← Book details Babban Yaro Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 60

Sashe 31

Babban Yaro Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

****
To muma namu b'angaran haka take mun shirya sosai ko wacce ta k'ure kwalliyar ta, ni da Mimi kayan mu iri d'aya, cikin Wanda ya aiko Rambo dasu ne jiya muka dauki wani masifaffan les ruwan Zuma, anyi mishi wani irin dinki mai tutoci gaba da baya dinki Riga da siket ne rigar kuma bata da girma babu abunda yafi burge ni da dinki sai yanda aka kaya ta hannun rigar d'aya dogone d'aya kuma gajere gajeran anyi masa wani falmaran a saman sa cif rigar tayi min amma duk da haka saman k'irjina sai da suka futo k'aida ne dama indai zan sanya Riga pitatd to sai saman nonuwana sun futo har tsagar su, saboda Allah yayi min baiwar su, sai nayi amfani da gyale mai Dan fad'i inda na samu ya rufe min mazaunai na, amma yana da sharara dole sai an ga komai nawa, hakan ma dai dashi gwara babu, ni kuma bazan yi kwalliya ta in sanya babban mayafi ba.
Mimi kam net ta sanya kamar yanda amare suke yi muka futo waje muna ta d'aukar hoto, wayar na hannuna naga kira, shine na daga kaina ina Neman Mimi tana can suna hoto, a dake na daga wayar nayi sallama.

Zuciyarsa yaji dam!! Jin muryar ta, dake namiji ne sai ya maze cikin wata 'yar iskar murya yace." Mommahh ga motoci nan sun tawo d'aukar Ku, na k'agu naga fuskar ki, wallahi naji k'amshin ki, humm! Ina fatan zan same ki, a yanda nake tsammani, sai kunzo."! Kashe wayar yayi ba tare da ya bari tace komai ba, ya maida ita aljihunsa, ya cigaba da sabgar shi da jama'a.

Saroro nayi da waya a hannuna gwiwa tayi sanyi sai naji duk wani karsashi da kuzari na, yayi kasa, tunanin guy nake, dama can yana son Mimi Ashe yake pretending ko kuma yanzu ya fara sonta, ni dai tunda nake dashi ban tab'a jinshi da irin wannan muryar ba, gashi yana fad'a mata kalamai na so, zuciyata ta shiga zullumi da wasi-wasi, gashi tayi min wani nauyi ina jin bakin ciki a cikinta da kyar na dai-dai ta kaina na shiga cikin jama'a muka cigaba da hoto amma lokaci lokaci sai inji fad'uwar gaba idan na tuno guy din.

Motoci uku ya turo masu zafi dama ba mu fi mu bakwai ba, muka shiga sai Jan bolo gurin parking motocin suka k'arasa da mu sannan ko wacce ta futo, haske ko ina da ina kamar rana ga wasu manya manyan motoci a fake a gurin, k'amshin turare kuwa na wannan yana wane wancan, can hango shi ya tawo abokanshi biyu a bayan shi, gabana ya dinga bugawa tun kafin su k'araso nake kokarin nemo jarumta ta tana guduwa yayi min masifar kyau! Farin mutum cikin bak'aken kaya, sai ya zama kamar wani tauraro cikin abokan nasa abun mamaki tunda ga nesa nake hango wani kwantaccan murmushi k'ayattace a fuskar sa, Suna karasowa gurin ya rike hannun Mimi tuni abokan shi da masu d'aukar hoto suka fara aikin su, suka fara tafiya mukuma muka rufa musu baya, na lura bani kadai ce na shiga halin d'imuwa ba har da k'awayemu suma duk jikinsu yayi sanyi ganinshi narasa me yasa yake wa mutane kwarjini haka,mussaman mata.
Addu'ar Neman
nake cikin zuciyata, *"Wallahu galibun ala'amri."* wannan addu'ar nake yi cikin zuciyata domin ina ganin zuciyata zata iya tona mun asiri, a gurin, shiyasa na dauki alk'awarin bazan k'ara kallon inda yake ba, suna. Tafiya ana musu vedio da hotona har suka Isa gurin zaman su, muma muka samu guri muka zauna, sannan guri yayi shiru mai gabatar wa ya tashi ya gabatar da malamin da zai fad'a kar kam zaman aure da abunda auran ya kunsa
Wa'azi yayi kyau kuma ya fad'ar kar sosai bayan ya gama. Masu rabo suka shigo suka fara raba wasu manya-manyan ledoji komai cikin nutsuwa akeyin shi, ko da wasa naki kallon inda suke zaune, hira ma muke yi da Maryam tana k'ara fada min Yanda Mimi tayi dace da miji tana fadin"Dole sai tayi da gaske domin akwai 'yan matan shi da suka d'aura arinyar akanta mussaman Alina." Nace"Dole kuwa Alina kinga ko zuwa bata yi ba." Maryam tace"Yaushe zata zo matar da tunda taji abun take tada Aljanu." Dariya nasa Ina rufe fuskata da hannuna kawai sai naga hasken flash dago kaina nayi da sauri, naga d'aya daga cikin abokan shi Wanda suka sanya kaya iri daya yana tsaye a kanmu nida Maryam sai daukarmu a hoto yake mussaman ni. Bata fuska nayi ina kallon shi, murmushi ya sakar min, tare da kashe min ido daya. Dauke kaina nayi ina Jan tsaki k'asa-k'asa. Gurin ya bari yana duba wayar shi, hotona yake dubawa

Duk abunda yake faruwa tsakanin Mujahid da Asma'u a kan idonshi, yasan halin Mujahid akwai son matan tsiya gashi dai da auran shi, amma in yaga mata jikinsa har tsuma yake, yaji wani iri a zuciyarsa amma kallon da yaga Asma'u na watsa ma Mujahid din ya ji dad'i a zuciyarsa yace." Mata masu daraja kenan."

Mik'ewa nayi daga gurin ina waige-waige Su Munnu na can baya an had'u da samari ana hira da ciye-ciye ganin na mike yasa Maryam mik'ewa muka fara ratsa jama'a tafiya zamu yi tunda dai an gama ango ya kawo amaryar sa gida domin na tsani kallon da maza suke min. Aikuwa ido yayi caaaaa! A kanmu ni kaina a jikina nasan kallona ake yi, cikin sauri sauri nake tafiya inda sassaan jikina yake motsawa, sai tsaki nake.

Amjadu kuwa tun lokacin da ta mike tsaye ya karewa jikinta kallo kuma yaga yanda shatin jikinta ya futo ta cikin sharara din mayafin ta, sai yaji kamar ana soka masa kibiya a kahon zuciyarsa, mussaman. Yanda yaga maza da dama sun raja'a a kanta, gumi ya tsinke masa, lips d'insa ya tura a baki yana ji kamar ya hadiyi zuciyarsa ya huta da wannan bakin ci, Mimi ya kalla a sace ya ga Sam ita babu wani abun assha da dinkin ya futo mata dashi, ya rasa wace iri ce Asma'u me karuwan jiki, ko wane irin kaya tasa sai sun tona mata asirin jiki. Innalillahi wa'inna'ilah raji'un. " shine abunda yake nanatawa cikin zuciyarsa ko ya samu sassauci.

Ganin duk sun mike ne suna kokarin futa daga gate sai hakan yayi masa dad'i mutuka wayar sa ya dauka yana kiran Rambo yace." Maza'a maida su gida shi da kansa zai kawo Mimi gida aikuwa haka aka yi, muna kokarin shiga mota ne sai ga Muhajid ya k'araso gurin, hade da kure ni da ido yana sakin wani murmushi, yace." Asma'u." Nayi mamakin yanda ya San sunana haka, babu yabo babu fallasa nace." Na'am ya kake."?
Murmushi yayi Wanda na lura hakan d'abiar shi yace." Lafiya amma ba Lou ba, tunda na ganki na rikice na gigice na dimauce na rasa nutsuwa ta, Asma'u ina kaunar ki fisabillah." Ya k'arashe maganar sa har da kwantar da kansa, Su Munnu kuwa dariya suke masa, yace." Ina da mata da yara biyu ni ma'aikacin lafiya ne, ina aiki a nasarawa hospital ina fata zaki so ni kar kice na miki tsufa." Yanayin barkwancin sa da yanda yake da sakin fuska da wasa da dariya yasa na saki fuskata nace"Ashe dai ka sani ni kam kayi min tsufa bazan auri me mata ba." Marairaice fuska yayi hade da fadin "Don Allah kinji. " sai na tsinci kaina da sakin dariya har fararen hak'ura na suka bayyana Wanda yayi dai-dai da zuwan Amjadu gurin Hannunshi rike da na Mimi, ina ganinshi na dauke kaina da sauri gaba na lugude, ko kallonmu bai yi ba nida Mujahid ya fara magana dasu Rambo Wanda suke kokarin saka mutane a mota, Ina jin Mujahid nace "Aboki nifa nayi mata a gurin nan gaskiya naji dadin wannan ranar wallahi na tsinci dami a kala."
Babu yabo babu fallasa ya kallemu dani dashi yayi wani killer smile As'usuel ya sosa kanshi tare da fadin"Kayi dace Aboki amma bakayi gaggawa ba, kuwa." Mujahid yasa dariya tare da fadin" Wane irin gaggawa kuma in tsaya kallon ruwa kwad'o yayi min k'afa."
Kamar babu abunda yaje damunsa ya sanya dariya tare da fad'in"OK ni babu ruwana wallahi kai da Madam."! Mujahid din yace." Shareta ai ba da ita kadai zan zauna ba." Shiru yayi masa ya cigaba da magana da Rambo, ko da wasa ban kalli shi ba sai ma sauri da nayi na bude motar na shiga.

Ina kallonshi ya rungume kafad'un Mimi a jikinshi lokaci-lokaci yana sumbatar goshin ta, hade da yi mata magana k'asa-k'asa, da sauri na kauda kaina dama tsautsayi ne yasa na kalleshi, Yanzu kuwa Allah Allah nake motar ta tashi mubar gurin.

*16/November/2019*
[11/17, 1:56 PM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*

*MALLAKAR_ BINTA UMAR*

*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI*

*54*
Chapter 31 · 0% Book details