Sashe 3
Auren Wucin Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yace: Haba Friend Kawai Dai Nace Maka Akwai Dalili Amma Dai Sai Mun Hadu. Yace: Shikenam Ka Gaishemin Da maman Boy ? Yana Ajiye Wayar Yaji Kuma An Kara Kiransa A Waya Sai Yaga Wata Bakuwar Number Yana Dauka Sai Yaji Ance: Ango Mijin Amarya! nine Garba Abokinka Ne Ya Aikoni Da Mashin Wai Na Kawo Maka Ina Kofar Gida ? Yace: To, Take Ya Cewa Jamela Ki Tashi Kawai Tacan Mu Wuce, Ko Musu Babu Ta Dauki Gyalen Ta Baki Mai Nauyi Ta Yafa Tabi Mijinta A Baya. Bai Bata Lokaci Ba Saboda Ba Sosai Yake Magana Da Garba Ba, Ya Karbi Mashin Din Yayi Hanyar Shiga Gari Shi Da Matar Sa Suna Tafiya Suna Tadi Gwanin Ban Sha'awa Tana Bashi Labarai Shi Kuma Sai Dariya Yake Cikin Tsananin So Da Kula. Basu Tsaya A Ko Ina Ba Sai Anguwar Dawaki Da Yake Zagaye Sukayi Suka Fara Zuwa Gidan Su Jameela, Tun Daga Kofar Gida Da Yara Suka Ganta Sai Suka Ruga Da Gudu Suka Nufi Cikin Gida Suna Cewa Ga Adda Jameela Ga Adda Jameela Kasantuwar Jameela Mace Ce Mai Son Yara Shi Yasa Idan Yaran Anguwa Suka Ganta Sai Kaga Suna Dauki Saboda Sun San Zata Basu Wani Abu In Zata Tafi. Cikin Nitsuwa Ta Sauka Daga Kan Mashin Tace: Mai Sanyi Sai Mushige Ko Cikin Kulawa Da Zolaya Yace: Sai Ki Fara Yin Gaba Tace: Naki Din, Sai Dai Mujera Mu Shiga A Tare In Har Bazakayi Gaba Ba. Dakyar Dai Ta Yarda Tayi Gaba Suka Shiga Cikin Gida, Su Jameela Bawani Babban Gida Bane Kawai Dai Irin Gidajen Nan Ne Na Rufin Asiri. Ta Masa Rakiya Har Falo Ita Kuma Umma Tana Ta Masa Sannu Da Zuwa Mutanen Kaduna Shi Kuma Gogan Sai Ya ke Yake, Suna Zama Yara Kanen Jameela Ameer Da Surayya Suka Zo Suka Durkusa Cikin Girmamawa Suka Gaishe Da Adda Jameela Da Sannan Suka Juya Zuwa Musa Sukace: Yaya Musa Ina Kwana Cikin Zolaya Yace: Bazan Amsa Gaisuwar kuba Saboda Bakwa Zuwa Gidan Addan Ku. Caraf Sai Surayya Ta Cafke Maganar Tace: yaya Shekaran Jiya mafa Munje Tun da Safe Sai La'asar Muka Dawo Lokacin Baka Gida ? Sai Ya Juya Gun Jameela Yace: Addarsu Anyi Haka ? Tace: Eh Anyi Haka Yallaboi Yace: To! Meye Yasa Baki Fada Min Ba Tace Na manta Ne Sorry! Take yasa hannu a aljihu ya ciro dari biyu ya basu sukaiwa yaran da suke waje akan su raba suka fita suna ta murna sunsan suma zai basu wani ba idan zai fita. Ana Cikin Wannan Muhawara Ne Sai Umma Ta Shigo Falon Da Suke Zaune Cikin Girmamawa Musa Ya Zube Kasa Yace: Umma Ina Kwana ? Cikin Kulawa Tace : Masa Lafiya Kalau Ya Aiki Ya Mutan Kaduna ? Yace: Lafiyan Su Kalau Umma, Sai Jameela Tace: Umma Ina Kwana Ta Amsa Mata Sai Take Tambayar Ta ina Abba Tace: Ya Fita Kasuwa Tun Karfe Takwas Dan Yace Za'a Sauke Masa Kaya Yau. Suna Gama Gaisawan basu wani dadewa ana tadi ba na wasa da barkwanci dan sun kai kusan dakika ashirin da daya sannan Sai Sulaiman Yace: Umma Mukan Zamu Tafi Sai Wata Rana Amma Daman Ina Sone Na Fada Miki An Kusa Gama Mana Gidan Mu A Kaduna In Da Zamu Koma Tare Da Jameela Cikin Murna Umma Tace: Tace Nayi Murna Sosai Amma Kafun Ku Tafi Da Kun Tsaya Na Muku Ko Dan Abun Da Zaku Taba. Caraf sai jamela ta amshe ta da cewa, haba umma kina nufin banyi masa abun karyawa bane muka fito? Da yake ita Umma mai wasa da dariya ne sai tace: aa ina nufin ku tsaya kuci dafaffen girkin ba shiririta ba ? Sai jameela tace: umma kina nufin shiririta nake mana a gida kenam? Ban fada miki ba nikam, umma ta fada. Shi kuma sai yake yake yana dariya a haka dai muka tashi zasu tafi. Sai sulaiman yace: umma zan dawo ko mu dawo tare saboda zanyi sati biyu anan garin kafun na koma amma idan abba ya dawo kice masa ina gaisheshi kuma zamu dawo gaisheki shi. Umma tace: Insha allahu zaiji dama kunyi hakuri ko nakira muku shi a waya yazo ku gaisa. Aa umma ba komai zamu dawo dai inji jameela tana maganar tana dariya. Haka zasu fita sai ya zare dubu uku dari biyar-biyar ne sabbi ya mikawa jameela yace: ki bawa ummana ta sayi goro, Tana karba kawai sai taje karkashin filon umma ta ajiye su umma tana gani babu yadda ta iya saboda kusan haka jameela take mata dan idan da zaace umma karba zatayi da sai dai su wuni su kwana amma bazata karba ba. Nagode, allah ya saka umma tace, tana nan a zancen ta sai ga surayya da ameer sun dawo suna ta tsallen wasa da murna nan take ya ciro 200 Ya bawa surayya da ta nuna bazata karbaba saboda idon umma amma sai jameela ta miqawa ameer wanda shi shiru-shiru akan ya kaiwa umma tana musu canji na kudin taran makaranta, ya karba. Sai inna ta fara yiwa jameela masifa akan meye yasa take haka ita kuma ta wuce gaba, sulaiman kuwa yana ta baiwa umma hakuri cikin raha sai kawai suka fita. Kafun su hau mashin din ne yace: sai JekaDaFari ko ? tace: sai yadda kace, nima bama wannan ba ina sone na kara maka godiya akan yadda kake karrama iyaye na da mutunta su kuma kake musu alkhairi... bai bari ta kara saba yace dakata wato ke kina ganin iyayenki ba iyaye na bane ko meye, wallahi kina bani mamaki idan ban yiwa naki ba waye zan yiwa, hakan ma dai nasan cewa babu abun da nayi ina fatan har na samu karin mukami a gun aiki buri na in biyawa umma da abba kujeran hajji saka makon yaba tukuici. INA NEMAN UZURI DAGA MASU KARATU AKAN CEWA WAYAR DA NAKE RUBUTU DA ITA TA SAMU MATSALA AMMA INSHA ALLAH BAZAN WUCE KWANA UKU BA KOMAI ZAI JARU, INA SONKA FATANA KUCE INA NISHADANTAR DAKU KASH MU HADU A PAGE 005 AUREN WUCIN GADI Page 005 Na Usman Umar Gombe (Babangida Ustazu) Call/WhatsApp 08137017208 Na Sadaukar Da Wannan Shafin Ne Ga Addata Ayshfat Muhammad Galadima (Momi) (Federal Lowcost Kusada Ministry of Agric/Fadama II Gombe) TSARABAR MAKARANTA Manzon Allah S.A.W.A Yace: (( [[Lallai Nina Bar Muku Khalifofi(na) Guda Biyu AlQur'ani... Da Iyalan Gidana -AhlulBayt-...]] )) MUSNAD AHMAD Basu wani dade suna tafiya ba saboda ba wani tazara bace mai nisa daga dawaki zuwa jeka da fari, Suka iso gidan su Sulaiman. Babban gida ne wanda babu yabo ba fallasa shigewa sukayi cikin gidan take yana gaba tana binsa a baya suna tattaunawa suna dariya irin na masoyan da suka shaqu da juna, sallama yayi aiko khadija ce ta fara gane shi tace, "Waalaikussalam" Aikuwa sai ta ruga da gudu ta fada dakin maman su tace: umma! Umma!! Umma!!! "Haba meye ne kina ta kiran mutum kamar wata makahuwa" Umma ta fada tana hada fuska. "Yaya sulaiman ne yazo, da anty jameela !!!" "Haba khadija shine kike ta kwalamin kira to ya fada min daman tun shekaran jiya kafun ya dawo" umma tace "Haba umma yaya baki fada min ba kuma" khadija tace. Kafun umma ta bada amsa, kawai sai sukaji sallamar sulaiman ya shigo daki. Umma ce ta amsa tana musu maraba lale da zuwa. Ita kuma khadija kamewa tayi tasha mur a gefe guda har sulaiman ya zauna suka gama gaisawa da umma. "Meye yasa mu 'yan gatan umma ne kam... ta share yayanta, Haba Dija Kaya bakisan ta gida ba..." sulaiman yayi ta mata maganganu dai na tsokana. Juyowa tayi tace: haba yaya yanzu zaka dawo baza ka kirani a waya ka fada min ba, sai dai ka kira umma ita ma ba fadamin tayi zaka dawo ba sai yanzu take fadamin.." Caraf sai jameela ta cafke maganar da fadinta "Rabu da ita daman bata ma ko zuwa gidan yayan nata..." Haba anty wancan satin ba naje ba. Khadija ta fada Amma ai ya dade shi yasa Tace: to shikenam zan na zuwa shikenam "Shikenam" shima yace. Daga nan ta juyo ta gaishe shi ya amsa yana mai fara'a. Ta juya sashin anty jameela ta gaishe ta ta amsa cikin sakin fuska ta amsa mata. Daga nan sai yake tambayar umma ina umma sa'adatu da sauran yaranta. Sai umma tace: sun tafi kuma auren wata yar uwarsu a kumo duk dama gobe zasu dawo. To umma kinsan fa na kusa komawa ko kaduna ya kamata idan na tashi ko mawa na tafi daku gaba daya gidan nan aje ayi walima na mussamam. "Ai kai ma kasan wasa kake dan kai ma kasan babanka ba bari zaiyi ba mu tattare gaba daya mu tafi gidanka dan mune sarakunan masu hankali. Sai dai kawai wasu yara suje daga baya manya suje ko da bayan walimar komawa din ne. To shikenam Umma amma dai ban so ba. Daga karshe dai sulaiman tashi yayi ya tafi gurin abokinsa ya bar Jameela tayi ta taya khadija aikin gida sukayi ta wanke-wanke da girki. Ana cikin haka jameela ta shiga daki ta tattaro kayan sawan umma wadanda sukayi dotti umma tana ganin haka tace aa wallahi ban isa na wahalar da surukata ba, da ker da ji6in goshi amma ta yarda saboda zakin baki da iyayi yasa ta dauko sabulu daman kala uku ta gani da alamar an saka ta wanke su tas suka fita ta shanya a lokacin ne abincin da suke dafawa tare da khadija ya karasa dahuwa ta sauke khadija ce ta raba aiko san ta saka muku jalof din taliya da waken a tire na umma dabam Sannan na yaya sulaiman dabam. Aiko sai umma ta tubure akan allanfir sai an hadasu suci su ukun tare hakan kuma akayi kasan tuwar umma dattijuwa ce wacce babu ruwanta ga kyan hali shi yasa kullum jameela take gode wa allah akan yadda allah ya bata umma uwar miji saliha. ASALIN LABARI Alhaji muhammad deba shine asalin sunan babansu sulaiman asalinsa dan garin deba ne na karamar hukumar yamaltu deba, a can ya taso amma sai sana'ar sa ta kasuwanci ta dawo dashi cikin garin gombe tun lokacin sulaiman yana yaro dan shekara shida kafun daga baya ya kara aure bayan kasuwancinsa na