← Book details Auren Wucin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 10

Sashe 6

Auren Wucin Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

shi yan bayyi ringing da yawa ba, ya daga wayar. Ji tayi yace: masoyiya yanzu haka kina raina ina so na kiraki amma ban san meye zan fada miki shine na kasa nake ganin zan bari idan mun sauka lafiya zan kira ki! "Ayya daman ina sone gobe inje wuni gidan mu dan rage kewa" jameela ce ta ke fada. "Na sha fada miki cewa irin wannan dukka baki bukatar sai kin fadamin a zahirin gaskiya, you are free to do what you want i believed with your all behaviour, dan haka baki da matsala in dai anje a gaishe min da su umma da sauran yara. "Nagode masoyi daka dauki 'yardarka gaba daya ka bani allah ya barmu a tare har gidan aljannah" jameela ce, ta fada. " idan kuma zaki tafi zaki iya kiran garba ya kaiki a mashin ko ? "Eh yadda kace haka za'ayi" ta fada Yace: A'a yadda kike so dai. "Yanzu kuna ina" Yace: Eh yanzu haka mun iso yankin bauchi" "Ayya to allah ya kaiku lafiya dan nabiyyur rahmati" A tare suka ce: SALLAL LAHU ALAIHI WA ALIHI WA SALLAHI. Yace: Idan muka isa zan kira ki Bye. Tace: Bye "I Love You" Yace: "I Love You Too" Sukayi ban kwana ai kuwa hakan yasa ta kara jin wani dadi na musamman bisa karfin guiwar da yake saka mata na nuna alamar ya yarda da ita dari bisa dari tana cikin haka ne sai bacci yayi awon gaba da ita da waje kusan 11 na rana. *** ***** *** Da kamar misalin 3:00pm musa yayi ta dialing numbern musa, amma sai dai tayi ringing shiru haka dai kuwa yayi ta try daga baya yaji ta a kashe hakan sai tasa yayi tsammanin ma watakila ya isa nema ya barta a caji ya tafi. Da kamar misalin karfe karfe 5:30pm ne lokacin da musa yana kan hanyarsa ta dawo wa gida yaji an kirashi da bakuwar number, sai kawai ya daga ya kara wayar a kunnensa ai aikuwa sai yaji ance "Assalamu Alaykum" Mai maganar bai bashi damar amsa sallamar bama yaci gaba da cewa "kaine Musa Abdullahi gombe Dan uwan Sulaiman muhammad deba wanda ya hau mota daga gombe zuwa kaduna da safiyar yau..." Musa bai bashi damar ko da karasa maganar ba yake ce masa "nine nine nine"!!! "Sunyi hatsari garin bauchi a hanyar su ta shiga yankin jos yanzu haka suna General hospital bauchi" Ai kuwa sai ya ji maganar nan kamar saukar araduwa akansa sai ya gigice yama rasa ma meye zaice ya kuma rasa abun da zai fara yi, ai kuwa a haka sai shawarin kawai ya tafi jeka da fari yayi kawai dan ya sanar dasu abban sulaiman din yadda ake ciki. Ai kuwa sai yaja mashin dinsa ya nufi anguwarsu gudu yake yana ta tunanin yadda al-amarin tafiyarsu zai kasance bai dauki wani dogon lokaci ba ya isa yana zuwa da yake ya saba kai tsaye yake shiga gidan yana zuwa gidan sai yayi sallama akan yana son yayi magana da abba umman sulaiman din nema da kanta Tace: ai Bai dawo gida ba. Tace amma dai lafiya kam. Kalau yace. Sai yace to bari yaje zai kira sa a waya ai kuwa haka akayi yana fita ya kira shi a waya ya sanar dashi halin da ake cikin ai nan take alhajin sai yace: kasan ya za'ayi mubi komai a hankali mu bari gobe da asussuba mu tafi. Amma yanzu zanyi waya da alhaji kasimu na bauchin akan yaje ya duba shi kafun mu taho, amma kada ka sake ka sanarwa da jameela da halin da ake ciki saboda kar kuma abun da sauki ta janyo mana wani abu dabam!. Insha allah abbba bazan sanar mata ba. Ya fara sukayi bankwana ya kashe wayarsa. Kawai sai ya kama hanyar gida yana zuwa sai ya samu iklima tana zaune tana karatun wani littafin addini na musamman na turanci mai suna "To be with the truthfull" wanda gaba daya ya dauke mata hankali gaba daya da alama tana kan wata gaba ta musamman ne a littafin yasa. Sallama ya sake maimaita mata da karfi ai kuwa sai tayi firgigit ta duba sai ta ganshi ta amsa masa sallamar sannan ne ta fahimci cewa gaba daya wannan littafin ya tafi da hankalinta. Zuwa kawai yayi ya zauna kusa da ita kadan sannan ya fara sakar zuci bai ce mata komai ba. Daga nan ta fahimci akwai matsala ta juya ta fuskance shi gaba daya. Tace: Baban sajjad lafiya kuwa naga ka shigo ba walwala ko dai an bata maka rai ne? Yace: Gobe zamu tafi bauchi! Kwatsam taji abun haka wani dabam Tace: bauchi kuma meye zamuyi a can ? Yace: sulaiman ne sukayi hatsari da mota a hanyarsa ta komawa gun aiki! Sai kawai ta ajiye littafi ta fara Istirjai (INNA LILLAHI WA INNA ILAHIRRAJEEUN) Da fatan dai yana nan cikin koshin lafiya, ta fada. "Kawai nima dazu yan Union suka kirani suke sanar dani halin da ake ciki amma wai sunce da sauki" Amma na sanarma abbansu yace ba komai gobe zamu tafi da safe duk da kuma ya gargade ni akan kar jameela tasan halin da ake ciki dan haka kema na gargade ki akan kada ma wani dabam ya sani. *** **** **** Hakan akayi a gida lokacin da abba ya koma ya sanar da umma da sa'adatu da sauran yaran gidan akan halin da ake ciki ai kuwa sai suka fara koke-koke. Nan take abba ya hausu da fada ya nuna musu ai ba rasuwa akace yayi ba balle suyi ta masa ihu a gida. Ai kuwa sai ya gargade su akan kada jameela ko wani dabam, yasan halin da ake ciki.
Chapter 6 · 0% Book details