← Book details Babban Yaro Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 60

Sashe 24

Babban Yaro Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ga mamaki na sai naga Mimi ta kashe wayar kamar yanda na umarce ta ta aje wayar gefan kamar ba ita ta saki fuska sosai tana yi min hira. Mamakin ta kawai nake, nace ta kashe waya ta kashe babu kara bare tayi min magiya kan in karb'i wayar kamar yanda ya bukata, lokotan baya idan taga ina mishi wulakanci haushi take ji amma banda yanzu. Kwanciya nayi gefan ta ina lumshe idona sama-sama naji muryar narse na shigo tana tashina, na bude idona Wanda suke cike da bacci ina kokarin mik'ewa zaune.

Mimi tace" Ki k'yaleta mu kwana tare domin ko a gidama a tare muke kwana." Nurse ta futa bata kara magana, sama-sama muke yin hira da Mimi bacci yaci karfina ban San sanda ya kwashe ni ba.

Shida shaura na Safiya na tashi lokacin har masu bada magani sun shigo dakin sun bawa Mimi wacce take zaune dungurgur taki yin bacci saboda tsabar farin ciki, mik'ewa nayi ina hamma idona cike da bacci nace." Mimi shine baki tashe ni ba ko? Kinga na rasa sallah asubah."

Murmushi tayi tare da fadin "Asma'u naga a gajiye kike gashi kince bacci kike ji shiyasa na kyaleki kiyi hakuri." K'wafa nayi kawai na sauka daga gado toilet din dake cikin dakin na shiga.

K'arfe takwas dai-dai likita ya shigo ya gama aune-aunen sa kan Mimi kuma yaji dad'i da ya duba yaga yanda ta kwantar da hankalin ta, nan ya rubuta sallama hade da kara tausar Mimi sosai kan ta kiyaye ta daina saka damuwa a ranta. Nima kuma yace." Mu dinga sanya ido ankata sosai muna guje b'acin ranta.

9:00 am mun futo daga asibiti da bamu shigo da kaya komai ba amma zamu futa dasu niki-niki a hannu muna futa harabar asibitin wata shirgegiyar motar *Siyana* mai dauke da tambarin *A&A mai nasara* sabuwa dal! Ta shigo gurin, Dravar shi ne ya futo da sauri muka hada ido dashi. Saurin kauda kaina nayi daga kansa

Ya k'araso gurimu hade da zubewa gaban Umma yana gaishe ta ta amsa a sake, Ummansu Munnu ma ta amsa ita da aunty Hauwa, sai ya mike hankalinsa na kaina yace." Ranki ya Dade oga ne yace in zo in kaiku gida."

Cikin zuciyata nace shi kuma ko wa ya fada masa anyi sallama oho! Shiru nayi masa, aunt hauwa naji tana fadin"Aikuwa mungode dama yanzu muke tunanin a dai-dai ta nawa zamuyi damu da kayan mu." Na muka nufi motar kowa na fadin albarka cin bakinsa.

Duk yawan mu damu da kayanmu motar sai da ta dauke mu, hat guri Yayi saura doh-doh yaja motar muka tafi gida, Mimi ta sake sosai ina jinsu suna hira da Munnu ban tanka musu ba.

Goma shaura muka Isa gida Har ya danyi kura saboda rashin mutane a gidan kwana biyu kawai, ni da Aunt Hauwa muka fara aiki Ummi da Mimi kuwa na rumfa daga inda muke muna jin yanda Umma take rarrashin Mimi da kalamai Masu dad'i da kwantar da hankali.

******

Yau Kwana ki biyar kenan da bud'e sabon company me zaman kansa a jahar kano company *A&A mainasara* ya amsa sunansa sosai ya samu daukaka domin an fara gudanar da harkoki yanda ya kamata kullum a cike yake da baki daga garuruwa daban-daban sun shigo d'aukar kaya.
Hakanan Sauran company sa na waje suma komai ya kammala harkoki ake sosai da sosai Allah ya shiga al'amarin.

Sanye yake da wani yadi mai masifaffan kyau da tsada ni kam sai ince ma a jikinsa na tab'a ganinsa milk coulor ne mai sharashara anyi masa dinki boda yayi amfani da singlet black kana ganin shatin ta, bai sanya hula ba taje lafiyayyar sumar sa yayi wace take bakkirin sai shek'i take, ya gyara sajan sa kamar ko da yaushe ya feshe jikinsa da turaran shi na ko da yaushe, takalmi mai gidan ya tsa ya sanya a fararen k'afafun shi, blck ne sunyi masa kyau ba kad'an ba, hannunsa daure da agogon shi, na zallar fata fad'ar kudin shi ma b'ata wa ne, komai na Amjadu colour ne domin bai fiye amfani da Abu gama gari ba.

A nutse ya futo hannunshi rike da wayoyin shi, kana kallonsa zaka fuskanci akwai damuwa a tattare dashi Dan dai jarumin namiji ne me b'oye damuwar sa. Harabar gidan ya futa, Doh-doh da Rambow suna tsaye kamar dogarai suna ganinshi ya futo Rambo ya nufi inda yake shi kuma doh-doh ya fara kokarin futo da mota.

Wayoyinsa ya karb'a yana yi masa barka fa futowa a dakile ya amsa masa ya wuce shi kuma ya bi bayan sa, motar ya bude masa ya shiga ya zauna shi kuma ya zaga ya gurin zaman shi, motar ta futa daga gidan.

Sai da sukayi nisa sosai Doh-doh yace." Oga ina muka nufa."? Zaman shi ya gyara tare da Dan ya mutse fuskarsa yace." Muje gidan granny ko." Doh-doh yace." Angama sir."

Wayarsa guda ya karb'a gurin Rambo ya fara laluben numbar jiya yaji mugun haushi abunda tayi masa ta sanya Mimi ta kashe masa wayar wato bata buk'atar tayi magana dashi abunda yarinyar take ya soma b'ata masa rai, Sam bai saba ganin wannan shariyar ba a gurin 'yan matan da suke son shi, amma yana ganin dole zai rage zak'ewa a kanta ko zata gane muhumamcin sa.

Cikin ikon Allah da ya kira wayar itace ta dauka muryarsa shi a cunkushe ya amsa mata sallama minti biyu tsakani yace." Kina jina ko."?
"Umm." Abunda tace kenan. Yace." Munyi waya da dector d'azu an baku sallama shine na turo Doh-doh ya dauke ku a mota babu wata matsala ko."?
"Ummm."! Nace. Haushin yanda take masa yaji Umm da Umm sai kace wata kurma, k'aramin tsaki yaja yace." Yanzu zanje in dauko granny zata zo ta duba Momyna."
Sama-sama nace"Sai tazo." Kafin na an kara ya kashe wayar a fusace.! Tab'e bakina nayi nace "Kai ka sani kuma.

Umma na fad'awa zuwan kakar shi ta tashi ya fara shiri aunt Hauwa na shirin tafiya gida Umma ta hana ta wai ta tsaya su tab'i bak'uwa sosai a ka gyara gidan duk a ka kauda kayayyakin sana'ar Umma dasu ke rumfar tamu kamar su kalazinr galan din mai robibin magi da su d'aurikan busassan kayan miya rumfar tayi tas da ita Umma ta shimfid'a tabarma ta zauna jiran zuwan su.

Wani irin kamshi ne ya bugi hancin mu kafin muji muryar dattijiwar matar cike da nutsuwa da kamala tayi sallama.
Umma ta amsa mata tare da fadin"Sannu da zuwa maraba lale shigo ciki Hajiya."

Granny ta shiga ta zauna kan tabarma fuskarta cike da farin ciki da annushuwa, suka gaisa da Umma cikin mutumci, aunt Hauwa ta gaishe ta hade da dauko mata Lemo mai sanyi hade da ruwan roba Wanda aka siyo mata shi mussaman, Granny ta bude ruwan tasha tayi hamdala, sannan ta kalli Umma cikin barkwanci tace. " Nazo duba kishiyoyina ne, kafin a Kai min su mu fafata da juna."

Dariya Umma tayi tace." Aikuwa dai, dole suyi miki ladabi domin shi kanshi uban gayyar da bazar ki yake taka rawa ba a raba hanta da jini kuma da tsohuwar Zuma ake magani."

Dariya Granny ta sanya tace." Ai ya juya min baya kwana biyu baya ta tawa kullum bashi da zance sai na kishiyoyina kin ga kuwa dole inyi kishinsu." Umma tace"In ya gama d'akinsa ai dolen sa ya dawo gurin ki." Dariya suka yi a tare aunt Hauwa ta mike tare da fadin "Bari a kira miki su Ku gaisa wai kunyar ki suke ji."

Granny tace." Wane irin kunya? Suna jin dai tsoron su hada ido dani tun kafin su shiga humm zasu aure min miji ai dole su b'oye je ki kira wo mun su." Aunt Hauwa ta futa tana Dariya tare da mamakin halin grnay kamar sun saba mata Mai fuska da fara'a gaskiya tana da kirki.

Tun lokacin da naji sallamar matar gabana yake fad'uwa har yanzu narasa ko ta menene aunt ta shigo tare da fadin "Sai kuzo Ku gaisa da ita ko." Mimi tayi s'aurin mikewa tana gyara hijab dinta ko jira na bata yi ba tabi bayan aunt Hauwa cike da mamaki nake bin ta da kallo ina mugun mamakin azarb'ab'inta da rashin kawaici lallai Allah mai mutane sai ga mutum yana Abu shi a ganinsa ba komai bane.

Muryar Umma naji tana k'wala min kira na amsa da sauri na dauki zurmemam hijabi na sanya na futa da sauri Mimi na zaune kusa da ita sai faman sunkuyar da kanta take tana murmushi nayi sallama granny ta daga kanta tana kallon Asma'u fuskar ka a sake tace" Zo nan kema ki zauna mu fahimci juna daku domin bana don Ku kwace min mijina."

Babu yabo babu fallasa naje na zauna kusa Da ita kaina a kasa na gaishe ta, ta shafa kaina tana fadin"Sannu Asma'u d'iyar arziki Allah yayi muku albarka gaba ki d'ayan Ku, Allah ya baku hakuri. Zama da juna kuyi ta hakuri da Mijinku domin wani irin mutum ne shi muskili kuyi hakuri da dabiun shi, gaku 'yan gida daya nasan baza a samu wata Matsalar ba ta fannin kishi tunda 'yan uwan junane Ku, Ku rike junanku da amana kunji ko Allah yayi muku albarka."

*12/November/2019*
[11/13, 7:59 PM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*

*MALLAKAR_ BINTA UMAR*

*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI*

*50*

Umma tace." Ameen suma ameen Hajiya ki kwantar da hankalin ki insha Allahu babu wata b'araka da taza faru a tsakaninsu zasu zauna lafiya tunda Allah yasa sun hada miji gasu kuma 'yan juna, komai zai zo da sauki. "

Granny tace." Masha Allahu to Allah ya tabbatar mana da alkairinsa, hira tsakanin Umma da granny ta mik'a sosai ba tare da sun gane ba, ni bar dakin cike da kunya, Sai ga Mimi ta biyo bayana kwanciya tayi kusa dani hade da lumshe idonta, murmushi nayi ina kallonta cikin tsokana nace." Mimi amaryar Amjadu Alherin Allah."
Chapter 24 · 0% Book details