ganin sai da ta mutu babu aure.

Wayar ra dauka tana neman numbar sa, bugu guda ya dauki wayar, cikin siriryar muryar ta tace"My kayi hak'uri don girman Allah nasan ranka yanzu a b'ace yake, babu shakka Asma'u bata kyauta ba."
Ajiyar zuciya ya sauke a kashi d'ari na damuwar sa kashi casa'in ya ragu , yaji dadin maganar Mimi yace." Momyna 'yar uwarki bata da kirki wallahi kanta rawa yake yi, ki rink'a yi mata fad'a kinji ko."

Mimi tace"Kullum kuwa cikin fad'a muke yi da ita Sam! Asma'u bata son San gaskiya, wallahi." Ina ji ina sallahr lallai Mimi har sunyi sabon da zata dinga kai suka ta a gurin shi.sauri nake in idar muyi wacce zamu yi da ita.

Ina jinsa yace." Kar ki biye mata da duk abunda zata yi miki na rashin mutum ci domin na lura tashan balaga take, idan tayi ba dai-dai ba ki yi mata fad'a koda zakuyi doke-doke da ita kuwa."
Mimi tace." Insha Allahu kar ka damu." Yace." Zan dawo gobe ko jibi kiyi min kwalliya me kyau sannan ki turo min pictures dinki ta whatsp zan gani." Cike da kunya tace" shikkenan ka bude data zan turo maka." Sallama sukayi Mimi tana saki murmushi daga ni tana cike da farin ciki.

Ina idar da sallah ko addu'a banyi ba nayi kan Mimi da masifa nace "Mimi kin Dade baki kai suka ta gurin sa, ba ki fad'i abunda ya fi haka a gurin shi ba damuwa ta bace, kece yake gaban ki da har idonki ya rufe a kansa kika kasa fari da bak'i aikin banza aikin hofi ina kara dai tunasar dake cewar kiyi hattara ki kula idan ba haka ba ke zai kai ya Baro....Wannan karon Mimi bata k'yale ni ba, itama a fusace ! Tayo kaina tare da fad'in" duk abunda zaki fada ki fada ke ya shafa kowa rai yayi wa dad'i ba kamar me shi ba ne Asma'u kije kiyi abunda kike so kuma wallahi kar ki sake ki kara zagina domin uba bai fi uba ba. " Kanta nayi zuciya ta namin zafi nace" Sai nayi RAYUWAR ki ce ko tawa dake dashi da Yaya Aminu kusa tsinken tsire ku tsikare n......Ban k'arasa ba naji saukar Mari! Da sauri na dafe fuskata ina kallon Wanda yayi min haka, Umma ce tsaye tsakiyar dakin ranta a mugun bace tace" Tsokane mata ido zakiyi ne Mara kunya."? Shuru nayi hade da sunkuyar da kaina kasa ta cigaba da cewa." Duk rashin mutumcin da kikayi ina jinki, ina ce Mimi ta girme ki da har kike tsaye kanta kina nuna ta da d'an yatsa kan ta fada miki gaskiya." Mimi tace"Umma kiyi hakuri don Allah." Tace" ke zan bawa hakuri Mimi da kike k'okarin nusar min da ita, duk da rashin mutumcin da take miki." Mimi tace"Umma wannan duk abunda ya shafe mu ne, dama mun saba fad'a haka." Cike da tausayi take kallon Mimin ta rasa wace irin zuciyace da ita, tace." Ba irin wannan fad'an kuka saba ba. Ke kam zuciyar ki tana da sanyi ina addu'ar kar Allah ya kai gidan me mata ki sha wuya domin kishiyoyin ki zasu raina ki wallahi." Shiru Mimi tayi. Ita kuma Umma ta kama hanyar futa,
D'an juyo wa tayi tana kallon katifar mu, waya ta gani tamfatsetsiya cike da mamaki tace"Wannan wayar waye a cikin Ku."? Shiru mukayi dukanin mu.Cike da zargi da tuhuma tace." Ba tambayar Ku nake ba."?
Baki na rawa Mimi tace"Tawa ce Ummah." Cikin mamaki tace "Mimi yaushe kikayi magana babu labari." Yanda Umma ta fad'i maganar kai tsaye ya tabbatar mana da cewar Hankalin ta ya tashi. Da sauri tace"Mik'omin wayar nan." Hannu na rawa Mimi ta mik'a mata, ta karb'a had'e da fucewa daga d'akin.
Shuru muka yi dukanin mu, yanzu na daina jin taikacin komai nayi kwanciya kawai a zuciya ta nace"Ke ma abunda ake min a gidanan yazo kanki sai kiji in da dad'i baya na juya mata ina lumshe idona babu abunda ya dame ni, injita ta kwanta itama jikinta duk yayi sanyi.

K'arfe takwas dai-dai naji hayaniyar Ya Aminu a kaina rumtse idona nayi da k'arfi ina fadin"Ya Aminu Dan bala'i ne wallahi.
Chapter 7 · 0% Book details