← Book details auren shehu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 34

Sashe 4

auren shehu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu musu Zainab ta bi bayan shi hanun ta rike da akwatin ta, ko waige ba ta yi ba bare ta tuna da gidan su ne nan ta bari.

*khadija sidi*Auren Shehu 2

2

Zainab na biye da Usman duk in da ya sa kafa nan ta ke dire na ta. Dan sahu ya tara ba su zame ko ina ba sai tashar Kano Line amma su ka yi rashin sa'a motar Taraba ba ta tashi sai sassafe. Direba ya dubi Zainab da gaba daya alamun gajiya ya bayyana a fuskar, a zahirin gaskiya idan aka dauke mayafin fulbe da ke yafe jikin ta, sam yanayin ta da zubin ta be nuna wani alaka tsakanin ta da Usman ba, Dan kuwa kana ganin Usman ka ga bafulatanin usul wanda babu wata alamun wayewa a tare da shi. Cikin dabarar Jin ko wacece Zainab ga Usman Driver ya kada baki ya ce

"Halan mikakkiyar tafiya ka yi tare da uwargiyar ta ka?"

"Eh mikakkiyar tafiya mu ka yi, haka kuma ita za mu tasarwa, shin ko akwai irin gidan kwana da ake biya nan kusa? Sai mu kwana washagari mu dau hanya"

Usman ya bashi amsa ba tare da ya fadi abin da Driver ke da muradin ji ba. Ganin yanda Driver ke kallan Zainab ba kakkautawa ya sanya Usman fadin

"Ni ta ita na ke ji ma, a gajiye ta ke...."

Driver na mai sosa kyeya ya ce

"Toh ka ga yanda za a yi, gida na nan kusa ne, ina da daki mai dauke da gado da katifa cikin zaure, haka kuma akwai bandaki ciki, ban fiye san saukar bakin da ban sani ba ciki, Amma ganin halin gajiyar da wannan baiwar Allah ke ciki, mu je sai na ba ku shi a kan naira dubu biyar..."

"Dubu biyar be yi yawa ba?"

Cewar Usman yayinda ya kai hannu aljihun shi domin jiyo lafiyar tattalin arzikin da ke ciki. Jin haka Driver ya ce

" Kai fullo ba dai san sisi ba, toh ai babu damuwa, kawo uku toh, ai matafiyi abin a tausaya masa ne"

"Toh babu laifi, gashi nan kirga ka gani"

Ya mika masa kudin da ya fidda daga aljihun sa. Driver ya dirga dubu uku cus sun cika. Sannan ya ce

"Toh Madallah sai ku shigo mota mu tafi nan tsallake ne ba nisa, ka ga da sassafe kafin shida sai mu fito mu yi lodi mu dau hanya"

"Abu shiga gidan baya mu tafi"

Cewar Usman cikin dakiya. Jin Zainab ta furta

"Toh Shehu mijin na"

Ya sanya Driver sake waigawa ya kalli Zainab kafin ya shiga motar ya tada cike da mamaki, ya tabbata dai wannan gabjejen bafulatanin Ruga majin wannan kyakkyawar yarinya ce, Driver ya dau hanya ya na al'ajabin yanda Usman ya tsinci dami a akala.

Kamar yanda Driver ya fada gidan na sa be da nisa da tashar. Dakin da yayi alkawarin bawa su Usman ya sauke su, babu laifi dakin be fiya dauda sosai ba, gadon gyare ya ke tsaf haka kuma kasan dakin shimfide ya ke da leda. Haka kuma akwai wutar lantarki. Daudar dai daya ne na rashin shara da dakin be samu ba. Shi ma din kafin su shiga Driver ya turo yaro daga cikin gidan sa aka share, tare da cire zanin gadon da ke shimfide bisa gadon, ya shimfida wankakken sai kamshin sabulun wanki ya ke, Sannan ya sa aka kunna mu su maganin sauro na igiyar leko, ya kuma debo ruwa ya zuba a robobin cikin bandaki. Yaron na shirin fita Usman ya tambaya ko akwai in da ake siyar da abinci nan kusa? Yaro ya ce babu sai dai akwai wajen me shayi ya na Kuma dafa indome. Usman na mai godiya ya sallami yaron da sauri saboda yanda wayar Zainab ta ishe su da kara. Ya na duban Zainab wacce ga wayar a hannun ta amma ta kasa dagawa saboda be ba ta izini ba.

"Waye ke kiran ki?"

Ko da ta duba wayar 'Ammy na' ta ga an rubuta, budar bakin ta sai cewa ta yi

"Wani suna ne wai Ammy na, haka dazu ma wasu su ka ta kira ban san su ba"

Zainab ta bashi amsa a sanyaye.

"Ki tura mu su sako na lafiyar ki lau, kada a sake kiran ki"

"Toh Miji na Shehu"

Cewar Zainab yayinda ta aikata umarnin sa. Yanayin gajiya da ta ke ciki da kuma yanda surkullen da ya mata ya kamata sam be saka tausayin ta ya tsirga zuciyar Usman ba, sai ma tsananin kiyayyar ta da ya ke ji cikin ran sa, da kuma bakin cikin da ke ziyartar zuciyar sa a duk sanda ya tuna ita ce sanadiyar rashin ganawar karshe tsakanin sa da Iyar sa.

"Ki kashe wayar kada ki sake kunna ta, zan fita na siyo abinci"

Cewar Usman cikin kokarin ficewa daga dakin, har ya kai kofa ya sake juyowa ya kara da

"Ki jawo kofa ki sa sakata idan na fita, kada ki budewa kowa idan ba ni ba ne, Ki yi wanka da sallah idan har ki na yi......."

Ya na jiyo amsar ta na

"Toh Miji na Shehu"

Ya fice zuciyar shi na tafasa na ba gaira ba dalili, shi kan shi ya san iya yan watannin nan gaba daya baya cikin hayyacin sa, babu abin da ke masa ciwo sai rashin Iya, yanayin da Bello ya shiga a sanadiyar Zainab da kuma dukan kawo wuka da aka yiwa Bello, duka a sanadiyar auren Zainab.

Bayan tafiyar Usman Zainab ta sa sakata kamar yanda Usman ya umarce ta, cire kayan ta tayi, tare da daura dan karamin towel din da ta saka cikin akwaitin ta. Cike da kyamkayami ta shiga bandakin, ba ta yarda ta tsugunna ba gudun daukar cutar bayan gida. Har ta gama wanka ta dauro alwala Usaman be dawo ba. Wata rigar baccin ta saka iya gwiwa mai dan karamin hannu sannan ta sanya hijabi har kasa ta shiga gabatar da sallah.

Idawar ta ke da wuya ta cire hijabi kan ta daure da kallabi ta ji ana buga kofa, ta karasa gaban kofar tare da fadin

"Waye?"

"Shehu"

Ya bata amsa a taikaice. Cikin rawar jiki ta bude kofar tare da fadin

"Sannu da zuwa"

Hanun sa rike da bakaken ledoji guda biyu, da kofi wanda ke fitar da turirin zafin bakin shayin da ya ke ciki ya wuce ba tare da ya tanka mata ba. Sai da ya aje ledojin da kofin shayin sannan ya daga ido ya kalle ta, tuni yayi saurin kawar da kai, cikin mummunar faduwar gaba, kan sa ya sara ganin yar rigar da ke jikin ta, da kuma yanda ya bayyana surar jikin ta duk da dai rigar ba matsattsiya ba ce, Zainab din ce MashaAllah. Cikin tsawa da fada ya ce

"Me ki ke jira a nan Abu? Ki rufowa mutane kofa ki zo ki saka hijabin ki! Kada ki sake yawo haka matukar ina wajen!"

A gigice Zainab ta rufe kofar tare da sa sakata, ta karasa da sauri hannu na rawa ta dau hijabin ta ta saka, can gefe ta sami waje ta zauna har lokacin gaban ta be bar faduwa.

Jin ta shiru ya dago kai ya dube ta, ganin yanda ta zauna ta yi shiru kamar ba tsigalalliyar Zainab din da ya sani ba, da Kuma kwallar da ta ciko idanun ta be sa yayi dana sanin ihun da ya mata ba, sai ma danasanin ganin surar ta da yayi da har lokacin ya ke masa yawo a idaniyar sa. Murya ya gyara ya na mai neman nutsuwar karfi da yaji, ya mata nuni da yatsa tare da fadin

"Ki zo nan ki ci abinci ga shayi nan shi za ki fara sha kin ji ko?"

Ya na maganar ne cikin dakiya. A hankali ta taso ta zauna in da ya umarce ta, shi ne ya bude mata ledar indomie din, yanda ya ga ta na ci hannu baka hannu kwarya ya tabbatar masa da cewa da yunwa ta wuni. Na shi ledar ya ja dan kuwa ji ya ke ya na bukatar kaɗaicewa a wannan lokaci, a hankali ya ja jikin sa ya fita ya bar mata dakin. Bakin kofar dakin ya zauna duk yanda ya so ya ci abinci ya kasa, tunani kala kala ke yawo cikin kwakwalwarsa, sam be da niya kuma ba zai yi danasanin tafiya da Zainab ba! Hakan shi ya fi cancan ta mutane irin ta!'

Furucin da zuciyar sa ke jaddada masa kenan har ya dan sami karfin gwiwar cin indomie din. Haka ya zauna a soro, 'ya'yan Driver na kai kawo haka na makota, har kafa ta dauke aka ma rufe gidan gaba daya. Nan soro cikin sauro ya kwana, da asubar fari ya buga mata kofa, ya ce ta tashi ta yi sallah ta yi wanka za su wuce.

Sai da aka idar da sallah sannan Zainab ta yi wanka. Ta na jiyo shi shi ma yayi na sa wankar tare da goge baki da dakakken gawayin da ya kullu tun daga Rugar Shehu. Cikin bandakin ya shirya tsaf ya fito cikin kayan saki riga da wando, haka kuma be fasa nada rawanin sa da bakin yadi ba. Ya na mai duban shigar da ta yi na bakar duguwar riga ya ce

"Ki cire kayan nan ki sanya hijabi"

Ga mamakin sa sai ga Zainab na kokarin zare ruga gaban sa, cikin tsawa ya ce

"Wai ke wata irin mara kunyar Bingel ce Abu???"

A dibirbice dan kuwa tsawar Usman rikita ta ya ke ta ce

"Ya zan yi miji na? Kai ka ce na cire rigar..."

"Mace da kunya aka santa duk da na dade da sanin ke ba ki da ita ko na miskala zarratun! Idan kin ga dama ki yi tsirara kafin ki saka hijabin!"

Ya na gama fadin haka ya bude kofa ya fice. Zainab ta yi kasake ta na kallan sa cikin tunanin laifin me ta yi har ran Mijin ta Shehu ya baci haka. Jin ya na buga mata kofa ta yi saurin saka hijabin haka ba tare da ta cire rigar ba, ta hade komai na ta cikin karamin akwatin ta ta fito.
Chapter 4 · 0% Book details