← Book details Babban Yaro Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 60

Sashe 54

Babban Yaro Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana dariya tace"Yanzu zata nuna muka halin nata na k'uya Iyami kadai ta sani saboda ita take bata abunci ni kaina wani lokacin sai taga dama take yarda dani." Aikuwa sai ta fara tab'e baki tana so tasa kuka, rungume ta nayi ina rarrashin ta, granny kuwa sai dariya take mana, Iyami ta shigo da fidar ta da sauri ta sanya mata a baki ta kama tana tsotsa sosai, Dan kanta ta cire bakinta sannan ta fara daga hannu wai zataje gurin Iyami aikuwa Munnu tace"Baki isa ba kuwa kin bar hannunta da sauri ta karb'a ta a hannuna ta dauki towel dinta ta goya ta a bayan ta, mik'ewa nayi da sauri Iyami ta mik'o min duk abunda zamu bukata nata, nace "Granny zamu tafi gida." Tace"To Ku gaida min Ummanku da kyau kuce ta kyauta." Nace insha Allah kuwa. "Har waje Iyami ta rako mu tana d'agawa baby hannu ita kuwa sai dariya take bangala mata tana daga bayan Munnu." Ganin rana ta kwalle nace dama zanga su Rambo da sun kaimu gida. Wata zuciyar tace min lallai Asma'u kina da samun shiga. Ni kaina dariya nayiwa kaina. A dai-dai sahu muka shiga nace"Munnu muje gida yau Umma taga baby inyaso sai ki tafi da ita ko."? Munnu tace "Shikkenan muje.""' Wasa nake ma baby daga bayan Munnu ita kuma sai bangale min baki take, nace"Laa Munnu kinga har ta soma hakori wallahi. " Munnu tace"Da gaske ne." Nace sakkota ki gani.' Aikuwa ta fara kokarin saukota tana dubawa, Kuka ta fara yi da alama tafi son goyon nace"Munnu mai da ita bayan baki ji yanda nake jin zafin Ku kanta Cikin raina ba." Kokarin mai da ita take, naji kira ya shigo waya ta, hankalina na can gurin rarrashinta ban duba waye me kiran ba na d'aga wayar hade da sallama.
Kukan Sweet heart dinshi ne yayi masa sallama, ranshi ya kara b'aci a fusace! Yace." Wai ke wace irin mayya ce ne? Meye alak'ar ki da baby da zakiji har gida ki dauke ta, OK naji kamar alamu kuna cikin abun hawa ne ana min gwajab-gwajab da yarinya tana kuka na rashin sabo. Maza ki mai da ita inda kika daukota tun wuri."! Hannuna ne yake rawa bakina na motsi na rasa abunda zan ce masa, Munnu dake kusa dani duk taji abunda yake cewa, hannu ta mik'a min wai in bata wayar , domin in fidda kaina a gurin shi nayi saurin bata wayar ta karb'a a nutse tace"Yallab'ai barka da rana." Jin muryar da bata Asma'u ba ya amsa da " Barka dai wacece ke."? Munnu ta tsorata jin muryar sa a kausashe!! Tace." Munnubiya ce, dama umm! Dama.... Babanmu ne yace muzo humm nazo in d'aukar masa baby Aysha yana so ya ganta.......... Sam bai gane Abunda take nufi domin shi har ga Allah ya mance da Kawun Mimi wato babban su Munnu, yace." Ke! Bana son shashanci dallah!Ku mai da min da yarinya wato wayar ta baki domin Ku shirya karya ni sa'anku ne."!? Cikin tsawa ya fad'i maganar! Nan Munnu ta kara daburcewa tace"Da gaske ne kayi hakuri Wallahi an turo ni daga gidan profesor Muktar Gyaranya ne ni 'yar shi CE" sai da ta fadin sunan Profesor Muktar sannan ya tuna da Mutumin , kashe wayar yayi ba tare da yace komai ba .Munnu ta kalleni tana dafe k'irji tace"Bala'i wannan guy anyi masifafe irin sune suke rigima da matayen su akan 'yaya gaskiya yana do son "yaya tab!!!!!!!

Girgiza kaina nayi ina tunanin abunda zanyi na huce takaicin abunda guy nan yake min aka 'yar Mimi wai ni yake kira da mayya lallai duniya. Ji nayi wasu hawaye na kokarin zubo min. Cikin zuciya ta nace zaka cigaba da kirana da wannan sunan indai akan baby ne. Nafi maye ma maita!
Umma taji dadin ganin baby sosai ta karbe ta ta rungume ta sosai a jikinta tana kallon Munnu tace"Ki bar min ita ta kwana a gurina gobe sai ki zo ki dauke ta ki kaita can gidan NAKU." Munnu tace"To Shikkenan, haka tayi mana sallama cike da jin kunyar Umma.

****
Amjad Kuwa bayan futar Su Asma'u ne ya kira wayar granny domin ya ji gwalatun babyn shi dama baya minti ashirin bai kira waya ba, kawai granny tace masa wai su Asma'u sun zu sun tafi da ita, a lokacin ji yayi kamar ya bar Abunda yake yi ya dira najeria ya yaga yarinyar saboda rashin zuciyarta har granny ma sai da ta fuskanci b'acin ransa dama ta saba indai akan baby ne rufe ido yake yayi kamar bai San mutum ba shiyasa Iyami take takatsatsan dashi, kashe wayarta tayi ta k'yale shi shine fa ya kira Asma'u a waya ya sauke mata rashin mutumci, ya Riga ya saba da baby kullum kafin yayi bacci sai sunyi hira Sam bai ji dadin wannan Abu ba, Dan dai kawai yana ganin mutumcin Mutumin ne.

****
Kwata kwata na mance da rashin mutumcin da guy yayi min, hidimar baby kawai nake yi yini Abu daya. Don har gidan aunt Hauwa mukaje da ita wai lallai sai na bar mata ita naje bazan iya ba. Ko sallama banyi mata ba na futo daga gidan.

Misalin goma na dare na gama lallab'ata tayi bacci na bude data muna hira da Mujahid, kira ya shigo wayata, ina dubawa naga numbar k'asar waje ne sai nayi mamakin waye zai kirani da wannan numbar ne. Cikin sanyin murya nayi sallama, nashi b'angaran yaji wani irin fad'uwar gaba jin muryar ta da alamun bacci ta kashe masa jiki, gyaran murya yayi yana kokarin dai-dai ta nutsuwar shi, yace." Ki duba na miki magana ta whstsap ki bani amsa yanzu."! D'iff! Ya kashe wayar mik'ewa zaune nayi da sauri ina kara duba numbar, tabbas shine domin numbar irin ta d'azu ce da ya kira lokacin muna a dai-dai sahu. Messages na fara dubawa Aikuwa na ga nashi can k'asa, ni ban ma San sanda ya shigo ba, girgiza kaina nayi kawai na bude ina dubawa.

_Ki turo min numbar wannan k'awar taki ina so muyi hira da Sweetheart_

Abunda ya rubuta kenan. Na karanta ya Kai sau goma da gayya na kashe data ta ganin yana online nasan ni yake jira. Cikin rashin sa'a kuma Jahid ya kirani a waya ganin na rufe data yace." Ko bace zakiyi ne naga kin rufe data gashi ni kuma ban gaji Da jin muryar ki ba." Nace"Nima haka my Jahid muyi hira mai dad'i aikuwa muka dinga hiraramu ta soyayya

Amjad nashi b'angaran yana sauraron yaga ta turo masa da numbar Munnu kawai sai yaga ta rufe data kuma gashi ta ga sakon bashi,ranshi a b'ace " ya fara kiran wayar ta a karo na biyu . wayar taki tafiya sai ace masa busy ya kira ya kai sau goma busy jifar da wayar yayi kan bed din da yake kwance yana Jan wani mutsiyacin tsaki tare da mamaki dawa take yin waya tsawon wannan lokacin..........................

*28/11/2019*
[11/29, 9:22 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*

*MALLAKAR_ BINTA UMAR*

*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI*

*67*

Mun fi rabin awa muna hira da Jahid a waya sannan yayi min sallama tare da fad'in"My Wife insha Allah, kiyi bacci mai dad'i kuma kiyi mafarkin kina gidana da yardar Allah." Cike da kulawa nace"Insha Allah Jahid zan kwana mana addu'a ni da kai." Sosai yaji dadin kalamai na cike da farin ciki ya kashe wayar......Mik'ewa nayi nima na futa domin wani irin futsari ne ya kulle min Mara, tsakar gidan shuru Umma ta juma da yin bacci, ina dawo wa na tadda baby ta farka tana cilla k'afafu daukar ta nayi da sauri don kar tayi min kuka, ruwa na fara bata sha ina kokarin bata madarar ta naga ta zura k'aramin ya tsanta a baki tana tsotsa bacci ya dauke ta, ajiyar zuciya na sauke na gyara mata kwanciya na kwanta kusa da ita, bacci ya soma fizgata naji shigowar kira waya ta na manta ban kashe ba, idona a lumshe na dauki wayar ina dubawa tsaki naja kamar in kashe wayar sai kuma wata zuciyar tace dauki kiji me zai miki." "Hello." Abunda na fada kenan kamar me ciwon baki,, sama-sama naji shi yana fadin"Ke ni kika rainawa hankali na miki magana kin share ni, kuma na kira wayar ki kina waya Lokaci mai tsayi! Nace "Ki turo min numbar Munnubiya ko." Kamar wani Ubana haka yake min magana da masifa! Cikin sigar kuntatawa nace"Ni fa duk ka dame da wani surutun ka, bani da numbar Munnu ko ina da ita ma bazan bayar ba, ba dai a kan 'yar kake min wannan hayaniyar ba Tom sha kurumin ka baby Aysha na gurina yanzu ma ta farka daga bacci na bata ruwa tasha, ka cigaba da kirana mayya a kanta wallahi dad'i nake ji, maganar da wa nake waya bai dame ka ba, mutum na son yayi bacci an dame shi."!! Kashe wayar nayi gaba ki d'ayan ta, wani irin sanyi naji cikin zuciyata na mayar masa da Martani Nasan yau da kyar in zai iya bacci.
Chapter 54 · 0% Book details