Sashe 9
Auren Wucin Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
amma ina kara miki nasiha daki lura da kanki kada ki tsaya sauraran maza a layi duk da nasan ba halin ki bane amma wannan nasiha ce da tunatarwa" abba ya fada. Jameela tace: nagode abba zanyi yadda kace, insha allah. Sai ya dauko wandon jamfansa daya rataye ya ciro dari biyar ya bata yace: kiyi kudin mashin! Tana karba sai tace: abba yayi yawa! yace: baiyi ba zaki iya ganin wani abu ai ki saya. Jameela tayi ta godiya, a lokacin ne umma ta shigo daki tace: ke kuma godiyan meye kike yi ? Tace: umma ina sone zanje gidan ikilima shine abba ya ban kudin mashin nake masa godiya. "Aiho wato ni bazaki tambaye ni ba saboda kina ganin bani da kudin da zan baki ko ?" Umma ta fada. Tace: haba umma na aike ba sai na fada miki ba, ai idan na fadawa abba ai na fada miki ne dan dake dashi kunfi kusa. Tana fadar haka kuwa ta ruga da gudu. Umma ta bita kamar zata mata duka tana mai cewa: jairar maras kunya. Abba ma dariyar kawai yake yi tun da yaga an amfara wannan muhawarar. *** **** *** Da kusan misalin karfe tara da rabi jamela ta gama shiryawa inda ta wata atamfa mai ja da kalan kore ta dauko babban mayafin ta ta yafa ta feshe kanta da turarurruka na musamman bakaken takalma tasa wadanda ba masu tudu sosai bane, ta shafa jambakin nan blue kamar ta shafa laka a akin ta kara jan giranta na ta sanya eyes shadow amma ta yadda baza kasan ta saka ba sai dai idan ka mata kallon kwarilla, rataye take da jakarta baka kalar takalminta, zaka iya rantsewa da allah akan cewa jameela ba bazawara bace, saboda yadda kyanta ya kara fitowa fili duk da ramar da tayi na saboda yawan tunanin mijinta sulaiman. tana fitowa sai yusra tace: yanzu adda bazaki tafi dani ba? "Ki bari sai watarana amma yanzu idan mun tafi wazai taya umma aiki da sauran aika" jameela ce ta fada. Yusra tace: to sai kin dawo ko gaishe da anty ikilima! "Zataji" ta fada ta fita ta samu umma a tsakar gida ta tsotstsoka neta sosai sannan ta tafi. Ai kuwa tayi sa'a tana zuwa bakin titi taga mai napep ta masa kwatancen inda zai kaita a unguwar tudun wada take kuwa ya gane gurin, yace: 100 zaki biya. "Allah ya kaimu lafiya" ta fada sannan ta shiga gidan baya ta nitsu sai kawai tunano tsohuwar rayuwar soyayyar da sukayi da masoyinta mijinta sulaiman tun kafun auren su. Ba tayi aune ba kawai sai ta jin hawaye yana zuba a idonta, sai ta ciro handkecip ta fara gogewa, shi kuma mai napep din ya lura kuma irin masu surutun nan ne yace: Haba hajiya yaya zaki sha kwalli kuma kina bata ta da hawaye ai sai kwalliyarki ta baci. "Babu komai" ta fada ne a daidai lokacin da aka iso kofar layin gidan sulaiman, Tace: anan ma ya isa idan ka samu guri. Haka kuwa akayi ta sallame shi ta juya. KASH MU HADU A PAGE 014 AUREN WUCIN GADI Page 014 Na Usman Umar Gombe (Babangida Ustazu) Call/WhatsApp 08137017208 I dedicated this page to Members Of [BUNDU WAILARU YOUTH DEVELOPMENT ASSOCIATION] (BYDA) (Bundu Wailaru Shamaki Gombe) DON MASU KARATU Imam Aliy bn AbiyDalib A.S Yace: ((Hankalin ka ya isheka hanyar da zai bayyana maka hanyar batan ka da shiriyar ka)) NAHJL BALAGHA J4 H416 A gefe guda kuma wani mutumi ne ya tsaya da alama gidan da yake arewa da gidan musa yake duba, tun lokacin daya ga jameela sai ya kura mata ido har ta fito daga napep, juyawan da zatayi sai taga ya kafa mata ido, tana sallamar mai napep sai taga mutumin nan bai kautar da idon sa ba akanta, sai tayi sauri ta shiga gidan musa dan har ta tsargu sosai. Sallama tayi ai kuwa kamar ana jiran ta caraf sai iklima ta amsa ta fito da gudu daga daki ta nufi kofar shigowa ai kuwa jameela ta gani ta shigo ta kama hannun ta suka nufi falo, meye jameela zata gani musa ne yake zaune akan kujerar 2siter mai fuskantar kofa, da alama shirin fita ma yayi. "Assalamu alaykum" jameela ta fada sannan ta shigo. "Wa'alaikumus salam" ya fada yana mai nuna farin ciki da zuwan ta. "Baban boy baka fita ba kenam" jameela ta fada cikin raha. Ikilma tace: Rabu dashi bashi da niyyar tafiya ne. "Aiho abun ma son jinsi ya dawo daga samun bakuwa sai ki fara nuna mini hali, ko bake bace kika ce na jira bakuwar ki mu gaisa ba" ya fada yana fada cikin raha da dariya. "Aiho ashe dai haka ne na manta" ikilma ta fada. Musa yace: ke kika sani dai yanzu kam. Tun da suka fara wannan muhawarar jameela ko hardewa tayi akan 1siter tayi tana murmushi a zuciyarta kuma tana jin inama da mijinta yana nan, kamar yadda suka saba zuwa tare, ikilima ce ta katseta daga wannan zancen zucin. "Kawata! kawata!! Kawata!!! Firgigit ta tashi kamar wance ta farka daga bacci. Musa ya dubeta cikin nutsuwa yace: haba jameela tunanin meye kike yi, irin wannan yawan tunanin yana iya jefa mutum cikin hatsari ko wani cuta fa! "Ba komai baban boy zan kiyaye" jameela ta fada a lokacin ta tuno ma ashe basu gaisa ba, ta gaishe shi ya ya amsa cikin fara'a da sakin fuska. Mamaki gaba daya ya cika ikilima ko magana bata yi sai da a zahiri a zuciyarta kuma cike take da tausayin jameela da halin da take ciki amma taki ta bayyana din ne dan kada jameela taki samun sukuni da sake jiki da ita tun da wuni tazo yi mata. "Meye zaki dafa mana yau ?" musa ne ya tambaya. Ikilima tace: haba baban sajjad bayan kuma ga mai girkin yau din ai ita zaka tambaya! "Zadai kuji dashi, tun da iyayi kuke so ku nuna mini" jameela ta fada tana dariya. "To nikan zan tafi, duk yadda kuka yi daidai ne kawai zan dawo around 2 inzo mu wuni da antyn sajjad dinmu" fada musa yayi yana dariya ya nufi hanyar ikilima ta bishi a baya suna tattaunawa kasa-kasa amma jameela ma batajin meye take fada, suka rabu ya dau mashin din sa ya buga ya tafi. A haka kuwa suka wuni cikin farin ciki da annashuwa haka nan sukayi Igga ikilima tayi musu da abun daya bawa jameela mamaki shine tanayin girke-girke kala-kala amma bata taba ganin anyi igga a gabanta ba, dan tun lokacin data kira shamsu almajiri ta aike shi ya sayo mata madara peak da tumatur da koren tattasai daman tana da fulawarta da dankalin hausawa da kwai da mai din suya. Jameela ta tambaye ta: yau kuma meye za'ayi da madara da tattasai da tumatur kuma. "Igga zanyi mana" "Meye kuma igga ?" "Sa ido ki gani!" A haka tayi ta taya ta aikin har akazo suya ta tsaya tana ganin al-ajabi har aka gama. Tana gamawa kuwa sai ta daura kus-kus kadan ta daura a wuta, har ta dafu suka ci abinci suka koshi daga nan jameela ta dauki hannu, shi kuma sajjad dan albarka ko kuka bayyi ba sai dai idan ya gaji yayi ta mutsu-mutsu sannan ta bashi nono hakan ba karamin burge jameela yake ba saboda har abada bata son yaro mai yawan kuka, can wajen kusan karfe 2 musa ya dawo ya gaji daga gurin aiki ya zauna yaci abincinsa ai kuwa sai ikilima tace: "Baban boy sai ka tashi ka mai data gida" "A'a ni bana son irin haka ita tace miki yanzu zata koma gida" ya fada yana mai kallon jameela. "Ai cemin tayi yanzu zata tafi tun da yanzu kusan 3o'clock kuma tace tacewa gida bazata kai 4 ba" Yace: jameela anyi haka! "Eh anyi haka" Haka kuwa akayi ba tare da bata wani lokaci ba ya dauke ta a mashin suna tafiya suna hira akan hanya har suka iso kofar gidan su ya sauke ta sannan tayi gaba ta shige gida shima ya bita a baya ya shiga suka gaggaisa da umma umma ta masa godiya ya juya ya tafi. *** **** *** Alhaji rabiu hamshaqin mai kudi ne wanda yake dillancin gidaje da filaye da gonaki, sannan kuma ya kafu a jahar gombe sosai, sai dai ko mutum ne mai yawan neman mata sosai wanda kowa ya shaide shi da hakan yana zaune ne a anguwar tumfure. Anyi masa tallan wani gida a anguwar tudun wada yaje zaiga wannan gida yana cikin kallon kuwa sai yayi arba da jameela ya fassarata a matsayin wata kyakyawar budurwa amma da alama bakuwa ce, nan take ya darsa a zuciyarsa cewa sai ya nemi yarinyar nan ko da kuwa da aure ne. INA MAI AMFANI DA WANNAN DAMAR WAJEN BAWA MASU KARATU HAKURI A BISA JINKIRIN CI GABA WANNAN LABARI, WASU ABUBUWA NE SUKA SHA MIN KAI NA MUSAMMAN KUMA INA FATAN ALLAH YA SHIGE MIN GABA A DUKKAN AL*AMURA NA DA DUKKAN MASU KARATU AMEEN NAGODE KASH MU HADU A PAGE 015 AUREN WUCIN GADI Page 015 Na Usman Umar Gombe (Babangida Ustazu) Call/WhatsApp 08137017208 Na Sadaukar Da Wannan Shafin Ne Ga Inna Na MAMAN ZAINAB (London Bayan Makarantar Kurame Gombe) DON MASU KARATU Manzon Allah S.A.W.A Yace: ((Ko wani mayaudari yana tutarsa -Ta Yaudara- Ranar Alkiyama)) SAHIHU MUSLIM H1735 "Da fatan alhaji kaga gida dai kam kuma ya maka" malam nura ya fadawa alhaji rabiu. "Eh naga gida kuma ya mini amma ta yamma da wannan gidan kan gidan waye ne? "Gida mai kofan karfe baki kenam ? "Eh shi dai" "Gidan wani matashi ne yanzu dayin aurensa kusan shekara daya da kusan rabi kuma shi daya ne da matarsa, To amma meye yasa kamin wannan tambayar kai da ba'a gidan zaka zauna ba? "Gaskiya jiya naga wata yarinya ce budurwa ta shiga gidan kuma har ga allah ina sonta da aure in har na samu dama" Haba alhaji rabiu sai kace ban sanka ba matanka fa yanzu uku, kace dai kana son kayi sha'ani da yar mutane kawai. "A'a ba haka bane gaskiya nake fada maka" Gaskiya bangane wace yarinya kake magana akai ba, amma sai dai in tuntu6a maka malam