← Book details auren shehu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 34

Sashe 16

auren shehu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da la'asar sakaliya ya dawo ya tadda ta zaune baci ba sha, ya na mai duban kwararen da daga gani ko bude su ba a yi ba ya furta

"Halan azumi ki ke?"

Ta masa banza. Ya na mai gyara tsayuwa ya kara da

"Toh ai ko azumin ne ai na karya shi dazu Abu, ki saki ran ki ki ci abinci"

"Ba zan ci abincin ba! Ina ruwan ka da cin abinci na?"

"Ni kuwa na ke da ruwa! Idan har ba ki ci kin koshi ba ina za ki sami damar bani hakki na?"

Usman ya bata amsa ya na mata murmushin mugunta. Hakan ba karamin tunzurata yayi ba, a fusace ta ce

"Ka sake ka kara zuwa kusa da ni sai na lahanta ka Usman!"

"Zuwa kusa da ke yanzu na fara, hakki na sai kin bani! Kuma ni ba na son raguwar mace! Na fi son mace mai kuzari, Dole ki ci abinci ko kuwa na dura ma ki ta karfi da yaji!"

"Hakan nan dai! Abin da ka iya kenan! Sai ka yi mu gani ai"

"Na baki minti talatin kacal matukar na dawo ba ki ci abinci ba ki kuka da kan ki"

Cewar Usman yayinda ya fice ya bar Zainab ta na bambami. Ko da ya koma bayan minti talatin din da ya ce, ba ta ci abincin ba. Kamar yanda ya ce zai mata dure, haka ya cafko ta cikin kokuwa ya matse kafafun ta cikin na sa, yayinda ya daure hannayen ta biyu ta bayan ta da wani dan kyelle, kunun da Iyalle ta aiko mata da shi ya shiga dura mata ta karfi da yaji Zainab ta datse bakin ta ki budewa bare ma ya samu ya shiga bakin ta.

Ganin haka Usman ya sa hannu ya ruke hancin ta yanda ba za ta iya nufashi ba matukar ba baki ta bude ba, da wuya ta yi wuya sai gashi ta bude bakin, yayi saurin dura mata, cikin kokarin numfashi kunun ya shige makoshin ta har ta kusa kwarewa amma Usman be sarara mata ba, haka sai da ta kusa shan rabin kunun sannan Allah ya bata iko ta sanya duka karfin ta ta kwabar da kwaryar da kirjin ta, nan bisa tabarma kunun ya malale.
Bin kunun yayi da kallo kafin ya dawo da kallan sa bisa fuskar ta wanda yayi shabe shabe da hawaye, ya bi bakin ta da yayi dumu dumu da kunun da ta tuzur ya ganganra har wuyar ta. Ba ta ankara ba sai gashi ya fara lashe kunun tun daga bakin ta yana kokarin sauka har wuya. Zainab ta saka ihu fadi ta ke

"Allah ya isa! Allah ya isa ban yafe ba! Allah ya isa wallahi sai Allah ya saka min! Maye! Maye kawai!"

Sai da ya lashe kunun nan tsaf sannan ya sake ta ba tare da ya kunce mata hannu ba, cikin akwaitin ta ya bude ya dauko doguwar rigar ta da bumshort, ganin ya sunkuya ya na goge kunun da ya zube bisa tabarmar cikin haki Zainab ta furta

"Wai kai wani irin azzalumi ne! Tufa ta ka mayar tsumma! Wallahi sai na saka an daure ka! Bari na samu na fita daga dajin nan! Ka kuka da kan ka Usman!"
Sai da ya gama gyara wajan tsaf, Zainab ta na ji ta na gani ya watsa kayan waje sannan ya kunce ta. A hankali ya furta

"Tun da wannan rayuwar ki ka zaba, Ni ma ita na fi so Abu, ki cigaba da taurin kunne ni ma kuma ba zan fasa aikata san rai na akan ki ba, ki sani daga ni sai ke a nan, ihun ki banza gwara ma kin sadudu...."

"Akwai Allah! Allah ne zai min maganin ka!"

Cewar Zainab cikin mayar da martani. Usman na murmushi ya furta

"Ashe kin san akwai Allah Abu?"

Shiru ta masa yayinda ta ke duban sa cike da tsana, cikin ran ta kuwa alwashin ramuwar gayya ta dauka kan Usman ko da kuwa za ta rasa ran ta ta sanadiyar haka.

Rahila kuwa ba ta yi kasa a gwiwa ba ta saci hanyar zuwa neman mijin ta Tanko, har ta fara fitar da rai sai gashi zaune in da Usman ya masa mararraba da Rugar Shehu. Sam be yi mamakin ganin ta ba dama tun kafin su iso sun shiryawa Usman, sun san zai iya hana Tanko zaman Rugar, dan haka su ka yi Rahila ta mu su leken asiri, haka kuma da ta sami wani hanyar tunkube Usman ta fito ta nemi Tanko.

Cikin rawar jiki ta kwashe komai ta fada ma Tanko. Cike da jin dadi Tanko ya ce

"Biri yayi kama da mutum! Ni na ga soyayyar kwadon nan cikin idanun Usman, ko shakka babu Usman ya kasance mai rauni a kan ta. Haka kuma daga gani diyar masu daula da daukaka ce, lalle kuwa za mu jefi tsuntsu biyu da dutse daya Rahila, kin yi aiki mai kyau ina alfahari da ke"

Jin yabo daga bakin mijin ta dadi ya cika Rahila, ba su sallama ba sai da ta masa alkawarin cika masa burin sa.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, Usman da Zainab suna zaman doya da manja har tsahon kwana uku, haka kuma be mayar da ita cikin ahalin sa ba ba sai ma kwaso na sa kayan yayi, nan su ka zauna da ga shi sai ita a gidan gona. A iya kwanakin da su ka yi tare, Zainab ta gano wasu dabiu na Usman da ya sanya sam ba ta taba jin wari ko makamanci shi ba a tattare da Usman. Na farko dai Usman mai yawan aswaki ne, yayi koyi da wannan hadisin da Manzo (SAW) ya ce ba dan kar na takurawa al'umata ba da na ce su dinga aswaki duk sanda za su yi alwala, haka Usman ya ke shi ya sa ko da yaushe bakin sa ya ke wasai haka kuma ya ke da fararen hakora. Bayan wannan duk da ba a raba hammatar Usman da gashi, sam ba ta taba ji ya na bugawa ba, ta sha ganin yana shafa farin abu kamar gari a hammatar shi duk sanda yar tsokanar ta tashi ya zabi ya sanya kaya gaban ta, sai daga baya ta gano ashe alimun ya ke shafawa, har ita ma ta fara fakar idanun shi ta na dan shafawa. Batun kamanin Usman kuwa bugun zuciyar ta na karuwa duk sanda ta ga Usman ba rawani, har ta kai ta na gujewa kallan sa musammam idan be da riga jikin sa.

Ran da ta cika kwana hudu ne ta tashi da zazzabi, hankalin Usman ba karamin tashi yayi ba musammam yanda ya ga ta na rawar dari. Duk taurin kan Zainab sai da ta yi laushi, cutar ta mata mugun cafka dan har da rashin cin abinci da ta ke yi. Hatta wanka shi yayi mata a ranar, rigar nan ta saki ya sanya mata tare da rufa mata zani, kafin ya shiga daji neman magani.

Cikin kankanin lokaci ya samo maganin da su ka saba sha duk sanda su ke mashasshara, Iyalle ya bawa ta dafa masa shi tare da jan kanwa, aka hada da abinci aka kai gidan gona in da Usman ke ta kai kawo dan zama ma kasawa yayi.

Kamar yanda ta saba masa gardama, yau din ma da kyar ya samu ta ci abincin da aka aiko musu, shinkafa ne da mai da yaji. Sai da ya ga ta danci sannan ya fara kokarin bata magani, nan ma sai yayi da gaske ta sha, aje kwaryar maganin yayi yayinda da ya jawo ta kirjin sa ya rungume. Yanda ya ji ta yi lamo ba tare da ta yi yunkurin kwatar kan ta ba Usman ya tabbatar Zainab na jin jiki. Cikin rada ya furta

"Ya zan yi da ke Abu? Duk yanda ki ka bata min! Duk yanda na so na gana mi ki azaba Abu na kasa, Abu kin cutar da ni amma gashi kin shiga rai na, ya zan yi da ke Abu?"

"Ka rabu da ni na mutu ko kuwa ka mayar da ni in da ka dauko ni"

Cewar Zainab daga can kasan makogaro. Usman ya dada rungume ta kamar wanda zai mayar da ita jikin sa ya furta

"Ba zan iya ko wani daya daga cikin su ba Abu, ba zan iya rabuwa da ke ba..."

Jin haka Zainab ta fara kokarin cire jikin ta daga na shi, hakan ya sa shi kara ruko ta sosai. Ya na shafa bayan ta ya ce

"Shhhhh! Ni da ke ba mu taba samun kusanci mai cike da nutsuwa irin na wannan yanayin ba, ki kwanta kawai Abu, ki yi shiru abin ki idan kin sami sauki za mu tattauna, Allah ya baki lafiya"
Karo na farko da Zainab ta bi umarnin sa cikin kwanciyar hankali, ta na mai runtse idanu ta yi kwanciyar ta jikin sa har bacci ya sace ta.

*Khadija Sidi*
Auren Shehu 2

10

A hankali ya kwantar da ita tare da mata matashi da daya daga cikin kullin rawanin sa, ya mata addua ya tofe ta. Cikin sanda kar ya tashe ta ya wuce fada da niyar sauraran korafe korafen jama'ar Rugan Shehu kafin Zainab ta tashi.

Be yi cikakken minti ishirin da tafiya ba kukun daya daga cikin shanun gonar ya dami Zainab har ta kai ga farkawa. Duk wanda ya saurari yanda saniyar ke kuka dole ya gane ta na cikin azaba. Tun Zainab na iya jurewa a tunanin ta Usman na tare da shanu, har ta kasa ta fito, Nan ta ci karo da abin da ba ta taba gani ba tun da ta zo duniya, ba ga bil adama ba bare dabba. Saniya ce ke kai kawo, ta baro cikin yan uwan ta shanu zuwa farfajiyar bukka, duk sanda ta taka daya biyu sai ta tsaya ta na mai fitar da sauti yayinda wani farin abu ke kokarin fita daga jikin ta.

Ganin haka Zainab ta ja da baya a tsorace har ta na shirin rugawa duk da dai sam ba ta jin dadin jikin ta, kiran sunan Usman ta ke bilhakki yayinda ta duba lungu da sako na gidan gonar babu Usman babu alamar sa.
Chapter 16 · 0% Book details