Sashe 5
Auren Wucin Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sa'annin da kayi kana bacci" Ji yayi kamar a mafarki nan take ya tashi cikin nitsuwa ya fara gabatar da adduan tashi daga bacci, yana gamawa ya bita da salati, yana dubawa sai ya ganta a gabansa ya sun banci kumatunta sannan tace masa: are you ready to bath? "Yes dear" yace mata yana dariya. "To tashi kaje ko in daga ka in kaika!" Ta fada cikin raha. "Ke da bakya cin abinci ma yaushe zaki iya dagani" ya fada ya tashi ya nufi bathroom yana zuwa yaga ruwa mai dumi baiyi mamaki ba ya dauka ya fara wanka. Ita kuma sarkin ayyuka cikin kicin ta nufa ta ta shirya musu danwaken nan ta yanka musu koyi a sama ta sanya kabeji wanda tun jiya ta saye shi saboda tafiyan mai gidanta, ta kaishi dinning table ta ta shirya komai da duk abun da za'a bukata. Yana fitowa sai ya ganta tana tahowa yace: sarkin ayyuka sannunki ko? Ta amsa da yawaa ta dauko masa jallabiya cholate colour da wanda ta bashi ya saka ya koma ya dauro alwala ya tafi masallaci, dan a wannan lokacin wasu masallatan ma sun fara sallah. Nan take jameela taje tayi sallahn asuba a dakinta, tana idarwa sai tayi ta addu'o'i dabam-dabam akanta da mijinta musamman da takeji gabanta yana yawan faduwa daga ta tuno da tafiyar mijin nata duk da hakan yana faruwa take Uzbini (Auzubillahi...) da neman tsarin ubangiji. Komawa bathroom ta sakeyi ta cancara wani sabon wanka na musamman ta shirya tayi kwalliya na musamman dan raka maigidanta ai kuwa ta hadu dan a wannan wankan ne duk wasu rukunai na kyawunta suka kara bayyana ta wani kashe dauri ta ta dauko jakan da sulaiman zai tafi da ita ta kara kade masa ai kuma tana cikin wannan halin sai taji sallamar mijin nata sai kuwa ta amsa cikin kulawa. Cikin mamaki yace: wannan kwalliyan fa sai kace wacce zata raka wani gwamna? "Eh ai gwamna daman zan raka amma na cikin zuciyata" jameela tace. Yanzu kam sai kasa kayanka sannan muje mu karya ko? Yace duk yadda kika fada haka za'ayi. Ina so nayi amfani da wannan damar wajen mika gaisuwa ta musamman ga RUQAYYA ADAM Yar mutan Gusau Ki Huta Lafiya KASH MU HADU A PAGE 008 AUREN WUCIN GADI Page 008 Na Usman Umar Gombe (Babangida Ustazu) Call/WhatsApp 08137017208 Na Sadaukar Da Wannan Shafin Ne Ga M=Square Nice Guys Musa Lil-m Musa Yellow (Obidien) (Ceceniya Police Barrack Gombe) DON MASU KARATU Imam Baqeer A.S Yace: ((...Dukkan Komai -Na Addini- Yana Cikin Littafin Allah Da Sunnar Annabinsa)) USULUL MINAL KAAFI J1/62 Ai kuwa dauko masa wasu kaya tayi wasu kufta blue da aiki zubin hannu suma blue an masa shige da bakin, ta na mika masa yana shiryawa kuma tana ta bashi labarai irin nasu na masoya da suka gama shaquwa da juna yana gama shiryawa ta riqe hannunsa kamar wani jariri ko mai koyan tafiya ta kaishi bakin dinning table, ta zaunar dashi. "Ni yau ni zan baka abinci saboda ya zamo nina ciyar dakai kafun ka tafiya" jameela ce ta fada saboda tasan shi baya son ana bashi abinci kamar yaro karami. "Shikenam tun da babu yadda na iya" haka sulaiman ya fadi hakan kamar wanda akayi wani galaba akansa. "Hmm Muci kawai tun da baka so" ta fada tana mai bata rai. Sai sulaiman yace: aa haba dan allah meye na kukan kuma ? "Ni ba kuka nakeyi ba" ta fada tana mai basarwa. Yace: to kiban abincin mana haba wasa fa nake miki haba sahiba muddin kikayi fushi dani yanzu na dole in fasa tafiyar nan saboda ba zanje wata uwa duniya ki daura min tunanin ki ba, bakin ciki ya kashe ni a can! "Nina fada maka raina bai baci ba" tace. Yace: to idan haka ne ki bawa mijinki a baki, ta hakan ne kawai zan yarda ranki bai baci ba!? Matsowa tayi kusa da kurar da yake zaune ta bude ta gauraya masa gabansa kawai sai ta fara bashi, yakai loma daya sai yace: kefa ya bakya ci ? "Ni ai ina gidan! Kai kuma da zaka tafi ta yiwu ma duk abun da kaci kafun shiga ya zazzage! "A'a ban yarda ba kawai nima ki bani cokali ina baki a baki" Hakan kuwa akayi daga baya tana bashi yana bata suna ta tadin soyayya. Basu san lokacin da kowwanensu yaji ya koshi ba. Wayar sace tayi ringing yayin da wani zikiri na larabawa ya cika falon sai yace: "Abokin ne ya kira" Ya daga ya kara a kunnensa "Assalamu alaykum" sulaiman ya fada. Musa ya amsa masa sai yace "haba sarkin soyayya ayya kana son komawa kuwa? "To meye ka gani" sulaiman ya fada. "Naga baka neme ni bani yanzu har shida saura" Sulaiman yace: Haba nasan zaka zo ko ban kira kaba. "Sai ka fito mu tafi ai? sai sulaiman yace: ka shigo dai mu fita tare. : "To gani nan" yana kashe waya sai kawai yaji sallama nan take ya turo kofa ya shigo saka makon daman yana jiran zuwansa shi yasa bai ma kulle kofar shiga da kuma na falon ba. Cikin girmamawa sukai musabafa sulaiman ne ya fara mikawa musa hannu suka gaisa, sai jameela ta dan rusuna kadan tace: Baban boy ina kwana? "lafiya kalau" yace ya kuma amsa mata ne cikin kulawa da mutuntawa. "Bari na kawo mata break fast" jameela ce ta fada tana fadan hakan kuwa sai ta juya da nufin tayi cikin kicin. "Haba dan allah barshi ni ai bana karyawa sai 10" ki tambaye shi sai yayi nuni ga abokinsa. "To shikenam" ta fada daga nan ne sai sulaiman yace: mai sanyi zu ki zauna anan yayi nuni da wata 1 sitter sai yace: aboki na zauna kaima anan zamu yi wata magana yayi masa nuni da 2 sitter yana zama kuwa sai shima ya zo kusa dashi ya zauna. Sai yace: daman ina sone in tuna muku abun da kuka sani musamman ma ke jameela, kin ga yau zan tafi na fada miki zanyi iya kokari na nan 2weeks zan dawo amma dan allah idan na tafi a iya tsawon yadda na kasance acan duk abun da yake damun ki kada ki boye ki tambaye shi akan komai na rayuwa bani da kokonto akansa idan kina da damuwa idan har bazaki iya fada masa ba ga kawarki maman sajjad ki fada zata iya sanar mishi? Kaima abokina ga tanan sai yayi nuni da jameela yace: na baka amanarta ka kula da ita idan na tafi. Sai musa yayi dariya yace: Haba abokina wannan ai bana tsammanin sai kayi mana wani tunatarwa akai! "Ai kasan shi tunatarwa a har kullum yana amfanar mumini" inji sulaiman. Jameela kuwa tun daya fara wannan zancen nasa ita kuma sai ta rasa meye yake damun ta ita ji kawai take gaban ta yana faduwa ta kuma kasa iya riskar meye yake damun ta, hakan yasa bata iya cewa komai ba. Kawai ji tayi yace: sai ki tashi muje bakin terminus ko? Ko yau babu rakiyan ne? Musa ne ya fadi haka ai kuwa sai sulaiman ya amshe da cewa kai baka ga tayimin kwalliyan rakiya bane? Ai naga kamar tayi wani jugum-jugum ne ko kuma kin fara tunanin kewa ne tun kafun ya tafi ? Jameela tace: a'a haba sai kace yau ya fara tafiya? "Sai ku tashi muje ko dan yanzu haka 6 saura kadan" inji sulaiman. Jameela ce ta kulle gidan ta baya da kuba, a yayin da suka hau motar da musa ya dauko a gidan su sulaiman dan rakiya, sulaiman sai ya koma baya "haba abokina dawo gaba mana" inji Musa. Sai shi kuma yace: Idan na dawo gaba ita kuma matar tawa meye amfanin daukota kenam ? " Allah ya shiryeka dai" inji musa. Haka kuwa akayi musa na jan mota sulaiman da matarsa kuma suna ta hira irin na masoya da jinjina al-amarin rabuwar da zasuyi na sati biyu. Basu wani wuce dakika sha biyar ba sai gasu a cross din tsohuwar kasuwar gombe, musa baiyi wata-wata da suba ya shige cikin terminus ai kuwa sun isa da sa'a dan saura mutum daya ma motar ta cika nan take musa ya dauko kayan abokinsa da suke cikin karamar akwati ya kai masa but, a wannan lokacin ne aka rubuta masa rasit din biyan kudi take ya biya aka karbi number wayan abokin sa kamar yadda akan saba, karban numbern dan uwan mutum idan zaiyi tafiya. Haka ya shiga motar sukayi bankwana yana dagawa abokinsa da matarsa hannu har motar ta shi suka tafi. "To kema sai kizo mu wuce ko ? na kaiki gida" tace: to tazo ta har ta shiga baya sai yace mata waye drivernki dan allah ki dawo gaba! Tazo ta zauna da sulaiman ya lura kamar tana jin kadaici sai ya fara kawo mata labarai na gidan sa da sauran al-amuran rayuwa dan ya debe mata kewa. Amma duk da hakan kawai yake take masa dan babu yadda ta iya ji ya zama dole amma daya bari ma shi da yafi mata a hakan dai ya kaita har kofar gida sukayi bankwana shi kuma ya wuce gidan su sulaiman da yake jekadafari dan ya mayar da motar ya kuma dauko mashin dinsa daya barta a gidan. INA SAMUN KIRAYE-KIRAYEN JAMA'A A WAYA SABODA YAWA GASKIYA BAZAN IYA LISSAFO SUNAYEN SU BA AMMA SU SANI INA MUSU GODIYA INA SONSU DA FATAN ZASU NA MINI UZURI AKAN JINKIRIN FITOWAR RUBUTUTTUKA NA A KOWA CE RANA KAMAR YADDA NACE ZANYI NA GODE KASH MU HADU A PAGE 009 AUREN WUCIN GADI Page 009 Na Usman Umar Gombe (Babangida Ustazu) Call/WhatsApp 08137017208 Na Sadaukar Da Wannan Shafin Ne Ga Ummana Ta musamman INNA ALTINE (Maman Suhairat) (London Mai Dorawa Gombe) DON MASU KARATU Manzon Allah S.A.W.A Yace: ((Ya Aliyu Babu mai sonka sai mumini babu mai kinka sai munafuki)) RAWAHU MUSLIM Komawan jameela gida ya zame mata kawar wani shiga kurkuku taga gidan gaba daya ya mata dubu sai tunane-tunane take tana kwance ta rasa tayi da nayi, sai taji kawai zata kira sulaiman dan gobe tana so taje wuni gidan su ko zai rage mata kewa akan tsananin zullumi da take ciki, Ai kuwa sai ta kira