← Book details auren shehu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 34

Sashe 7

auren shehu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Inda Iyayen yara su ka zubawa Zainab Idanu ba tare da sun tanka mata ba, yaran kuwa matsawa su ka yi kusa da ita suna kokarin taba akwatin ta, Zainab ta matsar da shi cike da kyamkayamin yara, ba ta ankara ba daya daga cikin yaran ya kai hannun sa kan wayar da ta har ya na taba hannun ta, cikin tsawa Zainab ta furta

"Stay away from me stupid boy kawai mara kunya da tarbiya! Sai na ci uban ka wallahi!!!!"

Yaro yayi baya da sauri haka ma sauran yan uwan sa, wanda daga baya su ka sanya dariya su na mai tafa hannu sanadiyar karar rashin chajin da wayar Zainab ta yi ta na mai kawo wuta. Zainab na girgiza kai ta ce

"Innalillahi wainnailaihi rajiun!"

Ta na ja akwaitin ta ta nufo iyayen yaran in da su kuma suka fara ja da baya, yara kuma ba su fasa shafa akwatin Zainab ba, inda ta ke kokarin hana su ta hanyar jijjiga akwaitin, ce mu su ta ke

"Dan Allah ku taimaka, ku min magana ko na sami sauki"

Ga mamakin ta sai ji tayi sun fara mata magana amma da fulatanci, a fusace Zainab ta ce

"Dallah ku yi min hausa ba na jin yaren da ku ke min! Sokwaye kawai!"

Maimakon ta ji hausan da ta ke bukatar ji, sai ma dada yara mata su ke cikin yaran fillo. Hakan ya sa Zainab fusata, ta na jan akwaitin yayinda ta ke dingisawa ta bi hanyar da ta ji ta kwanta mata ta na tafe yara na biye da ita suna tafa hannun ganin yanda Zainab ke jan akwaitin ta mai taya ne ya fi burgesu, tafi su ke suna fadin

"Kado! Kado! Kado! Kado"

Haka kuma masu kiriniyar cikin su ba su fasa kokarin taba akwati da wayar Zainab ba, haka su ka mayar da ita tamkar zararriya yayinda hawayen bakin ciki ya cika fal idanun ta. Fadi ta ke

"Madness! Mad people everywhere! Wallahi zan ci uban ku! Shegu 'ya'yan asara!"

Usman kuwa tun sassafe ya tafi fadar shi da ke can gefan bukkokin Rugar Shehu. Zaune ya ke da dattawan gari da kuma matasa, kasancewar shi ne ranar zaman fada na farko tun tafiyar Usman ya sanya babu wanda ya je kiwo ko gona, kowa ya hallacci zaman. Maganar Zainab kowa ke son ji daga bakin Zainab, Amma shakkar Usman ya sa su kasa bude baki su tambaye shi.

Zaune su ke kan tabarma karkashin katuwar bishiyar mangaro da ta yi mu su lema, Usman sanye cikin farin yadi da farin rawani wanda shi ya banbantashi da sauran jama'a da ke sanye da kayan saki, a matsayin shi na Shehu.

Ana tattaunawa ne akan sabbin tsari da dokokin da Usman ya kawo wanda za su shafe wanda su ke yi a da, sun hada da wajabta sanya mayafi ga duk wata mace baliga, dena shiga sassan da ba na iyalin ka ba kai tsaye ba tare da neman iso ba, dena koyar da karatun surkulle in da za a musanya shi da karatun qur'ani zalla.

Tun daga nesa ya hango ta tafe, yara da iyayen su biye da ita, haka shi ma Muhammadu Bello wanda ke zaune gefan Usman ta hannun dama ya hango ta, tun daren jiya ya ke fargaban tashin Zainab, ilekuwa sai ga abin da ya ke tsoro na faruwa. Usman na mai aje takardar da ke hannun shi ya tsaya cak yana tsimayin karasowar ta, haka ma sauran yan fada wanda su ka lura da inda hankalin Shehun na su ya tafi, su ma su ka zubawa sarautar Allah idanu yayinda Zainab ke dada matsowa gare su.

Tun da ta hango mutane zaune zuciyar ta ke Allah Allah ta karasa gaban su kila ta samu masu hankali ciki, idan har ta damu da zugin azabar da kafarta ta ke mata, ba ta nuna ba, sai dai dinkishin da take yi ne zai tabbatar da azabar da ta ke ciki. Ganin wani zaune tsakiyar mutanen, da kuma yanda shigar sa ta banbanta da na su ya tabbatar ma Zainab da shi ne shugaban Rugar, cikin fatan neman doki ta karasa. Zuciyar ta daya ta fara kokarin kutsawa ta cikin tarin mazan domin karasawa ga Shehu ta na fadin

"Ku matsa dallah! Malam matsa dallah!"

Duk da ba dukanninsu ne su ka fahimci abinda ta ke fada ba, ganin yanda ta tasar mu su da sauri su ka dara mata hanya, suna mai binta da kallo cike da mamaki har ta kai ga gaban Usman, idanun ta kan yaran da tun da su ka iso gaban Usman kowa ya nutsu kamar ba su ba ne su ke mata tafin atile ba, Zainab ta ce

"Kai ne shugaban wannan shedanun yaran da mahaukatan Iyayen su....."

Juyowa da ta yi ta kalli Usman wanda lafazan Zainab ba karamin tunzurashi yayi ba, ya tashi tsaye haka ma sauran yan fada su ka yi yunkurin tashi amma ya musu alama da hannu da su zauna. Zainab na girgiza kai ta ke nuna shi da dan yatsa, tsayin shi, fadin shi, da idanun shi ne ya kara tabbatar mata da Usman din ne, Abu na farko da ya tsirga zuciyar ta shi ne zaton ta ya tabbata, Usman ya cika dan garkuwa da mutane, gashi ya dauko ta duk da ta kasa tuna yanda aka yi . Cikin faduwar gaba ta saki akwatin hannun ta yayinda ta zube kasa, ta zauna dirshen ta na duban kasa tamkar mai nazari.

Yanda Zainab ta firgita da ganin shi, da kuma yanayin da ganin na shi ya sanya Zainab ciki ba karamin faranta ran Usman yayi ba dan a tunanin shi ta karaya ne. Jin Zainab ta furta

"Ya aka yi ka kawo ni nan? Menene dalilin ka na kawo ni nan?"

Usman ya tsaya ya na duban ta kamar yanda sauran jama'ar su ka zuba mata Ido. Ganin be da niyar amsa mata ta tashi a fusace dan masifa ma mancewa ta yi da kafar ta, sai da ta taka kafar ta cije lebe cike da azaba, ta na dingisawa ta karasa gaban Usman hannu a kugu take magana cike da tsiwa

"Dan ka na dan garkuwa da mutane ba wai zanji tsoran ka ba ne! Tun ranar farko da na dora idanu kan ka na san kai wanene! Dady ka yaudara har ka masa rufa ido ya kasa gane kalar ka! Haka Anty Sauda da Ammy su ka ki yarda da ni akan a min katangar karfe tsakanina da mugu irin ka! Nawa ka ke bukata? Nawa ka ke bukata ka mayar da ni gidan mu?? matsiyaci kawai!"

Ganin yanda Zainab ke yiwa Shehun su magana cikin tsawa da tsiwa ne ya sa matasa tashi tsaye cikin fushi suna mai yiwa Zainab ihu, da harshen fulatanci su ke fadin

"Karyar ki ta sha karya kado! Ki tuba ko kuwa muna tasar miki da bugu"

Ganin haka Zainab ta yi baya a tsorace kamar mai shirin ranta a na kare. Usman ya daka mu su tsawa cikin harshen fulatanci, ya ce

"Kada ku kuskura! Mata ta ce! Ni kadai na ke da ikon hukunta ta!"

Gaba daya su ka runsunar da kai sannan su ka koma wajan zaman su suka zauna, hakan ne ya bawa Zainab damar cigaba da tsiwa duk da cikin ranta ta gama tsorata da Usman, tsoran ne ba ta san nuna masa gudun kar hakan ya bashi damar cutar da ita, cikin karfin hali ta furta
"Ihun ku na banza ne dan ba ku bani tsora! Ku tambayi dan uwan ku ku ji yanda ya sha dakyar hannun sojoji!"

Usman ya kai kallan sa ga Muhammadu Bello, wanda ya kawar da kai gefe yayainda ya tuna kashin da ya sha a barikin soja. Cikin danne zuciya Usman ya mayar da kallan sa ga Zainab, wacce ba ta gushe ba ta cigaba da fadin

"Wallahi tun kafin na sabar maka ina mai baka umarnin ka yi duk yanda ka yi na wayi gari a nan ka mayar da ni makaranta! ba na san iskanci ban da lokacin batawa jarabawa na ke Idan ba haka ba sai na lahira ya fi ka jin dadi, kai ba kai ba har wa'annan yen koran na ka"

Ta karasa maganar ta na mai nuna jama'ar wajan da dan yatsa.

Cike da isa Usman ya koma wajan zaman shi ya zauna kamar ba da shi Zainab ta ke magana ba. Daya daga cikin dattijawan ne ya kada baki cikin harshen fulatanci ya ce

"Shehu ka gafarce ni, wannan mata taka sam ba ta da tarbiya, ba ka tunanin zaman ta a wannan Ruga za ta iya lalala ta mana tarbiyar yaran mu da matan mu?"

Sauran dattawa su ka goyi bayan shi ta hanyar jinjina kai. Wani ya kara da

"Shehu duk matan da ke Rugar nan, ga 'ya'yan mu amma ka rasa wacce za ka aura sai Kado? Wacce ba ta san darajar Shehu ba bare na al'ada ba? Ji fa yanda ta tsaya kerere gaban mu muna dattawa, ba kunya bare tarbiya"

Shehu na murmushi ya mayar musu da amsa cikin hausa ya ce

"Ba a san rai na aka daura min ita ba, sadakar ta mahaifin ta ya bani! Tabbas ba ta kai darajar matan Rugar Shehu ba, dan haka kada ku damu tamkar baiwa ta ke a Rugar nan"

Yanda Zainab ta kai hannu baki ta na kallan shi tamkar wacce ta ke shirin burma masa wuka, ya sa Usman canza harshe, dama yayi hausan ne saboda ta san abin da ya ke fada, ya na murmushi yayinda mazan wajan daga samari har dattawa ke kallan Zainab cike da mamaki, matan wajan kuwa dariya su ka sa bayan Usman ya dada maimaita musu cewa sadakar Zainab aka bashi, haka kuma ba takai matan rugar su daraja ba. Cikin ihu kamar mai shirun rufe shi da duka ta ke fadin

"Ka yi hausa mana! Idan ba munafunci ba ka yi yaran da na ke ji! Ni ba sadaka ba ce! Ba zan taba zama matar ka ba! Ni ba baiwar ku bace! Bloody fool! Ka mayar da ni na ce!"

Hankali kwance Usman ya ce
Chapter 7 · 0% Book details