Sashe 2
Auren Wucin Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mukabalar taku bari naje na dauro alwalah. Sai sukayi dariya dukkansu, sai musa yace: muje dai muyi tare zaifi dai ko ? Nan take suka tafi tare suka bar jameela ita kuma tana tunano zancen da musa ya fada mata, dan zancen ya kama hankalinta. Tana zaune sai taga sun fito suka nufi daki, basu wani dade wa ba suka gabatar da sallahr su ta magriba suka kuma hada dana isha, saboda shi sulaiman ya yarda da abokinsa sosai saboda yasan karatun da yayi na addini mai yawa ne, Idan yace masa abu ya halatta to zai aikata kanshi tsaye ba tambaya. Suna Fitowa daga uwar dakin ne sun nufi falo, sai kawai suka hango jameela ta fara bubbude kwanuka, Sai sulaiman yayiwa abokinsa musa rada da cewa bari na zolaye ta kadan, shikuma musa yayi kamar bai jiba. Cikin alamun ko inkula yace: wannan kuma meye kike yi haka ? tace cikin shagwaba: Abincin yallaboi ne. Yayi kamar bai gane ba yace: Waye kenam ? Cikin kwarin gwuiwa tace: kai mana! Yace: A'a Indai dan nine ki barshi kinganni nan mun biya gurin matar abokina ta hadadda mu da girki mai dan karen dadi. Tana jin haka sai ta fashe da kukan shagwaban nan tana cew: Wato shiyasa kaki ka dawo da wuri ko ? Sai Sulaiman yace: kin ganni nan wasa nakeAkafta Cikin kukan tace: babu wani wasa ai da bakayi da bazaka fada ba. Cikin muryar lallashi yace: haba mata ta tsokanarki nake yi, na ma isa nace wata ta fiki iya girki, hakan yaci gaba da lallashinta sai tadan sauko saboda musa yana nan, take ta sanya musu wannan abincin data dafa musu ta zuba masa shash kabab tunda tasan yana sonsa sosai, sannan ta sanyawa musa tace: Malam bari dai kuji yadda girkin namu yake tunda nasan yanzu kam kama fara mantawa da girki na. Sai musa yace: na isa ay nasan yadda kika iya hada girki amma na tabbata baki kai min maman sajjad ba. Sai jameela ta amsa cikin kukan shagwa ina ce kana jin abun da yake fada wai ban iya girki ba!? KASH MU HADU A PAGE 003 Zan Iya Samun Masu Tayani Murnar Ranar Haihuwata Kuwa a wannan Group Idan zaa samu To Akafta AUREN WUCIN GADI Page 003 Na Usman Umar Gombe (Babangida Ustazu) Call/WhatsApp 08137017208 Na Sadaukar Da Wannan Shafin Ne Ga Marubuciya Sister Fareedat Hussain Mshelia (NIGER STATE) Domin Makaranta Imam Aliy A.S Yace: (( Mutane Masu Gaba Ne Da Abun Da Duk Suka Jahilta )) NAHJUL BALAGHA Sai suka kwashe da dariya, Daga nan sukaci abincin nan tare su su uku suna ta barkwanci suna dariya gwanin ban sha'awa ita kuma sai tsokanar su take tana cewa NASAN SILA Santi ne kawai Ke ebarku. Musa bai ma bari an karasa ba yace: Kin ganni nan zan tafi! dan idan naci gaba da biye muku maman sajjad zata iya tarata latti a kowa ni lokaci. Sulaiman cikin zolaya yace: Ai kai ta gama da kai, kamar yadda jamsi mai sanyi na ta shanye ni, a malaman novel da littatafan koyan girki. Sai jameela tace: Kwadaiji da shi! Suka kwashe da dariya dukansu, sai da sukayi jayayya mai yawa sosai tsakanin Sulaiman da abokinsa sannan daga baya musa ya yarda sulaiman ya dan raka shi kadan bakin kofa dan ya hau mashin dinsa, Dan wannan lokacin ma tara ne da rabi 9:30pm, Sulaiman ya juya ya koma gida sai jameela ta tada sabon rikici kuma tana ta masa kukan nan na shagwaba akan sai ya fada mata meye yasa yau bai dawo da wuri ba sai kusan isha yayi ta lallashin ta, tace itafa bazata hakura ba, yace: to shikenam bari na durkusa har kasa dan kinsan ance durkusawa wada ba gajiya bane. Sai ta kara rushewa da kuka tace: Wato kenam ni wada ce agun ka, kana nufin kana da wanda ba wada ba a waje ko, Saboda ina tsammanin shi yake kaika yawon gane-gane. Da kyar da jibin goshi ta yarda ta daina masa kuka saboda yace: mata gobe idan allah ya kaimu zan daukeki muje muyi ziyarar gidan yan uwa da abokan arziki, dan haka zamu fara zuwa gidanmu da gidanmu. Cikin rashin fahimta Tace: Ban gane gidanmu da gidanmu ba. Cikin fushi yace: Wato ke gidan ku ba gidan mu bane ko ? Cikin jin kunya tace: Sorry! mai sanyi na. Can ta matse miki, yace yana mai nuna halin ko in kula. Tace: Nika ganka nan kawai ka tashi muje mu kwanta! Yana tace haka yace: saboda meye ai kawai ki barni, To ai ina sone gobe kada ka makara. To, naji, yace mata Ya tashi ya daga ta sama da hanneyensa biyu kamar wata yarinya karama yace: Mai Sanyi! meye yasa har yanzu baki da nauyi ne, ko idan na tafi bakya cin abinci ne ? Ba tafiya kake yi ka barni ba, kaje kayi ta kallon matan kaduna ba, tana fada kamar zata yi kuka. Yace: kwantar da hankalin ki an kusa karasa gina mana gidan mu nacan ana gamawa kuma zamu koma can idan ma meye nake gani duk tare zamu gani. ji tayi wani dadi ya ziyarci har cikin kwakwalwarta daga zuciyanta, tace: daman na gaji da zama a gidan nan ni daya. Cikin zolaya yace: Wato kice kafun na tafi na samo miki kanwa tazo ta taya ki zama. take ta kautar da maganar sai ji tayi yana sauketa akan gado, yaje ya kawo mata sleeping dress shima ya sanya nashi a jikinshi. (Lokaci daya ya tura kofar dakin ya barni daman ko bai barni ba, ba shiga zanyi ba Saboda Ni Daman Sunana Babangida Ustazu, Ustaz kuma ba'a sanshi da leqe-leqe ba) *** Washe gari da sassafe Lokacin da amma fara sallah a wasu masallatan sai jameela ta tashi mijinta akan ya tashi yayi sallahn asuba sannan ya koma baccin saboda tasan yadda yasha gajiyar mota jiya wajen dawowa daga kaduna, hakan kuwa akayi yana tashi yaje yayi wanka sannan suka gabatar da sallahn su na asuba a daki tare, sannan ya koma bacci, Ita kuma jameela ta fara kokarin shirya musu abun karin kumallo kafun ya tashi, bayan ya nemeta akan ta bari idan sun fita da safe su biya ta Aroma Restaurant Su karya a can, tace fir bata yarda ba dole ya koma bacci ya rabu da ita. Nan take ta dafa musu (Fried Rice) girkin nata bai dauki wani lokaci ba ta gama, sai ta dauko blandernta ta marka gyadanta, ta tace ta daura a wuta da yake da gas Cooker take amfani take ya tafasa sai ta dauko shinkafarta ta wanke ta zuba... a takaice MURDAM ta shirya masa mai dan karen lafiya, saboda tasan yadda yake masifan Son murdam. Tana gama wa takai kan dinning table shi kuma yallaboin yana can yana ta shakar baccin sa, Lokacin ta kara komawa ban daki ta shirya wani wanka na musamman ta dauko shaddarta Bugeggegiya Blue Ta kashe wani dauri na musamman wanda zaka iya kiransa da Step-by-Step ta baya kuma ta kumbushe shi, Saboda irin baiwar da allah ya mata na gashi mai tsayi da sheki ga santsi. (Hakan Fa Baya Nuna Nima Ustaz Na Taba, Taba Gashin A'a kawai Dai Alamomi Na Gani) Da kamar misalin karfe 8:30am ya tashi sai ji yayi dakin gaba daya ya kaure da kamshin turaren Techno da kuma One million suka hadu suka samar da wani irin daddadan kamshi daya cika dakin gaba daya, Sai ya fara dube dube dan ya ga Mai sanyinsa sai ya duba ta gefen dama kusa da gadon da yake kwance sai ya ganta a kan kujere hankalinta ma ya gama tafiya cikin abun da take yi. ji tayi kawai yace: Sarakunan online safe facebook da rana facebook da dare facebook, sannun ki da kokari. Cikin nuna ai ba komai bane tace: ayya ai rabo na da facebook tun jiya da safe saboda zaka dawo shine na kasa sukuni, shine yanzu nake basu amsa dan sunji ni shiru a group din mu na Dandalin Mshelia's Hausa Novel. KASH MU HADU A PAGE 004. AUREN WUCIN GADI Page 004 Na Usman Umar Gombe (Babangida Ustazu) Call/WhatsApp 08137017208 Na Sadaukar Da Wannan Shafin Ne Ga UwarDaki Na Mrs. Aisha Usman waziri (MAMAN IHSAN) (Aduwa Biyu K/Mata Gombe) TSARABAR MAKARANTA Imam Ja'arus Sadiq A.S Yace: (( [[Daga Halayen Jahili Karbar (Magana) Kafun Yaji (Hujja), Kalubalanta Kafun Ya Fahimta, Hukunci Da Abun Da Bai Sani Ba]] )) BIHARUL ANWAR J5 S63 Allah ya sawwake yace, sai tace: kaje kayi wanka bayan ka fito break fast is ready ranka ya dade, sannan kuma ga kayan dana zaba maka zaka saka a yau. kayan ma sai an wani zaba min baza a bani 'Yancin zabi ba, kamar yadda muke da'awar a bawa kowa yancin zabi. Tace: to ai wancan daban nikuma daban. To! yace ya tashi ya shiga bayan gida dan shiryawa bai dauki wasu lokuta ba yayi wanka ya fito, ya same ta anan inda ya barta tana ta danne-dannen waya Kai Shi Daki Tayi Ta Dauko Masa Blue din Shadda Kalar Wanda Yake Jikin Ta Duk Da Cewa Shi Ba Mutum Bane Mai Son Yin Anko Da Matarsa Amma Tun Da Yasan Hakan Zai Faranta Mata Yasa Ya Nuna Halin Ko In Kula, Ta Dauko Masa Wata Zanna BLUE Wacce Aka Mata Shige Da Fari Ta Dauko Masa Fararen Takalma Sau Ciki Farare, Take Ta Dau Turaren Nases Ta Shafa Masa Saboda Tasan Yadda Yake Masifar Son Wannan Turaren Ta Bi Ta Feshe Shi Da Turaren Five Eleven. Take Ta Kaishi Kan Dining Table Ta Fara Bashi Abinci A Baki Tana Bashi Labarin Gonayen Marubuta Littatafai Da Ta Sani A Baya Kamar Irin Su Shafiu Dauda Giwa Da Labarin Sa Na RASHEEDA, shi Kuma Yana Mamaki Da Irin Zurfin Tunanin Wannan Marubuci. Gama Cin Abincin Keda Wuya Sai Yaji Wayan Sa Tana Ringing Na Wakar Nazifi Asnanic Na Jameela Da Jameelu, Yana Dauka Sai Yaga Ashe Abokinsa Ne Sulaiman Cikin Kaguwa Ya Dauki Wayar. Yace: Haba Aboki Ya Baka Zoba What time now. Musa Yace: Sorry! Bazan Samu Zuwa Ba Amma Na Aiko Maka Da Mashin Tun Dazu Garba Zai Kawo Maka. Yace: Fada Min Gaskiya! Ko Dai Maman Boy ne ta Riqe Ka? Musa