Sashe 1
Auren Wucin Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Root Entry WordDocument 0Table Data AUREN WUCIN GADI Page 001 Na Usman Umar Gombe (Babangida Ustazu) Call/WhatsApp 08137017208 Na Sadaukar Da Wannan Shafin Ne Ga Al-ummar Jahar Gombe da Kewaye Bismilllah... Sanye Take Cikin Jar Atamfa Holland Wacce Tayi Matukar Karbarta Tayi Kyau Sosai Kamar Dan Ita Akayi Atamfar, Ta Kashe Wani Dauri Wanda Zaka Iya Ce Masa Ture Kaga Alkhairi amma tayi shi mai tocila yana kallan Kudu maso gabas gefe guda ta daura shi, Tana Sanye Da wasu takalma bakake masu dan tudu kadan, kana gani kasan sun karbe ta, ta sanya wani agogon da mata suke sanyawa shima dai janne kalar atamfar ta, Ta feshi jikinta da turarurruka na alfarma wani turaren body spread ne wani kuma turaren fesawa a kaya, kamshi ya riga daya bulbule gidan gaba daya A daidai lokacin da take ta kokarin jerawa babban masoyinta wato mijinta Sulaiman abinci, saboda sanar da ita da yayi akan cewa yau zai shigo garin gombe da kamar misalin karfe biyar na yamma, Zai dawo daga kaduna saboda sun samu hutun karshen shekara a agurin aiki amma sai ya sanar da matarsa tun saura kwana biyu yace mata ranar asabar da kamar misalin karfe biyar zai shigo hakan yasa ta shirya masa liyafa na musamman saboda yadda take shauki da mararin ganin ya dawo saboda tsananin soyayyar da take tsakanin su, Tun Daga Safe Ta Kira Sale a waya ta sanar masa Da irin cafene da zai mata, sale kani ne ga sulaiman daman tun lokacin da yayi aure yace mata idan tana bukatar tayi aike ta kira shi a waya zai zo yaje mata, saboda haka ne ma yayan nasa ya saya masa wata sakan din kasea saboda wannan aikin. Yana zuwa gidan yace: Anty jameela ina kwana ? Ta amsa masa da: Lafiya kalau sale kasan cewa yau yayanka zai dawo gida kuwa ? yace: A'a Wallahi bai sanar min bama ! Tace: Cefane Zaka je kamin na musamman. Sale Yace: haba anty jameela, wani wahalar da kanki zaki yi, ki bari kawai mana ya dawo ya kaiki hotel kuyi Lunching a can! Tace: Masa kawai kai dai ka rabu dani Ga can ATM dina kaje ka cire iya yadda zai isa. Sale Yace: Anty Jameela mai dina ma fa yayi kasa. Tace: to ka dauki dubu biyu kasa. Ta miko masa wata takarda wanda a jiki ta rubuta masa duk abun da take da bukata na daga kayan masarufi da zai sayo mata. fitar sa keda wuya bai dade ba sosai ba kusan kamar awa biyu sai gashi ya dawo da kaya niki-niki tare da wani yaro daya rike masa kayan a bayan mashin. Yana gama bata kayan da ya sayo matan ne ita kuma ta fara aikin sarrafashi, Ta dauko fulawanta ta fasa koyaye ta shirya masa Shash kabab, saboda ta taba yi masa ya sanya shi santi, Tana gamawa dashi ta dauko blandern ta ta markada strawberrynta ta shirma masa lemonsa. Ta dafa masa Dan wake kuma ta yanka masa dafaffen koyi akan saboda ya kara armashi, saboda tasan yadda yake bala'in son dan wake a rayuwarsa, ta dauko kazanta ta gida ta jara ta masa dahuwar kazan larabawa saboda tasan baya cin kajin Bitnary. bayan ta gama shirya su akan dinning table kai kace abincin mutum goma aka ajiye wa, ita a tunaninta kowwan ne sai ya taba, Karfe biyar takawo kai ita kuma tana ta dauki akan bazata kira shi ba, sai dai yazo yaga bazata, Taga karfe biyar tayi kai har shida shiru bataji motsin saba hakan yasa ta yanke shawarin kawai ta kira shi a waya ta tambaye shi ko lafiya bai iso ba ta dauko wayar sanda tazo har kan sunansa data rubuta MAI SANYI NA Da manyan bakake, Sai tace a zuciyar ta wata kila ma yana bakin terminus Sai ta fasa kiranshi, akan kawai bari tadan jira kadan ta rinqa jeka-ka-dawo tsakanin ciki da falo tana cike da tunane-tunane ta saka wannan ta sunce wancan da taga ta gaji sai ta je kan kujerar dinning table ta zauna ita daya zamanta keda wuya sai taji ana kiran sallar isha, sai a lokacin ma ta tuno ashe ma batayi magriba ba, take ta tashi da sauri ta dauro alwala ta gabatar da sallar magribanta sannan ta hada su da isha, ita a tsammaninta kafun ta idar da sallahr zataji shigowar gogan nata, amma shiru kake ji kaman maye yaci shirwa Take ta fara neman wayanta dan tama manta ina ta ajiye shi take ta shi taje tahau duba kan gado, amma bata ganta ba taje bandaki inda ta dauro alwala amma sai wayan nan tace mata dauke ni ta tafi kitching ta fara bude-buden kwanuka sai dai nan din ma shiru babu labari bakin ciki ya cikata ta juya zata tafi daki daga kitching sai kawai taji wakar (Mai Gadon Zinari) Na tashi A Falonta akan dinning table, Nan take sai ta tuno ashe daga kan dinning din tayi bandaki dan dauro alwala, Kafun ta isa ma wayar ta katse tana zuwa da gudu hannunta na bari ta dauko wayarta tana duba sai taga missed call wanda take tsammanin ne, Dan MAI SANYI NA tagani kawai sai ta kira wayar tana fara ringing ya daga yana dagawa sai yaji ta fara masa kuka irin na sakalcin nan mai kashe jikin duk da namiji mai saurarensa. Sai yace: Dakata sarkin kuka kiyi hakuri! kiyi hakuri, kin san yanzu haka ina ina ? tambayar da taji ya jefo mata kenam. Take cikin muryar sakalci tace masa: Nikam ban sani ba, tunda bazaka dawo ba! Yace: haba!! Yanzu haka ina kofar gidanki jira nake kizo ki bude min, amma dan allah kibar kuka saboda tare da abokina Musa nake ? Bata bari ya gama rufe bakin saba ta ruga da gudu bakin kofa tana zuwa cikin dauki ta bude kofar ina shigowa gidan bata bari ya kara saba ta daka wani uban tsalle ta rungume shi ta fara masa kuka. Tana ce masa: yanzu ne karfe biyar din naka tayi ko ? Duk abun da takeyi ta ma manta da akwai wani abokinsa agun shi kuma musa tsayawa yayi yana kallonsu da yaga abun bana kare bane, sai yace: Abokina nikam Bari na tafi kar amin tarar letti tunda naga abun naku bana kare bane. Take Sai jameela taji wani uban kunya ya kamata ta sake sulaiman a hankali Cikin jin kunya ta juya tace: Malam musa ina wuni ? Yace: Lafiya. Bai kara ce mata komai ba daga nan KASH MU HADU A PAGE 002 AUREN WUCIN GADI Page 002 Na Usman Umar Gombe (Babangida Ustazu) Call/WhatsApp 08137017208 Na Sadaukar Da Wannan Shafin Ne Ga Kawa Ta Gari FATYN MAMAN FATY (Ceceniya Bayan Tike Gombe) #ToDayIsMyBirthDay @21 Tun lokacin data hadu da sulaiman to tare take ganin su da musa, tana jin kunyar musa sosai saboda mutum ne kamili mai addini da son sada zumunci dan haka tun kafun ta auri sulaiman take matukar jin kunyar abokin nasa. sulaiman yaga shirun nan bana kare bane sai yace: Idan kun gama jugum-jugum din sai mu shiga ko ? Nan take ta karbi Jakar mijin natan wanda yake hannun abokin nasa suna shiga ciki tace yanzu kam sai ka shiga kayi wanka ka fito kazo kaga irin tarbar dana maka, daga nan kuma sai ka bani tsaraba na. Yace: to zumudi naji, Aboki na kaje ka zauna ta baka labarin mai ta dafa mana. Musa Yace: A'a Ni a Suwa ? Nama Isa kadai kawai kaje ka fito nima na samu na tafi dan kar amin taran latti a gida. Sulaiman yace: Ka ganka ko ka fara ko ? Nikam ko ka dawo Mijin tace ne Sai abun da maman Sajjad tace maka shi zakayi ? Musa Yace: Mijin kan tace nema! Dukka sai kuka fashe da dariya, sai sulaiman ya ruga da sauri ya shiga bayan gida dan ya watsa ruwa. Sai jameela tace: malam sai muje dinning table ko ? Sai yace: inje in miki meye ? Tace: Ah abun da yace na fada maka mana! Zama yayi a kujerar Falon Yace cikin barkwanci: Dan allah ki rabu da wannan mai zafin naki ? Tace: A'a Kul! shi mai sanyi nane bai mai zafi ba! Ai Allah ya raba mu da zafi kona wutan duniya yane, balle konan zuciya. Yace: To! Ameen tunda dokin mai magana yafi gudu! Tace: Babu wani! Suna cikin surutun sai taga ya fito tace muje ka canja kaya ko dan na tanada maka kayan sawa na musamman daman. Baima kula ta yace: Aboki na ta cikaka da cakwaikwaiwa ko ? Musa yace: nidai ban fada ba! Tashi tayi ta rike hannun sa ta jashi daki suna dariya suka bar, malam musa a falo, cikin abun da bai wuce minti biyar ba, sai gasu sun fito tare. Ganin hakan yasa musa yace: Gwanda na tashi na tafi naga kamar na hana ku shan iska ? Cikin dariya sulaiman yace: koma wani irin iska ne tare dakai zamu sha ta ? Cikin bude baki yace: na isa ma ? wane ni ? Ana cikin haka sai musa yace: Aboki ba muyi sallah ba ko ? Sai sulaiman yace: eh mana ai duk kaika jawo, tun da kaine ustaz gashi kuma ma har anyi sallahr isha kuma ko magriba bamu yi ba! Sai Musa Yace: A to ba komai sai mu hada su muyi su! Sai a daidai wannan gabar jameela tasa baki tace: Amma malam hakan ba laifi bane ? Sai Musa yace: Eh mana ba laifi bane ana iya hada sallah dan annabi S.A.W.A shima ya hada sallah a wasu hadisai. ZANYI AMFANI DA WANNAN DAMAR WAJEN MASU BIBIYAN RUBUTU NA INA MUKU FATAN ALKHAIRI BISA SHAWARWARINKU NA ZABI NA CANJAWA WANNAN LABARIN SUNA DAGA AUREN MUTUA ZUWA AUREN WUCIN GADI SABODA DUKKA ALAQAR SU DAYA NE Cikin mamaki tace: af to ai ance, wai bakyau hada sallah sai aguri hudu sune: Idan ana ruwan sama, ko idan mutum yana tafiya, dadai sauransu. Musa cikin fara'a yace: mata eh annabi s.a.w.a ya hada sallah a koma bayan wadannan lokuta akwai hadisai daban-dabam da suka karfafi hakan Domin lokaci azahar da la'asar lokaci kusan daya haka nan magriba da isha. Sulaiman yace: kafun ku gama