Sashe 39
Babban Yaro Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mimi na sanya tayi wanka ta gyara jikinta tsaf! Nima nayi wanka ban yi wata kwalliya ba, na sanya atamfar mu ta anko Candy mu, ina kokarin zama kusa da ita tace." Asma'u ya kamata a shirya masa abunci ko."? Kallonta nayi na minti biyu kana nace"Kina da tabbacin zai ci abincin idan ka shirya masa nifa bana son wulakanci domin yanzu ma na had'a kayana tsaf! Zan tafi inda nafi wayo."
Marairaice fuska tayi tace"Don Allah kar ki tafi yau kinji ki bari na warware tukkuna." Tsaki naja tare da fad'in "Kinsan inuwarmu bata had'uwa guri guda dashi, bana son abun bata rai." Tace" Ki rabu dashi don Allah duk abunda zai miki."
Shiru nayi kawai, Granny ta futo daga d'akinta da carbi a hannunta ta idar da sallahr la'asar, ta kalli Mimi sai ta saki dariya tana zama kan kujera tace." Wato da kika ji Mijin ki na kan hanya kinyi wanka tsaf har da kwalliyar fuska." Dariya nayi kadan nace"Dole tayi kar taje ki kwace mata gakinan kin rambad'a kwalli har da sabuwar atamfa." Granny tace"Sai kiyi kuma komai abunki bazan baki kwallina ba."
Dariya nayi nace"Ni ba kwalli nake so ba ki bani lallai me ja irin na k'afafunki."
Kallon k'afar tata tayi tace." Yana gidana nima Iyami ce ta kawo min daga garinsu, duk sanda zata zo gidanan zan ce ta Zo miki dashi."
Nace"Yawwa granny ko yanzu ma a kira ta a waya ai tana da waya ko?"?
Granny tace"Tana da waya to wai ke meye kika damu da kunshi sai kace wata me miji, ki bari mu masu miji muyi."
Dariya ta bani sosai nake yi nace"Ni ko nake da miji a hannu kin San shi don kullum yana zuwa gaishe k.............Kafin in karasa ya shigo parlor tuni k'amshin turaran sa, ya mamaye parlor. Yana sanya da Riga shart fara tas tana da gaje ran hannu, wando jikinsa jins ne blue ya sanya fencing cap (hana sallah) idanunsa sake da bakin glass wuyan shi wata siririyar sark'e ce silver sai shek'i take, hakama a gogon hannun Shi, shi kanshi blet din da yayi amfani dashi abun kallo ne kafin kazo kan takalmin k'afar shi, booth mai igiyoyi blue colour in da kasan bature haka ya koma.
Duk zancan da Asma'u suke da granny a kunne shi.
Fuskarsa murtuk! Ya tsaya bakin kofa, yana karb'ar wayoyin shi daga hannun Rambo
Granny ta washe baki tana fad'in"Oyoyo angon karni ya dawo sannu da zuwa angon Aishatu sannu da zuwa."! Mik'ewa tayi karasa bakin kofar sai washe baki take, fuskarsa ya saki kad'an ganin kakar tashi ya rungomta jikinsa hade da sumbatar goshin ta yana fadin"Granny na same Ku lafiya."? A sake tace." Lafiya ba lafiya gaskiya amma shige ka huta tukkuna."
Hannunta ya rik'o suka k'araso parlor, ina kallon Mimi ta yunk'ura ta mike tsaye ta nufi inda suke, sakin Granny yayi ya kamo ta ya rungume ta hadda lumshe ido! Kauda kaina nayi da sauri ina da na sanin zama na a gurin.
Fuskar ta ya d'ago da hannunshi yace." Momyna haka kika koma."!? Mimi ta fara k'walla, saurin rungume ta yayi yana Dan dukan bayan ta kad'an cikin sigar rarrashi yace." Sorry baby na ya taso ki a gaba kiyi hakuri insa Allahu zaki warware."
Kungunta ya riko har suka k'araso tsakiyar parlor.
Ya kalleni a d'age. Nima na kalle shi babu yabo babu fallasa.
Wuce wa yake kokarin yi, granny tace "Zaka wuce baku gaisa da Asma'u ba, yarinya hazika kuma jajurtacciya ta tsaya kan matarka sosai, gaskiya samun me zumuncin ta sai an tona."
Babu yabo babu fallasa tace." Granny na ganta ai ni da ita waye zai fara gaida wani ko banza na girme ta nesa ba kusa ba, bayan haka kuma a gidana take dole ta girmama ni."
Tsaki granny Taja tana fadin"kai dad'i na da kai kenan,son girma kowa ai da irin tashi fahimtar ko kaga ka wuce bata gaishe ka ba."
Fuskata na saki don kar in kunya ta granny nace"Sannu da zuwa ka dawo Lafiya. "? A fakaice ya kalle ta, yayi saurin dauke kansa, jin muryar ta ya tayar masa da abubuwa da dama, yana tafiya yace." Lafiya k'alau na dawo."
Bedroom d'insa ya shige da Mimi rungume a jikin sa.
Wanka ya shiga ya futo Mimi na kwance kan bed ya kalleta cike da tausayi ya dawo da matsananciyar sha'awa babu hali domin akwai rashin imani ya kusanci Mimi duba da halin da take ciki.
Sabbin kaya ya sanya ya shirya tsaf dashi kana ya zauna kusa da ita.
Mik'ewa tayi zaune cikin kasala, shi kuma ya tsira mata idonsa.
A hankali yace." Momy kin rame sosai laulayi ya sanya ki a gaba ko." ? Mimi tace." In laulayi ne kadai da sauk'i kullum da daddare fa bana iya bacci ciwon ciki, Dr Mujahid ne a tsaye a kaina sai Asma'u, domun ta dalilinsa take zaune a gidanan tunda shi ya tursasa ta, yana da kirki wallahi, kusan kullum sai ya shigo ya duba ni."
Fuskarsa ya kirne! Kamar bai tab'a Dariya ba yace." Kina so kice min kun karya mun doka ke da Asma'u, bana nan kuna shigo mun da k'ato cikin gida. "!?
Mimi ta tsorata ganin yanda yake zare mata idonsa.
Tsawa ya buga mata tare da fadin" Kinyi shuru ki bani amsa ta."
Gyada kanta tayi tace." Tun ranar ya ganmu zamu hospital shine ya dauke mu a mota can asibitin su ya akaimu shine ya sanya akai min duk wasu gwaje-gwaje."
Mik'ewa yayi tsaye da sauri ya nuna ta da hannu Cikin daga murya yace." Da kika kirani a waya me na fada miki."?
Mimi tayi shiru gabanta sai fad'uwa yake yi.
Ni da granny duk muna jiyo hayaniyar shi, yace." Ko ba cewa nayi dake kar Ki sake ki bi ra'ayin wancan yarinyar ba, wato ni ban Isa dake ba kenan , in banda lalacewa da kudina da komai Ku shigo mun da wani banza cikin gidana bayan bananan, me hakan yake nufi."!!? Mimi har ta fara kuka tana bashi hakuri
Cikin banbami masifa ya cigaba da cewa" Nace dake akwai kudi a dakina ku yi amfani da ko nawa ne, shine zaku zumar mun da mutumci, ni d'an maula ne."!? Ya fada da wata irin tsawa.!
Mamaki ya kamani jin wata irin magana tana futowa daga bakinsa, dama alkairi yana koma wa sharri ? Me ya kawo maula cikin taimako na tabbata Mujahid bada wata NIYYA ya taimake Mimi ba sai dai hakkin makota ka.
Shashshekar kukan Mimi muka ji nida granny sai hakuri take bashi shi kuma yana kara fusata sai hayaniya yake mata cike da rashin tausayi.
Cike da b'acin rai granny ta mike tana fadin"Wannan rashin hakuri dame yayi kama? Daga zuwan ka, ka fara fad'a ki tausayi babu, wato kai duk irin abun da akai maka na taimako baka gani."
Dakin ta bude ta shiga tana cigaba da fad'an ta.
Mimi tace"Don Allah kayi hakuri wallahi ba laifi na bane."
Da sauri yace." Dama nasan ba laifin ki bane nasan me zuga ki, duk abunda kike yi tunda da kunne na naji."
Granny tace"Kai ko daga dawo wa zaka soma tashin hankali ka duba halin da take ci ki mana, kila da bama gidan dukan ta zaka yi ko."? Ranshi a bace Yace. " granny a gaban ki ake shigo min da namiji gida bananan,duk da cewa makoci na ne, amma shigowar shi cikin gidana bashi da wani amfani mutukar bani na kawo shi ba, kuma nasan dalilin da yake kawo shi gidana,kune kuke ganin taimako ne yake kawo shi ni za'a rainawa hankali."!
Ya k'arashe maganar sa cikin hayaniya.
Duk ina jinsa, a zuciya ta nace"Ikon Allah daga taimako ya koma tashin hankali, mik'ewa nayi da sauri na nufi bedroom din Mimi domin in fara had'a kayana zama bai ganni ba.
Granny rarrashin Mimi take sosai ganin yanda take wani irin haki! Ya tsorata sosai, ta zauna kusa da ita tana fadin "Kiyi hakuri ki daina kuka shi namiji ba'ayi masa haka, kinga yanzu kin nuna masa langon ki." Ita dai Mimi hawaye kawai take sharewa tana mamakin jarabar mijin nata .
Shi kam Amjad tuni ya bar dakin. Ko da ya futo yaso ya samu Asma'u a zaune ya wanke ta tas sai yaga bata gurin, k'wafa yayi a fili yace."Zamu hadu dake kema."
Parlor ya zauna hade da Dora kafa daya kan daya ya k'urawa TV ido sai faman huci yake.
Futowa nayi daga bedroom din bayan na gama hada kayana,kawai na ganshi zaune da har zan koma ciki kawai na dake sosai Nazo na gifta shi zan nufi kicin, k'afar shi ya sanya ya tad'o tata cike da mugunta
Taga-taga nayi zan fad'i da sauri na rike hannun kujera, sai ya sanya hannunsa guda da k'arfi ya buge min hannuna na fad'a jikinsa kaina ya daki k'irjinsa.
Kafin inyi wani yunkuri ya ture ni daga jikinsa hade da Jan tsaki, yana min wani irin kallo.
Kamar zan fashe da kuka na mike tsaye hade da d'aukar dankwalina da ya cire na d'aura.
Murya na rawa nace"Allah ya Isa wallahi."
Zuba min ido yayi yana kallona.
K'irjina nayi saurin kalla ganin shi yake kallo, saman breast dina duk sun futo dama kaida ne hakan.
Tsaki naja nace"Iskanci a cikin gidan aure Allah ya raba mu da irin auran wannan mazan." Kicin din na wuce da sauri ina hard'ewa nasan kallona yake yi.
Dauke kansa yayi bayan shigowar ta har yanzu ya rasa wane irin hukunci zai yi ma yarinyar .
Tsayuwa nayi tsakiyar kicin din ina tunanin abunda ya kawo ni, minti biyu na tuna Mimi nake so inyi wa miyar ogon da hanta, kullum nake mata taci da bread ko gurasa domin su kadai take iya ci,sai wainar fulawa, gurara sa, Mujahid ne yake jigilar kawo mata, in bashi ba, Umma ta aiko mata.
Cikin sauri na fara had'a abun bukata, Allah-Allah nake in gama in bar gidan.
Ina tsaka da Yanka hanta ya fad'o kicin din.
Saboda tsoro saura kadan in yanke hannuna. Jarumta na aro na daure fuska ta tamau.!