Sashe 4
Auren Wucin Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dilan manja a babbar kasuwar gombe ta bunkasa. Ya auro sa'adatu wacce yar ubangidan sace da yayi masa silan bunkasar kasuwancinsa, a shekarar daya auro tane matarsa ta farko ta sake haihuwa ya mace wacce taci sunan mahaifiyarsa wato khadija. Ana nan dai har sulaiman ya fara makaranta a jalowaziri primary school ya gama karatu har matakin NCE amma a gurin babansa yake zuwa yana taya shi aiyuka a shago shi kuma baban yana bashi wani abun kashewa kuma yana daukar nauyin karatunsa, Alakar musa da sulaiman ta faru ne tun suna makarantar kwana da sukayi tare a garin pindiga amma asalinsa dan tudun wadan gombe ne. A lokacin da musa ya tashi yin aure babban abokinsa shine sulaiman inda a wannan bikin ne allah ya hada jameela da sulaiman har maganar aure ta shiga tsakani. Iyayen jameela ba wasu masu hali bane sosai amma mahaifinta alhaji kabeer mai tireda ake ce masa yana manyan shaguna guda biyu a kasuwa na saida kayan masarufi, matarsa daya ita ce asma'u yayansu uku jameela suhaima ameer amma sun samu ratan shekaru a tsakaninsu sosai da addarsu jameela. Sulaiman ya samu aiki ne a hukumar wutan lantarki kuma yayi sa'a an dauke shine da takaddunsa na dan babban matsayi ma ya samu saboda yana da wanda ya wuce masa gaba. Daga fara aikin ne babansa ya saya masa gida akan yayi aure ya kawo matar nan daga baya idan yana da raayin zama acan ya iya gina musu gida a can ba musu kuwa ya yarda. Ya auri jameela auren ya tara jama'a sosai saboda har abokan aikinsa daga kaduna ma sun samu halarta auren jameela ya kafa tarihi wanda baza'a mance dashi ba a dawaki saboda daruruwan mutanen daya tara duk da cewa shi angon ba dan siyasa bane ko kuma hamshakin dan kasuwa. YAN UWA MASU KARATU INA DA WATA BUKATA TA MUSAMMAN KUMA TA ALKHAIRI A GURIN ALLAH INA FATA ZAKU TAYA NI ADDU'A AKAN ALLAH YA BIYA MIN BUKATATA! !! KASH MU HADU A PAGE 006 AUREN WUCIN GADI Page 006 Na Usman Umar Gombe (Babangida Ustazu) Call/WhatsApp 08137017208 Na Sadaukar Da Wannan Shafin Ne Ga Mai Gida Mal. Kabiru Keji Tela Gombe (KEJI BOOK SHOP) (Bakin Cross Tsohuwar kasuwar Gombe) DON MASU KARATU Imam Ja'afarus Sadiq A.S Yace: (( [[Duk Wanda Ya Kosar Da Makiyinmu-AhlulBayt- Hakika Ya Kashe Masoyinmu]] )) MA'ANIL AKBAR Murna ce ta kara zamowa biyu wanda a rana ta biyu wato ranar wuni matar musa ma ta haifa masa wani kyakyawan yaron gwanin ban shaawa, nan take kuwa ranar bakwai yaron yaci sunan Sajjad, bayan suna ne da jameela da sulaiman sukaje gidan musa sai tadi ya fara nisa lokacin tana riqe da yaron tace: baban boy wannan yaron wani irin suna ka sanya masa mun san dai akwai sajida mace amma ban san ana sanyawa namiji irin wannan suna ba ? Sai sulaiman yace: "ina ruwanki ko kuma so kike kiyi masa shishshigi ki bari mana kema idan kin samu naki kisa masa duk sunan da ki kaga ya fi miki ? "Aa haba aboki daga tambaya ai ni ta tambaya ka bari na bata amsa kawai" musa ne ya fada yana dariya. "Yanzu kam kai ka sani daka biye mata. sai ya fara da ce mata ai kinsan nana fadima tana da 'ya'ya guda uku ko? "Eh" tace. Kuma akwai sayyadina hassan da sayyadina hussaini wanda aka kashe a karbala. "Ni ban san wannan ba" jameela tace. Ya kamata koda wikipedia ki hau kiyi searching na wannan kisan, a takaice dai yana da yaro wanda shi daya ne ba'a kashe ba a inda aka kashe sayyadina hussain, to shi sunan yaron aliyu babansa kuma hussaini dan aliyu dan abiy dalib, to shine saboda tsabar yawan ibadarsa sai yan uwansa sharifai suke masa laqabi da Assajjad Ma'ana mai yawan Sujjada wato ibada kenam, Da fatan kin fahimta? "Na fahimci wani abu amma zan kara bibiyan wikipedia kamar yadda ka fada mini dan ina son ina sanin tarihin magabata" jameela ta fqda tana dariya. Suna isowa daf a zancen sai jaririn ya tashi yasa kuka kawai sai Iklima tace: bani dana dan baki san darajar shiba tunda baki haifa ba. "Eyey ba komai nima kwana nawa ne, ai kamar yau nima zanyi yaro kam" ta fada tana mika mata shi a lokacin sai ta juya ga sulaiman tace masa: "Ko ba haka bane angona" da alamar wasa. "Can ta matse muku keda kawarki..." "af yanzu fa tara tayi!" Inji sulaiman yana duba agogo "eh mana to sai meye, ko a daji kake" musa ya tambaya. Nan take iklima ta mikawa musa jariri tace masa bari mu shiga ciki mu tattauna da kawata, bata ko jira amsa ba ta ja hannun jameela uwar daki. "Mata mata mata Babu mai iya muku sai allah" sulaiman ne ya fada yana dariyar mamaki. Iklima taja jameela daki da dauko mata wasu turare na hayaki dana shafa irin nasu na mata a cikin abun da bai wuce dakika shabiyar ba ta kara koya mata wasu muamala na musamman da yadda ake tarairayar miji da salon kwanciya kala-kala. Anan ne ta fahimci cewa lallai wanda yayi gaba yayi gaba ne a harkar zaman aure. "Ke kam ki sake matar mutane mana haba kina ta mata musu lokaci..." taji muryan musa ne. "Gamu nan dai baban sajjad muna hanya, mun ma gama" iklima ta jawo jameela suka shigo falon. Tashi sukayi gabaki daya suka raka su har bakin inda motar da sulaiman ya karbu aro agurin babansa saboda yawon ziyara na musamman, a hakan sukayi ban kwana tare suka fito daga anguwar kasuwan mata suka wuce unguwansu na byefass. *** *** *** Haka dai rayuwa tayi ta dadi a tsawon hutun wata daya da sulaiman yake sun sha soyayya tare da matarsa na qin karawa kamar bazasu rabe ba, tun daren washe gari zai koma jameela ta shiga yi masa kuka akan kada ya tafi a lokacin da abun ya fara yaw ne sai ya kamota ya rumgumeta a jikinshi ta yadda suna iya jin numfashin juna. Yana cewa: " haba masoyiyata farin cikin raina abar alfaharina ki sani kece kadai a zuciya ta babu wata nima a gaskiya ban so ace nayi nisa dake ba, dan bani da wani buri da ya wuce na zauna tare dani kina shayar dani madara da zuma na soyayyarki, ban san wata 'ya mace ba bayan ke, ki yarda dani bazan kusanci wata ba bayan ke ki karfafai guiwa ta akan neman halal, ko so kike na ginawa wuta naman iyalina da wuta, ko so kike na daina" Nan take ta fara kuka tana cewa: fadin wallahi ni bana son inji kana kiran wuta dan wallahi bana son allah ka shiga wuta, amma muddin duk yadda rayuwa zatayi damu inaso ka kasance tare dani karka gujeni kada ka kini wallahi ina sonka irin son da uwa bata yiwu danta. KASH MU HADU PAGE 007 AUREN WUCIN GADI Page 007 Na Usman Umar Gombe (Babangida Ustazu) Call/WhatsApp 08137017208 Na Sadaukar Da Wannan Shafin Ne Ga Matasan Aduwa Sulaiman Terry-g (Dan Oga) Isa Shadulin (Isa Chairmo) Bunu (Baban Bariki) (Aduwa Biyu Kasuwan Mata Gombe) DON MASU KARATU Manzon Allah S.A.W.A Yace: ((Ku Sanyaya Abinci, Dan Babu Albarka A Cikin Zafin)) TIBBUN NABAWIY S11 To ki kwantar da hankalinki na ma fasa yin wata dayan sati biyu zanyi ko angama mana ko ba'a gama ba gwanda na kaiki can ko a wani gida mu zauna tun da bana tsammani za'a wuce wata daya za'a karasa aikin yana isowa nan ne a zancensa, sai jameela ta janye jikinta daga nashi ta fuskance shi da kyau ido sha6e-sha6e da haweye tace: kayi mini alkawari bazaka dade ba? "Eh nayi alkawari, amma kuma naga kamar baki yarda" ya fadi hakan ne a yayinda yake kura mata ido dan fassara sirrin zuciyarta. "Ta amsa na yarda mana Mai Sanyi na" A fannin jameela tana jin hakan amma ta kasa nitsuwa duk da cewa sulaiman bai taba mata karya ba a mu'amalarsu na zaman auren kai tun ma kafun ya aure ta. Da yaga kamar tana cikin kokonto sai shi kuma ya matse bai nuna mata ya fahimci hakan ba, sai ma kawai ya jawota jikinshi ya fara sarrafata da irin salon soyayyarsa na musamman ana haka har ta gama dauke wuta, har sukayi abunda sukayi bayan abun da ya faru ne ya samu tayi bacci shima ya kwanta maimakon yayi bacci sai yayi tunane-tunane akan yadda yake tausayawa matar tasa idan har baya nan duk da cewa baya zarginta kuma bai taba jin zata iya cin amanar saba duk da yadda take nuna tsananin damuwar ta akan tana rabanshi kusan kullum, a haka yayi ta irin wannan tunanin har sarkin barayin bauchi ya sace shi yayi sama dashi. *** *** *** Kiran asuban fari jameela ta tashi taje ta dauko heater ta daura musu ruwan zafi bai dauki wani tsawon lokaci ba ya tafasa ai kuwa nan take ta shiga tayi wanka tana fitowa kuwa sai ta jira ta tsantsame sannan ta nufi cikin kicin ta kunna gas cooker nan take ta debo fulawa gwangwami uku ta dauko kuka ta gauraya guri daya ai kuwa sai ta dauko ruwan kanwa wanda ta masa gora na musamman daman sai kawai ta saka ta fara gwabawa ai kuwa ruwa yana tafasa ta fara jefa danwake yan kanana, tana gama jefawa sai taje ta dauro alwala tayi sallah raka'a biyu na nafila, a karkashin zuciyarta kuma tunanin tafiyar mijin tane fall a zuciyarta data idar da sallahn sai tayi ta addu'a akan allah ya kaishi lafiya ya dawo lafiya. Ai kuwa da gudu-gudu sauri sauri taje ta samu har dan waken data daura ya dago sama alamar ya nuna kenam, saukewa tayi ta koma dakin ta samu mijinta yana ta bacci da yake yana fada mata idan ta riga shi tashin asuba ta tashe shi, ai kuwa tana zuwa ta haye kan gadon ta kwanta a kusa dashi a hankali ta daura bakinta a setin kunnensa sai ta fara hura masa iska a hankali, nan take sai ya canza numfashi sai ta kara kura masa ta yadda yafi na farkon sai take ce masa "mijina wannan shine kadai lokacin da zaka baiwa ubangijinka a cikin