← Book details Auren Wucin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 10

Sashe 8

Auren Wucin Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka nan dai jameela ta nuna ta damu akan a sallamesu a asibitin ana sallamarsu kuwa da kusan karfe goma dan a lokacin ne ruwan da aka daura mata ya kare, sulaiman ya dauke su yayi hanyar gidansa da ita tare suka kwana da ita, sannan ya mayar da su ummanta gida ya biya ya maida khadija gida. Haka nan dai jameela ta kwana tana kuka idan ta gaji sai ta tashi tayi sallah iklima tayi matukar tausaya mata akan halin data shiga haka har gari ya waye jameela haka taki taci komai da kyar da sidin goshi ta yarda ta dan sha shayi ba ko madara, hakan ma dan musa yasa baki ne, Da kamar karfe bakwai garba musa ya dauki mashin ya kai jameela har gidan su abba taga gidan ya cika babu masa tsinke tun daga matayen anguwa wasu kuma yan uwa da abokan arziki na kusa, ai kuwa suna shigowa sai sabon kuka jama'a suka fara ai itama kuwa sai tayi ta kuka tana cikin kukan ne sai sukaji ance to za'a shigo da sulaiman motar asibiti tazo. Haka aka mammatsa aka shigo da shi a makarar asibitin aka kaishi daki jameela tana ganin an wuce dashi dakin da garba yake kwana ta shiga tana ganin an ajiye shi sai tayi birki a lokacin ne, ta tsaya ta hange shi a cikin likkafani tana kure masa ne ai kuwa sai ta fadi ta kara suma. Haba wa ai sai gida ya kara hautsinewa da hayaniya. KASH MU HADU A PAGE 012 AUREN WUCIN GADI Page 012 Na Usman Umar Gombe (Babangida Ustazu) Call/WhatsApp 08137017208 I dedicate this page to my arabic student of Mahdi Scout Fudiyya Ceceniya yashin Dam gombe DON MASU KARATU Imam Aliy bn AbiyDalib A.S Yace: ((Tsoron Allah Shine Shugaban Dukkan Halaye)) NAHJL BALAGHA 4:613 H404 A wannan karon ma dai kamar wancan lokacin tana farkawa daga dogon suman da tayi sai ta duba gefe da gefe sai kawai taga umma faty kanwar mahaifiyarta tana zaune a gefen gadon tana jinjina irin halin da jameelan take ciki, a gefe kuma kawarta ce ikilima matar musa, da kuma khadija wacce bata cikin hali mai dadi. "Ina miji na? da gaske ne mijina ya rasu? Na rabu dashi kenam har abada?" Haka jameela ta rinka sanbatu, Wannan kukan kamar kara alerting din khadija ya itama ta sake fashewa da sabon kuka tare da sheshshekar hawaye. Umma faty tana ta bata hakuri tana ce mata: yanzu ashe jameela da iliminki da hankalinki da girmanki kina so ki afka cikin sabon ubangiji kina nuna fushinki akan abun da allah ya kaddara miki na rashi, ni bazan hana ki kuka ba saboda kuka yana rage bakin ciki na radadin rashi, amma na tambaye ki shin yarda da kaddara alkairi da akasin sa baya cikin akidar musulmi? Ko kuma kina sone ki nuna kinfi ubangiji son bawansa wanda ya kaddara masa rasuwa? Ki fada min shin kin ubangiji sonsa ne, kuma kina tuhumar ubangiji akan Adalcinsa ne? Ki fada min kawai. Da ta sata a gaba sai da tace: a'a? To, ki bar kuka ki fawwala dukkan al'amarinki ga allah shine kadai mai yaye bakin ciki a duk lokacin da musiba ta samu mutum. Maganganun da umma faty ta mata na nasihohi ba karamin tsumata yayi ba tare da khadija da ikilima wadanda a sashi guda suna kuka ne kawai dan tausayin jameela a wancan lokacin. "To yanzu umma faty yanzu kina ganin yanzu a duniyar zan iya samun kamar sulaiman ne kuwa lallai nikam ni nayi rashi wanda bana tsammani zan mai da gurbinsa" jameela ta fada tana share kwalla. Sai umma faty ta rufe bakin ta tace: haba jameela karka fadi haka yanzu ke kina tsammanin wayonki ne ya baki sulaiman din ko da kin sanshi, to ki mai da al'amarinki ga allah zai kawo miki abun da yafi shi..." Jameela dai kawai jinta take tun bata yarda har tazo tana ganewa, da yake umma faty ta kasance mai tarin ilimi da hikma dan wanda take aure babban malami ne na addini, kaga kenam ko da ba tayi karatu ba akwai tsammanin haka balle daman ita din ma ba kanwar lasa bace. Hakan kuwa akayi alal a qalli sai da su jameela sukayi kwana uku sannan aka sallame su a wannan asibitin haka sukayi ta zaman takaba tare da ikilima da umma faty ai kuwa sai gaisuwa ya zama biyu da ta'aziyya da gaisuwar maras lafiya, gaske a cikin ran jameela cike yake da mamakin wasu jama'ar da take gani na musamman wadanda bata tsammanin sulaiman ya sansu ai kuwa haka daga garuruwa dabam dabam ana zuwa gaisuwa idan anje gidan su na jekadafari sai azo gidansa na byepass a gaishe da matarsa, tsawon wannan lokaci. A ranar safiyar bakwai ne na rasuwar sulaiman sai musa ya tara taro na musamman dan karantawa marigayin al-qur'ani da niyyar allah ya kai masa ladan ya gafarta masa, akayi kunu da masa aka raba raba sadaka da neman allah ya gafarta masa, haka kullum musa yake kawo matarsa da dare kuma ya koma dare ya dauko ta. *** *** **** Haka nan jameela taso ta koma gidan tun bayan kwana arba'in da rasuwar mijinta amma babanta ya tubure yace sai ta karasa iddanta duk sannan ta dawo, hakan kuwa akayi ta zauna a gidan ba saka turare ko mai mai kamshi aka hanata saka lalle ko wani ado na musamman na mata tsawon wata hudu da kwana goma na iddanta, ga tunani na rashin mijinta ga kuma an hanata kwalliya ko wani ado na mata hakan yasa ta canja jar fatarta ta wani dishewa ta kara rama kai kace ba ita bace jameela idan ka santa a baya. A lokaci da dama ikilima tana kokarin ta bayyanawa jameela akan cewa daina wasu ado da kwalliya ga mai takaba wannan wani gargajiyanci ne na yan mazhaba ba wai daga allah yake ba ko daga annabi. Sai jameela tace: to ai wannan shine al'adarmu kuma na tabbata yadda abbana ya zafafa akan wannan abun muddin yazo ya taras ko labari ya riske shi, ba karamin matsala zamu samu ba dashi? "Sai kici gaba da zama cikin kuncinki ke daya" ikilima ta fada mata tana mata dariya. Haka dai tana dawo wa gida ne abbansu sulaiman yaje ya samu abbansu jameela ya dauki wasu kudade makudai yace: wannan shine tumulin takaba na jameela. "Haba alhaji duka wannan ai yayi yawa. yace: a'a baiyi ba gaskiya wannan haqqin tane. "Allah ya saka alhaji shi kuma sulaiman allah ya gafarta masa zunubansa mu kuma idan tamu tazo allah yasa mu ciki da imani" abban jameela ne ya fada. Haka dai suka rabu suna yiwa juna jajen abun da ya faru na sannan sukayi sallama da juna abban su sulaiman ya nufi gida da motarsa daga nan kuma abba ya shige gida...? **** **** **** KASH MU HADU A 013 (Meye Kuke Tsammani A Idan Musa Yace: Zai Auri Jameela ya hada su da ikilima) ??? AUREN WUCIN GADI Page 013 Na Usman Umar Gombe (Babangida Ustazu) Call/WhatsApp 08137017208 I dedicated this page to my mentor Aunt/sister SHAFA'ATU S.A CHILO (Bundu Wailaru Gombe) DON MASU KARATU Imam Aliy bn AbiyDalib A.S Yace: ((Farkon Addini -shine Saninsa -Allah-...)) NAHJL BALAGHA H1 Bayan abban ya shiga gida ne, umma ta fara masa maganar ko waye yazo yace mata: Baban marigayi ne, amma ki kira mini yarinyar nan! "Jameela! Jameela!! Jameela!!!" Umma take ta fada a yayin da ta nufin dakin da jameela take. Tayi ta kwalla mata kiran ne a lokacin tana sallah shi yasa bata amsa ba, umma tana shiga dakin sai ta ganta tace: to idan kin idar abbanki yana kira, tana fadan hakan kuwa sai ta koma ta sanarwa da abba sannan ta zauna a gefen sa a kan taburma. Ba tare da wani bata lokaci ba kuwa sai ga jameela ta fito ta durkusa ta masa sannu da dawowa ya amsa cikin fara'a sannan ya mata nuni data zauna a gefen ummanta, ai kuwa tana zama sai abban nata ya fara cewa: Yanzu haka alhaji muhammad deba ne yazo min wato baban marigayi mijinki sulaiman, sannan ya bani wannan yace hakkin kine a baki, kudi ya ciro masu yawa a leda ya bude ya ajiye a gabansa. Tun bai karasa maganarsa ba jamela ta fara hawaye taso ta boye kukan iya karfinta amma ina sai da kukan ya bayyana. "Yanzu ba kuka ya kamata kiyi ba akan tuno da mijin kiba, duk da cewa kuka wata alama ce ta rahama da nuna soyayya akan wanda mutum ya rasa, duk da cewa kuka yana rage bakin ciki amma baya taimakon shi wanda akayi kukan danshi ba, kawai addu'a tana amfanar mamaci a kowani hali..." abba ne yayi ta mata wannan maganar hakan yasa jikinta yayi sanyi kalau, sannan sai ya karasa tuna mata da maganar kudin da aka kawo mata. Tace: abba bana bukatarsu tun da babu abun da na nema na rasa komai kana mini kawai ka rike su bani da bukatarsu gaskiya. "A'a jameela wannan hakkin kine kawai dai kice masa ya ajiye miki su nan da wani lokaci tun da zaki iya bukatar su ko wani lokaci" umma ne ta fadi hakan inda tana maganar tana fuskantar jameelan. Jameela tace: to abba ka ajiye su agunka! yace to shikenan jameela allah ya miki albarka tashi kije ciki, ai kuwa hakan tayi ta shiga ciki. Ta kunna wayarta ta hau yin sana'ar kullum (facebook) tana hawa kuwa sai taga ikilima a online hakan yasa ta mata sallama har ta roketa akan ta taimaka tazo mata su wuni man ta nuna mata ba komai idan har gobe abba ya barta zata zo. **** **** **** Da washe garin ranar talata ne wanda yayi kwana goma na dawowar jameela gida da safe ta nufi dakin abba dan ta gaishesu a lokacin da su yusra kuma sun maida bacci. "Assalamu alaikum" jameela ta fada. "Wa'alaikumus salam" kara so mana, abba ne ya fadi hakan bayan ya gane muryarta. Tana shigowa ta durkusa ta gaishe shi da fulatanci ya amsa cikin kulawa da nuna soyayya, sai jameela tace: abba ina sone yau naje ziyara gidan su kawata iklima matar musa! "Jameela baki da matsala zaki iya zuwa
Chapter 8 · 0% Book details