Sashe 10
Auren Wucin Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
musa mai waccan gidan in yaso koma yaya daga baya zakaji, Alhaji rabiu yace: haba malam nura nifa gaggawa nake da wannan abun gaskiya, banki bama yanzu haka ma muje mu same shi ba tunda ka riga da kasanshi. "Haba meye kake ci na baka na zuba, kawai ka saurare ni zan tuntu6e shi gobe da safe" Malam nura ya fada yana yiwa abokinsa dariya. Alhaji rabiu yace: to mu dawo maganar gidan da muke *** **** *** Washe gari da sassafe malam nura yaje kofar gidan musa ya rangada masa sallama mai kyau. Daga ciki kuwa ikilima tace: baban sajjad kamar fa sallama ake yi daga waje! "Sallama kuma? "Eh wallahi" bata gama rufe bakinta ba kuwa sai ji ta karayi an kara sallamar da karfi, musa yace: eh yanzu kam naji, kawai sai ya amsa da karfi, daman jallabiya ce baka a jikinsa ya tashi ya tafi ya nufi kofar gida ai kuwa sai yaga malam nura kasantuwar malam nura irin shahararrun mutanen nan ne da kowa ya sansu a unguwar. Yana fito yaga malam nura suka gaggaisa daga karshe musa yace masa: lafiya kuwa yau naganka da sassafe ? Yace: eh wallahi lafiya daman jiya ne mai gida na wato alh. Rabiu da yake tumfure yazo duba wancan gidan ne yana so ya saya sai yaga wata yarinya tazo gidan nan kuma alal haqiqa yaji yana son ya yarinyar nan da aure, ni kuma nace masa ni dai ban san akwai wata yarinya budurwa a gidan nan ba, shine ya nemi alfarma akan na taimaka nazo tambaya masa inhar ba'a mata miji ba to yana sonta da aure. Sai musa yace: eh gaskiya ne jiya akwai wacce tazo gidan nan kuma a gaskiya ba budurwa bace bazawara ce, matar abokina ne sulaiman wanda ya rasu, in dai har ita yake magana to ba'a mata miji ba amma ba'a anguwar nan take ba tana dawaki ne, acan gidan iyayenta suke ? "To yaya kake gani idan har yaje gidan nasu?" mal. Nura ya tambaya. Musa yace: a matakin farko idan har ta masa yaje ya fara neman amincewar mahaifinta tukun na daga baya kuma duk yadda ta kasance tsakanin ta da shi mai gidan naka maji mukam. "To nagode musa allah ya saka kuma insha allah zan isar masa da duk yadda mukayi" Malam nura ya fada. Nan take sukayi bankwana sukayi sallama musa ya juya ya shiga gida. Yana shiga gidan kuwa sai ikilima ta tare shi tace: waye ne yazo ? kuma meye ya faru ? Nan take musa ya fada mata duk yadda ta faru tsakaninsa da malam nura bai rage komai ba. Nan take taja wani dogon numfashi tace: To kai kasan shi alh. Rabiun ne ? "A'a" Yace yana mai kada kayi. Tace: to idan nagari ne allah ya tabbatar mata dashi. "Ameen" yace kawai sai ya nufi parlor ya shige, itama binshi tayi a baya tana jinjina maganar daya fada mata a ransa. *** ***** *** Baya malam nura ya isarma da alh. Rabiu yadda sukayi da musa, tun da yaji ma bazawara ce sai kawai ya sanya a ransa cewa bazai aure ta ba zai neme tana idan bukatarsa ta biya kawai ya gudu ya rabu da ita, hakan tasa ya kuduri niyyar sakewa iyayenta kudi ta yadda zai samu sauqi wajen cika burinsa da gaggawa wannan shine abun daya kudurce a zuciyarsa ko malam nura bai fadawa. Ai kuwa nan take sai ya sanya wani yaronsa ya bincika masa masa komai na dan gane da gidansu jameela, da yake mutuminsa ne sosai yace: masa ya bincika shin tukun nama gidansu suna da kwadayin abun duniya, ya bashi kwanaki uku dan gabatar da wannan aiki na musamman dan alhajin ya bayyana masa cewa wannan aikin da zai masa yana da matukar muhimmanci dan haka baya so ya kuskure wajen neman bayanan. KASH MU HADU A PAGE 016 PAGE SummaryInformation DocumentSummaryInformation WpsCustomData TECNO LD7 WPS Office Normal Default Paragraph Font Header Char header Times New Roman Times New Roman MT Extra MT Extra Symbol Symbol Wingdings Wingdings Clockopia Times New Roman !%),.:;>?]} $([{ ac8be1207dba4199975b0c08ed59f1c7