← Book details Babban Yaro Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 60

Sashe 48

Babban Yaro Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Likitoci kusan biyar ne suka rufu a kan Mimi domin ceto rayuwar ta suma sun tsorata da al'amarin kuma yayi musu bazata lallai ubangji Shahidi ne kuma shine yasan gaibu kana taka Allah na tashi, duk iya bunkicen su a kan Mimi bai nuna musu wata alamar na cewa zata yi jijjiga ba, amma dake Allah Allah ne ya saukar da hukuncin sa kan baiwar shi, a war su biyu a kanta suna kokarin shawo kan Matsalar da tsayar da jinin da yake zuba Abu ya fassakara, Wanda a wannan lokacin Mimi ta amsa kiran Ubangji dukanin su sun tsorata mutuka duk da suke likitoci suna ganin irin wannan tashin hankali amma al'amarin Mimi ya girgiza su, Dr Faruk ya lura cikin na na motsi take suka shirya yi mata CS domin a Ciro abunda yake Cikin tunda da ran shi.
Jahid daure wa yake akeyin aikin dashi, zuciyar sa nacan tunanin ya za'ayi ya Sanar da Amjadu wannan mummunan labarin. Cikin hukuncin Allah suka samu nasarar ciro baby girl 'yar wattani bakwai ba sati d'aya, yarinyar 'yar mitsitsya da ita, tana cikin koshin lafiya take suka sanya ta Cikin kwalabar su, da aka tana da domin irin su, suka kimtsa gawar Mimi , cike da alhini da tausayi suka futo
Da Amjad suka yi karo tsaye a kofar dakin dasu ke, Jahid yaji gaban shi na fad'uwa, hannunsa yaja suka shiga ofis din sa.
Amajad yace." Jikina na bani bazan ji alkairi ba daga gare ka, kawai ka fad'a min menene? Domin fuskar ka ta nuna alamun damuwa." Babu wani kwane-kwane da b'oye-b'oye domin dole ya Sanar dashi hakkin shi, yace." Allah yayi wa Mimi rasuw..... Kafin ya karasa ya d'aga masa hannu da saurin! Yace." Kar ka k'arasa min naji."!!!!!!! Jahid ya mike daga inda yake ya zauna kusa dashi da kalamai masu taushi yace." Ubangji shine ya hallice ta a sanda yaso babu tsammani kuma a karb'i abunsa a sanda yaso kar ka manta dani da kai duk zamu je inda Mimi taje komai daran dad'ewa mutuwa riga CE, aya ce ga dukanin wani musulmi Mimi tayi sha hada ta mutu ta farkin haihuwa addu'a zaka yi mata."!!
Hannun Jahid ya rike tamau! Leb'anshi na rawa haka zalika jikin shi na wani irin tsuma yace." Innalillahi wa'ina ilahi raji'un. "!!!!!!!!! Jahid ya dinga dukan kafad'un shi alamun rarrashin yana tausar zuciyarsa da kalamai masu sanyi, d'ago idonsa yayi Wanda suka zama kamar Jan gauta bakin shi na rawa yace." Muje a shirya min gawar Momyna ayi mata suttura."!!
Jahid ya mike tare da shi suka futa kai tsaye dakin dasu ke aje gawarwaki suka nufa, tuni an daure Mimi guri guda tana kwance sambal kan wani siririn gado an lullub'e ta da wani farin zani, fuskar ta ya bude, yaga tayi kyau sai murmushi take kamar yayi mata magana ta amsa, zubewa yayi jikin gado yana sakin wani irin kuka. Tare da fad'in"Momyna Allah ya jikan ki, halin ki nagari ya biki, Momyna na hafe miki insha Allahu kece Uwar gida na a aljannar Fiddausi."!

Jahid na tsaye yana kallon shi cike da tausayi da alhini, mik'ewa yayi hade da sanya tafukan hannayen shi ya shafe fuskar shi, ya kalli Jahid din a dake yace." Muje." Jahid ya bishi a baya suka futa.
Ko da ya shigo dakin da muke bai yadda ya had'a ido da kowa ba yace." Zamu je gida yanzu Jahid ya bamu sallama."
Granny da Umma ba yara bane balle maganar sa ta shige su Granny tace"Kai k'ato bana son kumbiya-kumbiya kawai ka fad'a ma kome yi mu 'yan Adam ne zamu dauki kaddara rufewar bata da amfani, shin ya jikin Aishatu ne."? Yana kokarin futa yace." Allah ya amshi ta." Wani irin ihu! Na kurma had'e da bin bayan sa a guje, ina kokarin taddashi tafiyar mu ba d'aya bace ina kuka nake fad'in"Karya kake mugu azzalimi sai dai idan Kaine ka kashe mana ita, idan hakan ta kasance sai na dauki fansa."!!!!!!! Ko juyowa bai ba, ya shiga wani daki, kokarin binsa nake wasu nurses suka rirrike ni suna bani hakuri, wani k'arfi ne ya zo min a lokacin na fuzge daga jikin su sai kace wata mai iskokai na afka dakin a guje! Abunda na gani ya sani jin wani irin jiri tuni na fad'i a gurin ina kallonsu dishi-dishi inda suke kokarin Dora mimi kan wani gado Duk an dad'adaure mata k'afafunta da hannaye ta babu Wanda yabi ta kaina harshi kanshi Jahid din suka tura Mimi dake kwance kan Wani k'arfe suka futa.
Silalewa nayi na fad'i a gurin ba tare dana San a wace duniyar nake ciki ba.
Tuni Umma da Granny sun futa sun tsaitsaya aka futo da gawar Mimi tare da sanya ta a motar asibiti Umma sai share hawaye take yi, suka shiga, dravar yaja motar, lokacin kowa ya manta dani sai Jahid din da ya dawo ta kaina shine duk yayi min taimakon su na likitoci na dawo hayyacina kuka sosai nake yi had'e da dukan shi kamar mahaukaci nake cewa an hada baki dashi an kashe min Mimi, ganin kamar bata cikin hankalin ta ya sanya yayi mata allura take bacci me nauyi yayi gaba da ni.

Wasu nurses ya sanya suka shigar masa da ita mota, ya bar asibitin cikin halin damuwa da tashin hankali, Kamar gawa a ka shiga dani cikin gidan Amjadu inda ya cika da Jama'a maza da mata lokacin tuni an shirya gawar Mimi an futo da ita, saboda haka Jahid kawai ya tsaya nan aka sallace shi da ita, shine a gefe Amjad din a gafe suka dauki makarar dukanin su zuciyoyin su babu dad'i amma dai komai ubangji ya saukar kan bawan shi ne dai-dai.

*25/11/2019*
[11/26, 9:20 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*

*MALLAKAR_ BINTA UMAR*

*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI*

*63*

Mutuwar Mimi ta girgiza zuk'atan Al'umma bamu kad'ai ba hatta da masu gadin gidan sai da suka ji a mutuwar a jikin su, Jama'a kuwa daga ko ina b'arkowa suke yi ta'aziyya wasu kuma gulma ce take kawo su, domin 'yan jarida sun ruga sun gama wa tsawa duniya cewa mutuwar mayar Young millionaire tana da nasaba ne da harin da jama'ar gari suka kai masa, wa 'yanda basu San yayi aure ba suka dinga mamaki shine suke zuwa zaman makoki, mai girma governor Sarkin kano duk dasu akai sadakar uku, su mai citta ma duk dasu babu tsoron Allah ko na kwabo a tare dasu, a fili sun nunawa Amjadu kara a zuciyarsu kuwa murna suke yi sosai, shi kuwa governor abun ne ya soma bashi tsoro ganin yanda yazo zaman sa na k'arshe jama'ar gari na raka shi da dutsina suna fadin "Ba mayi."!!! Kuma tunda ga mutuwar Mimi jama'a suka fara gane cewa harda sa hannun governor akan sharrin da akai wa Amjdin, ranar a tsorace ya bar kofar gidan Amjad ganin yanda matasa suke jifansa kamar ba governor ba, sai da jami'an tsaro suka fara sakin harbi sannan kowa yq shifa taitayin sa, Umma kuwa jin irin zantukan da jama'ar gari suke yi kan mutuwar Mimi yasa tace" Suyi hakuri kar su bata wa Mimi gawa kawai Allah ya amshi abunsa lokacin da yaso.

*****
Yau kwanan Mimi bakwai a karkashin k'asa, na fige na tsigale sai Umma tayi da gaske nake cin abinci kullum ina zaune zukud'inm! Ko kuma in tafi dakin ta in kwanta kam bed dinta hade da rungume wani k'aramin hoton mu, dake cikin frem a kan drowr gefan gado ta aje shi, kuka nake yi sosai, Umma granny dashi kanshi Uban gayya naga duk sun saki jikinsu har hira suke yi suci abunci hankali kwance kuma suyi dariya, ni kadai ce nake cikin halin damuwa da bakin cikin rashin Mimi, tsakanina dashi kallone domun tunda Mimi ta mutum magana ta fatar baki bata hada mu dashi yau kwanakinmu bakwai kenan a cikin gidan shi, ya sake sosai yayi wanka ya shirya harda fesa turare sai abun yayi ta bani mamaki ina zargin sa, dama ya fi son Mimi ta mutu ya cigaba da tsula tsiyarsa take wata irin tsanar sa ta cika min zuciya ta.

Jahid kullum yana kirana a waya sai dai Sam bana sakewa dashi domin gani nake yi kamar bakin su da daya da Amjad din, matar shi Hafsa me kirki da ita duk a gama zaman makokin INA lura da ita da yanda take satar kallona a fakaice.
Chapter 48 · 0% Book details