← Book details Babban Yaro Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 60

Sashe 30

Babban Yaro Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan Sallah Jama'a aka d'aura auran Asma'u da Mimi a babban masacin juma'a Mai Martaba sarki ne ya karb'i wakilcin Amjadu duk da cewar akwai wakilan sa, d'aurin auran ya samu halatar manya manya mutane sosai abunka da na Jama'a garin labarin d'aurin auran Amjadu ya baza garin kano da ma kewayen ta, 'yan jarida sun samu abinyi,da kyar ya samu ya futo daga cikin jama'a ya shiga mota ba tare da b'ata lokaci ba ya umarci doh, ya wuce dashi gidan granny saboda yasan in gidansa ya wuce wata Matsalar ce Jama'a gami da 'yan jarida baza su kyaleshi ba.

*15/November/2019*
[11/16, 10:02 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*

*MALLAKAR_ BINTA UMAR*

*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI*

*53*

To gidan granny ma cike yake da 'yan uwa da abokanan arzikinta sun zo taya ta farin ciki mutanan Chadi ma suna kan hanyar zuwa, aikuwa suka yi masa caaa! A ka masu tsokanar sa nayi masu fad'a masa magana nayi a fakaice Inna Suwaiba take yar masa da magana yak'i d'iyar ta Hafsa gashinan ya kwasowa kansa kara da kiyashi, wad'anda suka San akwai maganar sune suka fahimci inda ta dosa basu dad'in abunda tace ba ko babu komai ai matar mutum kabarin sa ce, Granny ma bata ji dadin abunda Inna Suwaiba take yi ba, tunda tazo gidan take yar da haibaci sai kace k'aramar yarinya.
Shi dai shigewar sa yayi bedroom din granny don har ga Allah baya cikin nutsuwar sa ballanta ma ya fahimci Abunda Innarshi take nufi

******
Wallahi duk makiyin mu idan ya kallemu sai mun burge shi, munyi kyau ni da Mimi har mun gaji duk inda muka wuce cikin jama'a sai kaji suna fad'in "Wai wacece amaryar ne tsakanin su biyu sai da a nuna Mimi kawai amma lokaci guda baza ka ban bance mu ba, sai hotona muke da k'awayenmu, ko wacce da k'atuwar wayar ta, nima hannu na rike da wayarshi da ya bawa Mimi mai muguwar camera mai fidda mutum nasa Munnu ta dinga d'aukar mu hoto ni da Mimi, wacce take cikin tsananin farin ciki da annushuwa.
Umma ita da jama'ar ta sai hidima suke yi aunt Hauwa kuwa ai ba'a ganinta, tun da safe da suka gama rigima da Mimi kan wani magani tazo dashi cikin jarka wai lallai Mimi sai ta shanye shi, Mimi taki shine take tayi mata masifa, nice na lallab'ata ina fada mata amfanin maganin a jikinta sannan ta dauka tasha, magani iri-iri aunt Take dirkawa Mimi wai lallai sai tayi ni'ima ni kuwa dariya kawai nake musu mussaman in naga Mimi na kuka tana shan magani. Yanzu ma gidan kawarta ta tafi wai zata karbo wani turare duk dai Mimi ake so tayi amfani dashi kafin a kaita dakin mijinta.

Dakinmu cike da 'yan uwanmu da k'awayenmu sai surutu kake ji ana shewa zan can aure kawai mukeyi ina gefe ina sanja kayana wayar Mimi tayi kara, dama tana kusa dani ina dubawa naga heartbeat nace" Mimi zo ki d'auka. " da sauri tazo ta karb'i wayar daga hannuna, ihu! 'Yan dakin suka sa, suna fadin"Da Alama ango ne ko."? Gyada kaina nayi nace." Shine ya kira yaji lafiyar amaryar shi" suka fashe da dariya hade da tafawa suna Fadin "hohh-hohh Yau Mimi zata ji maza."! Ita dai futa Tayi daga dakin tana murmushi.

Yana kwance kan bed din granny ya cire babbar rigar jikinshi daga shi sai singlet da dogon wandon arniyar shadda da yayi futar d'aurin auren sa, da ita, juyi kawai yake yi zuciyarsa babu dad'i, ji yayi kawai yana sha'awar jin muryar Asma'u yasan hakan ba dai-dai bane, to ya rasa ya zaiyi da zuciyar sa, wacce take nema tafi karfinsa a kan Asma'u, wayar sa ya dauka ya kira numbar Mimi yana fatan Asma'u ta dauka kamar ko da yaushe, sai dai sab'anin haka Muryar Mimi yaji tana yi masa sallama, lumshe idonsa yayi hade da d'an cije lips d'insa na kasa, yace." momyna ya hidima."? Mimi ta damkewar wayar sosai wani irin dad'i na ziyartar zuciyar ta, a hankali tace." Alhamdullahi." "Ok babu wata matsala ko." "Eh babu mungode sosai da Hidima" murmushi yayi kawai yana jin tausayin yarinyar yasan so masifa ne, abunda yake ji a halin yanzu yasan shi take ji a zuciyar ta dole ya girmama mai sonshi yace." Haka nake so, Idan anjima Ku shirya akwai Walima da abokina masu mak'otaka dani suka shirya min,zan aiko a dauke Ku a mota OK." Mimi tace." Insha Allahu. Kokarin kashe wayar yake tace" ko in bawa Asma'u wayar ne." ? Girgiza kansa yayi kamar tana kallonsa yace." K'yaleta kawai Momyna zamu gaisa idan anjima OK."
Kafin Mimi tace Wani Abu ya kashe wayar yana jin wani mugun daci a bakinsa, ko wane ango yana farin ciki ranar d'aurin auransa mussaman idan ya tuna amaryar sa, amma shi ranar d'aurin sa ta zame masa ranar bakin cikinsa Asma'u ta cuce shi, bai ta tunanin zai fada rudani na so irin wannan ba.dole yayi kokarin sa Mimi cikin zuciyar sa, ko don ya haddasa Asma'u ciwan zuciya kamar yadda take kokarin haddasa masa, wannan itace shawarar da ya yanke.

****
Mimi ta dawo fuskar ta cike da walwala da farin ciki, tace"Asma'u yace." Mu shirya bayan sallah magariba zai turo a dauke mu akwai walima da a bokanshi suka hada masa, da har nace ko in baki wayar Ku gaisa yace A'a in k'yale ki." 'Yan dakin suka kwashe da dariya tare da fad'in"Haka kurrum yana jin zakin muryar ki, zaki had'a shi da masifaffiya mai saurin baki, mai zai fuskanta ya burgini da ya gwale ki." Dariya suka kwashe da ita har Mimi din, wani irin b'acin rai ne ya kamani lokaci guda, ganin yanda suke min dariya sai naga kamar da gayya suke yi min har ita Mimi din, raina ya b'aci mutuka, Mimi tace. A bani wayar yace baya bukata lallai ma guy nan, cikin jin haushin su nace banzaye 'yan iska kawai baku da aiki sai iskanci da dariya Ko wacce ta rasa mashinshini don Allah a daure ayi aure ko kwa rage zumudi da tsiyayar da kuke yi." Ihu!! Suka sanya kamar wasu shashasha, Maryam tace"Dallah malama yi mana shiru ke akwai wacce ta fiki zuba, daga an fara zancan aure zaki hau lumshe ido idonki har ja yake yi "yar iska, hahahahaha " ta k'arashe maganar tana dariya Tare da bawa ta kusa da ita hannu suka tafa tsaki naja me k'arfi nace "Kanku a keji, kun dai ji Abunda Mimi tace ko, gaskiya Ku kintsa sosai bana son shirme a gurin ku zama manyan baby's kar Ku bani kunya shegu." Munnu tace"Dole ne ai nasan gurin zai had'a had'addan Samari gaskiya

Dariya muka kwashe da ita nace"Munnu ta Shamsu kenan" Hararata tayi, ni ko na cigaba da shiryawa ta ina mata dariya, aunt Hauwa ce ta lek'o dakin tare da kiran Mimi hannunta taja suka futa, nace"Mimi yau kin bannu a gurin aunt Hauwa.

****
K'arfe takwas dai-dai gurin Walima ya k'ayatu, nan cikin Estate din aka shirya komai guri Tasha decoration, haske ko ta ina ga wasu shegun kujeru an ajiye guda biyu na ango da amarya ne, su uku ne kacal cikin Estate din, Ma'aruf Mujahid Hafiz sai Amjadu din, dukanin su ma'aikata ne, Hafiz yana aiki a babban banki najeria, shi kuma Ma'auruf yana aiki a babban Asibiti na nasarawa Mujahid yana aiki a Company d'angote cement shine manager dukaninsu suna da aure da yara biyu Hafiz ne me D'a d'aya tunda shi bai jima da yin auran ba, sai Amjad da yayi aure yanzu, suna zama na fahimtar juna a tsakaninsu, kasamcewar su Ma'aikata yasa basa haduwa sosai sai weak end suke had'uwa su gaisa da junansu sai kuma lokacin azimi suke shan ruwa tare, yau idan an sha ruwa gidan wannan gobe a sha gidan wancan, Amjad sai dai yaje domin shi bashi da matar ma, sunyi ciwon baki har sun gaji, Matar Hafiz me suna Samina ita ce ta dinga nanika masa k'anwar ta yana basarwa da ta lura ba auran zaiyi ba kawai sai ta hak'ura, amma dukaninsu sun yi mamaki da suka ji labarin auran sa katsaham! Shine suka shirya masa walima domin taya murna, amma da ba don haka ba , shi babu wani shiri da yayi domin murnar ranar.

Dukaninsu sun gayyaci abokanan su shiyasa guru ya tsaru domin duk manyan 'yan boko ne samari masu kwalisa gayu kenan, ango kuwa babu wani abokan shi da ya gayyata, to yawanci ma shi bai fiye sakewa da mutane ba, kuma abokan shi da suka shak'u da juna turawa ne, 'yan gari daban-daban shiyasa sam bai da abokai a najeria sai Wanda ba'a rasa ba.

Shigar wani irin yadi suke yi baki Wanda bantab'a ganin irin shi ba, dinki iri daya huluna iri daya takalman su iri daya kai hatta da agogon hannunsu iri daya ne, sunyi kyau sosai da sosai, Amjad ya futo ango dashi sai gaisawa yake da jama'a fuskar shi babu yabo babu fallasa.
Chapter 30 · 0% Book details