← Book details Auren Wucin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 10

Sashe 7

Auren Wucin Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

KASH MU HADU A 010
AUREN WUCIN GADI
Page 010
Na
Usman Umar Gombe
(Babangida Ustazu)
Call/WhatsApp
08137017208
Na Sadaukar Da Wannan Shafin Ne Ga Yayan
Anty LAMRATU M. LADAN wato
M. AUWAL M. LADAN
(YAYA AUWAL)
(Byee pass Gombe)
DON MASU KARATU
Khalifa Omar bn Alkhattab Yace: ((Kada Ku Tsarkake Ni Da Abun Da Bani Dashi))
WASAYA WA NASA'IHUS SALIHIYN 12
Jameela kuwa tun lokacin data kwanta bata tashi ba sai wajen hudu saura, tana tashin ne sai taji gabanta yana ta fadu, kuma sai taji kanta yana wani irin sarawa, tana duba agogon bango kuwa sai ta fara fadin ((Inna Lillahi Wa Inna Ilaihirrajiun)).
Nufin ta tashi ta daura alwala amma kuwa sai abun yaqi saboda ciwon kai din, sai tayi niyyar ta tashi tasha magani ai kuwa, kai kuwa a daddafe ta shiga cikin kicin ta bude Cooler irin yan madaidantan nan masu riqe zafi kadan ta sakawa kanta, sai taje ta ajiye akan dinning table sannan cikin karfin hali ta nufi bathroom taje ta dauro alwala, tana daukowa ta nufi daki inda first aid box yake ta dauko iya maganin da take tsammani zai sa taji sauki, ta nufi falo inda dinning table yake ta fara cin abincin bajin dadin abincin take ba amma haka take turawa dan ta samu maganin da zata sha ya tsaya a cikinta.
Abun da yake bata mamaki shine bata san dalilin yawan faduwar gaba wanda take yawan yi ba.
Da kamar kusan 5pm ta idar da sallolinta kawai sai mijinta ya fado mata a rai ta dauko waya ta kirashi shiru switch off kawai takeji sai tayi mamaki dan tasan ba halin sulaiman bane kashe waya, tunda tasan cewa wayar sa a cike take da caji kuma idan ta cika tana kaishi kwana biyu, kuma tasan yanzu ba lokacin sallah bane balle tace ko ya shiga sallah ne.
Watakila da yayi sallahr la'asar ne ya manta bai switch on na wayar ba.!
A haka ta tsaya ta da tunani taje ta kunna C.D Qira'a ta kunna na Alkhusary na suratul Maryama tana ji tana ta bibiya ko zata rage kuncin da yake damunta a cikin zuciya.
*** **** ****
Da asuban fari ne abba, musa da garba suka hau mota suka nufi hanyar bauchi musa ne yake musu Driving na motar amma baba yana baya garba kanin sulaiman yana gaba, tun bayan gaisuwan da akafi kafun a dau hanya babu wanda ya karayin magana ga dan uwansa, tafiya ta fara nisa a garin kashere suka ga ana ta shiga sallahr asuba abba yace: Su tsaya anan kasuwan suyi sallah sannan suci gaba da tafiya.
Hakan kuwa akayi suna tsaya ba tare da bata lokaci ba sukayi sallah suka daura tafiya ta alkaleri suka shiga.
Duk lokacin da suka hadu da road block abba ne yake musu magana da yake mutum ne mai cikar kamala hakan tasa basa bata musu lokaci, karfe takwas daidai sai ga su abba babban asibitin jahar bauchi nan take suka nufi fannin Emergency abba yana shiga sai yaje inda wata nurse take rubutu yace: madam barka da aiki ?
Tace: yawwa barka alhaji?
jiya ne akayi hatsari a mota daga gombe zuwa kaduna a gombe line amma sunyi hatsari a anan bauchi kuma nan akace an kawo su.
Tace: To ka duba duba kujerun waje zakaga wasu daga yan union ka tambaye su.
Nagode Abba ya fada ya juya su musa suna biye dashi a baya.
Yana fita sai yaga wasu mutum biyu da uniform na Yan union ya musu sallama suka amsa.
"Suna na alhaji muhammad deba nine mahaifin sulaiman wanda yana daya daga cikin wadanda suka taho a motar gombe line zuwa kaduna..." abba ya musu jawabi gamsheshshe Sai dayan yace muje ka duba shi suka shiga emergency abba yace a cikin duk wadanda aka kwantar babu shi.
To kenam yana cikin mutum hudun da suka rasa rayukansu a wannan hadari daya faru.
Musa yana jin haka ya fara fadin: Sulaiman ya rasu!!!
Yana fadan hakan sai ya wani mummunar hajijiya ta jashi nan take ya fadi yayi ta kuka mai tsuma ran duk mai sauraren sa, a lokacin ne garba ma ya durkusa yayi ta kuka sakamakon jin wannan labari mai mummmuna.
Yana kuka yana cewa: meye zan fadawa anty jameela idan ta tambaye ni akan yaya sulaiman, a lokacin da duk yan wannan gurin aka juyo da idanuwa kansu abba ne kadai baiyi kuka ba.
Yan union din suka cewa abba kaikam zaka iya komawa gida yanzu haka zamu wuce tare dashi da motar asibiti zuwa medical center gombe, a can zaku karbi gawarsa, abba yace dashi da waye suka rasu mutum hudun.
Suka ce masa: da driver ne da mace daya da maza biyu.
Abba ya juya kallonsa ga garba da sulaiman wayanda har a wannan lokacin basu daina kukan nan ba, abba ya fara rarrashinsu yana fadin: kuyi hakuri ubangijinsa ya fimu sonshi ya dauke shi, mu kuma mu masa fatan rahma da gafara ya jasu ya daura hannunsa akan kafadunsu kamar wasu kananan yara ya nufi bakin inda aka ake parking mototi.
Sai wani daga cikin yan union din da alama shine babbansu yace: alhaji idan ba damuwa na hadaku da wani mana yayi driving naku tunda shi drivern naku ma ga halin da yake ciki.
Babu ko musu abba ya amince.
sai ya juya ga daya daga cikinsu yace: Ya'u ka jasu kawai mu zamu taho a motar asibiti mu hadu kawai a can.
Nan take sukayi musayen
Number saboda idan sun iso medical center zasu iya kiran abba su sanar dashi.
Yau ya karbi mota da yake tsohon driver ne tafiya yake a titi cikin kwanciyar hankali kuma yake gudu basuyi awa daya ba kuwa sai wayar musa ta fara ringing.
Baiyi niyyar dauka bama sai yaji abba yace: ba kiran ake yi a wayan wani ba ya daga mana.
Ai kuwa yana duba numbern wanda yake kira, sunan JAMEELA Ya gani baro-baro a kan sensorn wayar ai kuwa sai ya kara rushewa da sabon kuka yana fadi: (Meye zan fadawa jameela akan sulaiman ta fahimta)
Sai abba ma yaji wani hawaye na tausayin jameela ya sirnano masa.
Ya ciro handkecip ya goge hawaye.
A lokacin wayar jameela ta katse.
Ko minti daya baiyi da katsewa ba, wayarsa ta kara daukan ringingtone abba yace: ka sakata a silent amma karka daga dan idan ka amsa zata iya fahimtar halin da ake ciki gwanda ka bari har sai mun koma gida daga baya kawai tasan komai zaifi.
Baza mu sanar da kowa ba sai mun koma gida.
Shi kansa dan union din sai da tausayi ya kama shi, shima yayi ta musu nasiha.
*** **** ***
Da kamar misalin karfe daya suka isa gida ai daman umman sulaiman tayi ta kiransa taji ya kashe tasan cewa akwai matsala, ai suna shiga gida sai jama'ar gidan yanayin sulaiman da garba ne ya fassara musu halin da ake ciki.
nan take Abba yace: To sai dai muyi hakuri sulaiman kam wanda yafi mu sonsa ya karbesa, Allah ya masa rasuwa sakamakon hatsarin da sukayi a wani jeji a garin bauchi.
Nan take gida ya hautsune da kuka ummansa daman tana cikin daki amma tana jin duk abun da yake fada, su kuma yaran gidan sai gidan ya gauraye da kuka da ihu, ihunsu har ya ankarar da yan unguwar halin da ake ciki inda suka ringa shigowa dan jin meye yake faruwa
Kafun kace meye labari ya karade anguwar gaba daya.
JAMA'A BA JAMEELA KADAI AKA YIWA RASHI BA NIMA ANTYNA #LAMRATU_M_LADAN TA RASU INA NEMAN ALLAH YA JIKANTA
KASH MU HADU A PAGE 011
AUREN WUCIN GADI
Page 011
Na
Usman Umar Gombe
(Babangida Ustazu)
Call/WhatsApp
08137017208
I dedicate this page to my heart desire Balkisu S.A Chilo
DON MASU KARATU
Imam Aliy bn AbiyDalib A.S Yace: ((Karanta Iyali Daya Ne, Daga Abubuwa Biyu Masu Sauki...))
NAHJL BALAGHA 4:564 H142
Jameela ta tashi ne a yau cikin wani irin yanayi na daya ciwon kai na biyu kuma ta kasa samun nitsuwa akan tana so taji shin mijinta ya isa lafiya ne, haka nan dai ta dafa indomie miemie guda biyu saboda ta karya, tana dafa abincin tana ta try na numbern sulaiman amma baya tafiya, gabanta sai kara faduwa yake amma ta kasa amintarwa da ranta ce cewa mijinta yana cikin wani hali ma balle ta darsa a ranta ya rasu ta dauko zata ci kuwa ai tana farawa kuwa sai taji bazata iya ci ba sakamakon yadda kirjinta yake bugawa.
Kawai sai ta ciro waya ta fara neman wayar musa akan ko yana da labarin abokinsa ya isa lafiya kuwa, haka kuwa akayi har sau biyu bai daga ba hakan yasa ta yanke shawarar ta kira iklima dan ta tambaye ta.
Har sai da ta kusa yankewa sannan sai iklima ta daga kamar ba komai.
Tace: Assalam kawata!
"Wa'alaikumus salam..."
Iklima tace: wato sai yau kika tuna dani ko? Ta fadi hakan amma tana ta kokarin boye abun da ta sani na rasuwar mijin nata!
Jameela tace: ai na kira baban boy bai daga ba har sau biyu nace to bari na kiraki ko zaki hadani dashi?
"Ayya ai ya tafi Bauchi yau da asuba amma yau zai dawo insha allah" inji iklima.
Jameela tace: ayya to kina da labarin ko jiya sulaiman yayi waya da baban boy?
"A'a wallahi bai fadamin ba amma dai yace min ya rakashi kuma ya kaiki gida daga baya" inji iklima.
Jameela tace: amma dai idan har kunyi waya ki tambaya min shi kice tun jiya bamu yi waya dashi ba amma yace masa ya kira ni.
"To shikenam sai anjima"
Bata bari ta bata amsar tambayarta ta ba, ta datse :wayan, hawaye ne ya cika idon iklima fal tana allah allah su karasa maganar saboda kar ta fara kuka ta fahimci akwai wani abu a kasa.
Haka nan dai kuwa ta fara tausayawa halin da jameela take ciki.
*** **** ***
Da kamar misalin karfe 1:40pm ne suka kira alhaji suka sanar dashi cewa an dauko gawarsu sulaiman da wadanda sukayi hatsari suka rasu tare yanzu haka suna Medical center gombe, zai iya zuwa su ganshi, nan take alhaji ya kira yace garba ya kira masa jameela a waya yana kiranta ya mika masa.
Ringing daya tayi jameela ta daga tace: Assalamu alaikum Garba.
"Bashi bane abbansa ne" abba ya fada.
Jameela tace: Abba ina wuni?
"Lafiya kalau jameela yanzu ina so kizo gida nan jekadafari ki same ni ina jiranki" abba ya fada.
Jameela tace: Abba lafiya kuwa?
"Lafiya kizo dai ki same ni" abba yana fadan haka ya kashe wayarsa nan.
Sai kawai ta fara cewa allah kasa dai ba wani abu bane ya samu sulaiman.
Da yake a lokacin tayi sallahn azahar kawai dauko hijabinta tayi ta sanya ta kulle gidan ai kuma da yake basu da tazara da titi sosai tana isowa bakin titi sai taga wani mai napep ta tare shi tace malam jekadafari zaka kaini yace: dari a hamsim zaki biya da yake tana sauri ko musu babu ta hau tun a keke napep din ta ciro dari biyu ta bashi yace: hajiya ba 50 naira fa.
Tace: babu komai ka rike kawai.
Yayi ta godiya da saka mata albarka.
Nan take suka iso gidan kawai fita tayi ko waiwayan mai napep din bata yiba, ta shiga gidan cikin gudu-gudu sauri-sauri ai tana shiga sai taga bakon yanayi sai ta hango garba da sulaiman suna zaune a gefe daya.
Ita kuma kanwar sulaiman wato khadija tana ganinta sai kawai ta rushe da sabon kuka sai sauran yan gidan suka dauka sashen matan ta nufa ta fuskanci inda khadija take.
Tace: khadija meye ya faru ki fadamin mana? Karki barni cikin rudu a lokacin ne umma ta jiyo sautinta daga daki sai ta fito, ta kama hannun jameela jameela abun da bata taba gani ba a rayuwarta da umma shine taga umma tana kuka, umma tace: jameela hakuri zamuyi allah yayiwa sulaiman rasuwa sunyi hatsari a hanya.
Nan take jameel
a taji duniyar na juyawa tace: a'a ba sulaiman dina baka, aa umma tana fadan haka ta sulale daga jikin umma ta fadi sumammiya.
*** **** ***
Duru-duru take gani tana bude idonta taga ashe ummanta ne a gefe kuma khadija ce, khadija tana ganin haka ta ruga da gudu tayi waje tana kiran yaya musa, basu dade ba kuwa sai gasu sun shigo tare, tace: musa ka fada min gaskiya wai da gaske ne mijina ya rasu ta fadi hakan ne cikin kuka mai tayar da hankalin mai saurare.
Shima kukan ne ya sake kama shi yace: jameela allah yayi wa sulaiman rasu yanzu haka gawarsa tana wannan asibitin ta fara kuka rikitar da mai saurare ummanta ta fara rarrashinta.
Nan take ta fara cewa ita kan sai an kaita taga mijinta, sukayi ta rarrashinta akan an rufe gurin sai gobe za'a masa sallah sai dai ta bari sai gobe, ana cikin hakan sai ga abbanta ya shigo, irin tsananin damuwar da take ciki yaki ya buya ga abban nata, shine yasa baki akan ta bari sai gobe kafun a masa sallah zata ganshi haka ta hakura tayi ta kuka khadija ma zama tayi a gefenta tana taya ta kukan dukka mutanen wannan dakin gaba daya hankalinsu ya koma ga su jameela kowa sai tausaya mata yake musamman idan sukaji watan ta shida da aure mijinta ya rasu.
Chapter 7 · 0% Book details