← Book details Babban Yaro Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 60

Sashe 14

Babban Yaro Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Carbin ta aje ta kallemu tare da fadin "Babban al'amari ne yake tunkaro mu dani da Ku, ina so kuyi min adalci kuyiwa kanku a adalci bana son zumuncin Ku ya lalace saboda duk inda akace kishi to sai anyi shi ko ciki daya kuka futo
Yanzu daga gidan Yunusa nake Wannan yaron da yake Neman Ku da aure tun safe ya turo magabatan sa, da kud'in aure harda sadaki yace." Nan da wata guda yake so, ayi komai a gama. Kawu Yunusa ya amsa musu hade da karb'ar dukiyar auran, kafin in futo daga gidan Aminu yaje da maganar shi ta cewar yana son auran ki." Tafad'a tana nuna Mimi da hannu, a cewar sa tun kina yarinya yake sonki ya ki fada ne kawai saboda yana ganin baza ki fi k'arfin sa ba, sai Kuma gashi lokaci guda wanki hula na Neman ya kaishi dare.
Kawu Yunusa yace magana ta wuce tunda har ya bari aka karb'i kud'in auran ki. Sai dai yayi hakuri kawai. Yanzu halin da ake ciki yana babban asibiti na Malam Aminu domin fad'uwa yayi a gurin har na tawo bai dawo dai-dai ba."
Umma ta k'arashe maganar ta zuciyar ta babu dad'i.
Nace"Umma me yasa Ya Aminu bai yi magana da wuri ba har sai da ya bari aka karb'i kud'in auran ta, to ai itama Mimin. Zata shiga wani hali
Kuma jiya mun gama magana da Amjadu cewar ya janye aurena saboda rashin dacewar haka, Mimi zai aura kuma daga baya azo ana kace nace."
Umma tayi shiru fuskarta cike da alhini.
A hankali Mimi tace." Umma ki kwantar da hankalin ki, Indai akan sona Yaya Aminu ya suma har ta kaishi ga kwanciya a asibiti insha Allahu ni zan share miki hawaye
Dama nike son Amjadu bashi ba Asma'u yake so tuntuni zuciyata takasa yardar min da haka, Umma zan auri Ya Aminu ki kwantar da hankalin ki."
Umma ta share hawayen ta, tace"A'a Mimi bazan miki dole ba bayan an kawo kud'in auran ki saboda son kaina ince ban yarda ba ga Wanda nake so ki aura duniya sai ta zage ni mutanan gari su dinga fadin"Don bani na haife ki ba shiyasa nake miki bakin cikin shiga cikin daula bayan haka kuma zuciyar ki tana son Amjadu idan nayi haka ban miki adalci ba, dole Aminu shine zai janye kudurinsa."

Kuka Mimi ta sanya hade da rungume Umma tana fadin "Wallahi Umma da gaske nake babu abunda zaki nema a duniyar nan ban yi miki ba, mutukar ina dashi, Na hak'ura da Amjadu zan auri Ya Aminu."
Cikin kuka ta k'arashe maganar.

Rungume ta Umma tayi tana kuka, nima naji k'walla ta cika min ido nace"Umma yaushe zamu je asubitin ."? Je ki d'aura abunci da sauri ana idar da sallahr magariba sai muje."
Mik'ewa nayi na nufi kicin.

*7/November/2019*
[11/8, 11:36 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*

Mallakar_BINTA UMAR

LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.

44

A gurguje na kammala dafa abunci shinkafa da faduka nayi wacce taji allayyahu da albasa, Bayan mun idar da sallahr magariba ne muna shirye-shiryen tafiya sai muka ji sallama Umma ta futo da sauri Yaya Aminu ne da Musa da Kawu Yunusa suka shigo, Umma tace"Kaddai an sallame shi."
Kawu Musa yace." Gashinan kina gani dama nace Zai farfad'o Suma yayi."
Ya Aminu ya zauna kan tabarma hade da dafe kansa.
Nida Mimi muka futo muka tsaitsaya
Dariya nake wa Ya Aminu ganin yadda ya fyad'e lokaci guda.
Sallama Kawu Yunusa yayi suka tafi ni da Musa kuwa babu Wanda ya kula kowa.
Umma tace"Maza je ki kawo masa abunci."
Kicin na nufa da saurina.
Mimi ta zauna gefansa tana yi masa ya jiki.
Abunci na kawo na aje gabanshi
Naje na dauko ruwa pure watar babu sanyi,yace." Kije ki siyo min me sanyi."
Umma ta mik'o min ashirin tare da fadin"Ki siyo guda hudu.

Hijab din Umma na zura na futa daga gidan da sauri

Ya Aminu bai ci abincin sosai ba ya aje cokalin ya mike ya bar gurin.
Duk muka bishi da kallo. Umma tace"Cuta ta samu manya ." murmushi nayi kawai
Mimi kuwa tashi tayi simi-simi ta shige dakinmu
Nida Umma bamuyi hirar arziki ba muka tashi
Ina shiga dakinmu na tadda Mimi ta juya baya tana Kuka harda shashsheka.
Cikin mamaki nace"Mimi kuka kike yi."?
Banza tayi min
Da sauri naje na birkitota sai naga idonta yayi mugun ja sai ajiyar zuciya take.
Zama nayi kusa da ita hade da rike hannunta nace"Mimi nasan kin amsawa Umma ne domin ki kwantar mata da hankali.
Nasan bakya son Ya Aminu Amjadu kike so Mimi me zai sa baza kiyi wa kanki gata ba zaki jefa kanki cikin mummunan hali. Kinsan bakya son Ya Aminu me yasa kika amsawa Umma."
Hannuna ta rike tamau! Naji jikinta sai karkarwa yake
Tace." Asma'u na rasa yanda zanyi da zuciyata nayi-nayi incere son Amjadu abun yaci tura ji nake kamar zan mutu Mimi zuciyata tana azabtar dani kan abunda bazan samu ba, don girman Allah ki taya ni da addu'a zuciya tabar cutar dani, soyayyar da nakewa Amjadu Allah ya cire min ta gaba daya ta koma kan Ya Aminu."

Kuka nasa saboda tausayin ta tabbas so bala'i ne hannunta NA rike dake yin wani irin karkarwa nace"Mimi zan sanya ki a adduata in sha Allahu, kinga na farko ke kika cuci kanki d'azu da Umma tayi miki maganar Aminu sai ki nuna rashin amincewar ki, tom kinga daga baya baza kije mata da wata magana ba.
Zan cigaba da taya ki addu'a Ubangiji Allah ya yaye miki ya zab'a miki mafi alkairi."
Sosai take kuka ina rarrashinta
Sai kuma naji ta fara wani irin tari!! Na mike da sauri na dauko mata ruwa
D'ago ta nayi na fara bata,
Tana shan ruwan tana tari da idonta yayi jazur
Cire ledar ruwan nayi na bugun bayan ta.
Tare da yi mata sannu.
Dana ga tarin yak'i sauk'i futa nayi da sauri na dauko gishiri a kicin na zo na Dan gwala mata a baki.
Tafi minti goma tanayi sannan ya lafa.
Sai haki! Take.
Ruwan na mike mata ta karba ta sha kadan.
Nace "ki kwanta kiyi bacci zakiji sassauci.
Kwanciya tayi tana lumshe idonta
Sai dana ga bacci ya dauke ta sannan nima na kwanta ina sak'e-sak'e Cikin zuciyata.
Bacci ya soma fuzgata naji kiran waya
*haetbeat* tsaki naja na dauki wayar na kashe gaba d'ayan ta domin shi nake mutukar jin haushi a ganina duk shine ya jawo mana wannan masifar.
Tun farko da bai nunawa Mimi yana sonta ba, ina ganin duk haka baza ta faru ba.
Da tune-tune bacci b'arawo ya kwashe ni.

******
B'angaran Amjadu kuwa, tun bayan da Wakilansa suka zo suka Sanar masa da cewar An bashi guda cikin 'yan Matan da yake so ya aura sai gaban shi ya fad'i ya tunini ko Mimi ce, shine dalilin da yasa ya tambaye su kud'in wacce a ka karb'a a cikinsu nan Kawunsa yace." *Asma'u* yaji dadin haka don haka kafin su tafi sai da yayi musu kyauta ta mussaman.

Shirye-shiryen bude company ya kammala yau saura kwana biyu gari ya dauka kafufin yad'a labarai in ka bude zancan kenan *Ranar Juma'a Biyu ga watan bakwai za'a bude shaharrarn company nan wato AmjaduAbulAbbas materials* za'ayi bononza a ranar abun dubu daya Dari biya abun dubu goma dubi biyar. Mutanan gari sun kunzige kudinsu suna jiran ranar domin su je su kwaso garab'asa.

***
Washe gari muka tashi da jiki a sanyaye Mimi ta rame lokaci guda, shi ko Ya Aminu dama tunda Kawu Yunusa ya Sanar dashi cewar an fasa karb'ar kud'in Mimi ya watsake ko da ya tashi da safe tamkar Wanda bai yi ciwo ba, yanzu Mimi CE abun tausayi so ya tasa ta a gaba.

Da kyar na rarrashe ta ta Karya kummalo
Umma ta tsaya bakin kofar mu tana fadin "Menene wai naji kuna takkadama."?
Zuciyata tace kawai ki fadawa Umma ko menene ko Allah zai sanya ta fahimta."
Kaina a kasa nace"Umma ina ganin wa....Shiru nayi na kasa magana.
Umma tace." Meye kika yi shiru."?
Bakina na rawa nace"Umma don Allah Ya Aminu ya janye kudirin sa a kan Mimi akwai cutar wa a ciki, ya kamata Mimi a bata zabin zuciyarta Ya Aminu Namiji ne shi zai iya jure komai kinga Mimi ko yarinya ce mai karanci shekaru gata kuma mace."
Shiru Umma tayi tana nazarin magana ta.
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali tace"Kin yi gaskiya Asma'u ni ma zuciyata batayi na'am da haka ba, saboda ina gudun zagin jama'ar gari tunda duk sun San komai Da Aminu da ke da Mimi duk daya kuke a gurina babu Wanda zan ce nafi so, amma kina ji da bakin ki tace ta amunce da Aminu kuma ko jiya Kawun Ku ya maimata min maganar babu gudu babu ja da baya tunda sunyi magana da mahaifin ta a waya yace ya bashi wuka da nama, Babansu Munnu ma har dashi cikin maganar kin ga bani da ta cewa."
Chapter 14 · 0% Book details