← Book details Babban Yaro Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 60

Sashe 5

Babban Yaro Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

NTA HAUSA muna tsaka da kallon wani najeria film kawai suka katse tare da nuno *Amjadu* a filin jirgi lokacin yana k'okarin hawa matattakalar jirgi ya tsaya yana magana da wani d'an jarida, tsakanin ni da Mimi ban San Wanda yafi shiga d'imuwa ba, lokaci guda naji wainar da nake fi ta fuce min daga rai duk dadin ta kuwa.
Yana sanye da wasu uban suit blue and white hade da necktie d'insa hannunsa daure da wani irin agogo na zallahr fata sai blue sai shek'i yake, k'afar sa sanye da takalmi rufaffafe black sai shaining yake, hannunsa rike da irin jakar nan ta matafiya.
Dan jarida bayan sun gama magana dashi sai ya juyo yana fuskantar TV din yace." *To masu kallon ga dai Amjadu AbulAbbas Wanda kuka fi sani daYoung millionaire, zai tafi k'asashe biyu domin gudanar da harkokinsa na yau da kullum domin kawo wa k'asar shi cigaba muna yi masa fatan dawo wa k'asar shi lafiya tare da nasarori, duk wani me kaunar sa, sai ya raka shi da addu'a Allah ya bashi sa'a a dukanin abunda ya sanya a gaba.*
Yana gama maganar tashi
A ka d'auke shi, film din ya cigaba, aunt da kawarta suka dinga yi masa addu'a gami da fatan alkairi, Ni da Mimi kuwa babu Wanda yace." Uffan! Har yanzu ko wacce ita tasan halin da take ciki.
Aunt naji tana fadawa kawar ta abunda ya faru kwanakin baya, Zainab tace"Ko sonta yake ne."? Aunt tace " Nima nayi tunanin haka wallahi amma sai naga kwata-kwata bai nuna alama ba, Zainab tace"ke akwai dai abunda yake faruwa wallahi tunda nake ban tab'a jin ance ya dauki budurwa ya kai ta tayi shopping ba sai akan Asma'u ina ganin son ta yake."
Da sauri na kalli aunt Zainab nace"Bani yake so Aunt." Duk suka kalleni nace"Wallahi kuwa Mimi yake so." Mimi tayi saurin sunkuyar da kanta cike da kunya,
Aunt hauwa ta jawo ta jikinta tana dariya tare da fad'in"Kai Alhmdullahi kice wahalar mu ta kusa karewa dama nasan Mimi na ta shiga tsara ce babu namijin da bazai so ta ba farar mace alkyabar mata.. Wai!!!! Kice wata shekarar damu za'ayi aikin hajji.'"" Aunt Zainab dariya kawai take wa kawar tata ni kaina duk da halin da nake ciki sai da na dara ganin yanda aunt Hauwa duk ta gigice! Aunt Hauwa ba dai son kudi ba.

Nace"Aunt kinga ma wayar da ya bata." K'okarin dauko ta nake Mimi tana kwace jakar sai da na Ciro na mik'awa aunt ta karb'a tana dubawa hade da rik'e baki take fad'in"Mimi wannan wayar si tafi dubu Dari."" Lallai Juma'ar da zata yi kyau tunda ga laraba ake gane ta."
Aunt Zainab ta karb'i wayar tana dubawa itama jinjina kai tayi tare da fadin" har wani kamshi wayar take lallai abun na manya ne, Mimi Allah ya dubi maraicin ki, idan kika shiga gidan nan kar ki manta damu don Allah."
Cike da mamaki nake kallon su, ina mamakin son kud'in su lallai a duniya idan kayi kudi ka wuce komai Mimi tun kafin ta shiga gidan sun fara magiya.. Kallonsu kawai nake suna zolayar Mimi ita kuma tana wani sinne kai, cikin zuciyata nace "Kin had'u da aiki babba Mimi.

*********

K'arfe goma da kwata mun fito cikin shiri kamar wasu taurari Munnu nan tazo mu tafi tare, munyi bala'in kyau mussaman ma ni suffa da b'oyayyan kyau na yau sun futo a zahiri saboda abunda bana yi shi nayi wato kwalliyar fuska, kamar wata Queen haka na zama muna sanye da material dinmu Wanda aka yi mana dinki duguwar Riga mai tattara daga baya daga gaba kuma yayi sama anyi masa wani irin yanke gege da gefe dogon hannu ne yayin da rigar ta kasan pitat gown ne gaba d'aya rigar take tayi matse ni tam!! Nishi ma da k'yar nake, gani da manya breast da uban hifs Sai da na sanya yari da sark'a na sannan na kalli mudubi, ni kaina nasan nayi kyau sosai, Munnu da Mimi suka saki baki suna kallona, nace" Meye wai!? Munnu tace." Anya baza ki cire kayan kuwa ba kinga yanda suka matse ki, ke gaki tubar kallah." Nace" lallai Munnu wallahi ko Umma yau baza ta hanani futa da kayan nan ba.Mimi tace" sai ki sanya hijabi idan muka je can ka cire,amma dai kin San gurin ya hada samari da 'yan mata duk budurwar da take da saurayi zata gayyace shi yazo gurin." Nace" Mimi ina ruwana wai don Allah Ku k'yaleni mana." Ganin raina ya b'aci ya sa suka k'yale ni. Umma na zaune s rumfa tana kule-kulen ta muka futo takalemu a tsanake tace "kunyi kyau tamkar wasu amare,amma ke Asma'u meye kika sanya hijabi."?
Nace" Umma dinkin ne ya matsani shine nace"idan na shiga cikin 'yan uwana mata sai in cire." Tace" haka yayi to Ku kula don Allah Ku tsare mutumcin Ku ana gama taro ku dawo gida kar Ku tsaya kad'e-kad'e da raye-raye." Muka ce insha Allahu."

Muna shirin futa daga gidan wayar Munnu tayi k'ara ts dauka a nutse tare da kashe muryar ta, kasa kunne nayi cike da mamaki jin tana ambatar sunan Shamsu. Ni da Mimi muka kalli juna. Ji mu kayi tana fadin"Eh ka shigo da motar yanzu zamu futo." Sukayi sallama, dukaninmu muka kalleta cike da mamaki nace"Munnu yaushe Shamsu ya dawo kuka kuma jone wa." Murmushi tayi tace" shekaran jiya ya dawo da k'arfin sa, Wallahi aurena zai yi domin aranar da ya dawo ma Baban shi yazo gurin Babanmu baku ga kayan da ya kawo mun ba, wannan hayaniyar da muke ciki ce ta hana ni fada muku."
Ni da Mimi muka Ce"Toum Allah ya sanya alkairi lallai alk'awarin Allah ya cika. " dariya Munnu tayi cike da farin ciki muka futa daga gidan. Samari na bakin titi suka bimu da kallo kamar wasu mayu.

Wata had'adadiyar mota na hango a fake gefan titi Shamsu na zaune a mazaunin dravar tare da wani Wanda ban gano fuskar shi na, suna sanye da wata masifaffaiyar shadda wagambari hade da hula damanga sunyi kyau har sun gaji. Ganin zuwan mu gurin yasa Shamsu futowa da sauri ya bude wa tauratowar shi motar yana fadin" Girman kujerar ki ne." Hararasa nayi tare da tab'e bakina nace"Haji Shamsu Ashe zaka dawo ai na dauka muma yaudarar tazo kanmu." Dariya yayi yace." Inaaa!! Baby Asma, Ai Munnubiya ta daban ce cikin mata, tab'e bakina nayi nace"Allah yasa da gaske kake."
Tunda na fara magana abokin Shamsu yake kallona ina kallonsa ta wutsiyar ido tsaki naja a fili na tsani kallo wallahi.
Munnu ta shiga ta zauna Mimi ta zauna nima nashiga sannan Shamsu ya koma gurin zaman shi hade da kunna motar muka tafi.
Shamsu sai janmu da hira yake yana fad'in"Ai duk naji labari lokacin da na tafi har daku ake cewa dama yaudarar Munnu nake yi humm yanzu Asma baby kina ganin zan aikata haka kuwa."
Nace"sosai ma kuwa Shamsu namiji ne fa kai hunm halin Ku sai Ku."Abokinshi ya juyo yana kallona tare da sakin murmushi yace." Baby Asma wasu mazan ne suka bata wasu amma abokina da gaske yake." Tab'e bakina nayi nace" muna da labarin fa duk 'yan Matan da ya yaudara sun kai goma. " Shamsu ya rike baki yana dariya tare da fadin" duk sharri ne wallahi, karya suke min." Mimi tace"Babu sharri nan gaskiya ce mu dai don Allah kar ka kara guduwa domin wancan karon sai da mukayi jiyyar ta" suka kwashe da dariya shi da abokinsa.
Munnu sai mintsina take wai in daina surutan da nake yi ina jinta na kiyin shiru.

****
Lokacin da muka Isa guri ya soma cika sosai aka kawata gurin gurin malamai daban da iyayen yara wajan dalibai daban, muma wajan mu daban wajan manyan baki daban .. Masu hotona da vedio baza su kirgu ba, saboda ko wacce da nata,muma mun dauki namu can muka tadda shi, MA kad'a sun fi su biyar suna gefe suna jiyar taro ya watse a fara shagali. Ko wane class da gruop d'insu da kuma irin kalar ankon su, ko wacce tana wace wannan.

Mai girma principal ya bude taro da addu'a tare da yi mana nasiha sannan yayi wa 'yan matan da aka kusa bikinsu a cikinmu addu'ar zaman lafiya Wanda basu da mazaje Allah ya kawo musu, hakanan Wanda suke shirin cigaba da karatu Allah ya bada sa'a.

Haka Malamai suka dinga mik'ewa suna jawabi tare da addu'a, taro ya tashi guri ya hautsine kowa da ta wagar mutanan shi, da kawayen shi sai d'aukar hoto ake hade da vidio,

Ina gefe tare da jama'a ta domin wasu ma ranar na fara ganinsu duk ya wancin su maza ne, tuni na cire hijabina ina yawo yanda na gadama 'yan ajimu sai jana suke dole sai munyi hoto duk inda na sanya kafa abokin Shamsu nan yake sauke tasa ya zame min jele, haka na dinga shiga cikin abokan da samarin 'yan ajinmu muna hoto wasu nayi da waya wasu nayi da Camera man. Abun mamaki ni kadai jama'a suke ja lallai sai sunyi hoto dani, haka Alina ma duk gabar da muke da ita sai da tazo ta jani cikin a bokanta maza da mata mukayi hoto wasu daga cikinsu na fiddo wayoyinsa nayi min.

Mimi ce tazo ta jawo ni da k'arfi tana fadin" meye haka kike yi don Allah ki daina ratsa maza kina shiga tsakiyar su baki San suba
Fuzge hannu nayi INA fadin "Kinga Mimi yau rana daya ce daga ita babu wata ki k'yaleni." Mimi ya rabu dani ta koma gurin Munnu da sauraynta
Chapter 5 · 0% Book details