← Book details auren shehu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 34

Sashe 27

auren shehu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammy kuwa kuka ta saka ta salati, cewa ta ke

"Innalillahi wainnailaihi rajiun! Innalillahi wainnailaihi rajiun!"

Anty Sauda ta kara da

"Sai yanzu ki ke da bakin salati? Ai dama aka ce wanda be ji bari ba ya ji hoho, mu ka yi mu ka yi ki dakile auren nan ki ka min kunne uwar shegu! Ai ga irin ta nan! Kai idan har ba a kama min yaran nan ba ban isa Sauda ba! Likita mu na so a cire cikin nan da gaggawa....!"

"Babu wanda zai cire min ciki!"
Cewar Zainab a fusace. Hakan ya sa su Anty Sauda sakin baki su na kallan ta. Ba ta gushe ba ta kara da

"Cikin shege ake zubarwa ba na halas ba, dana dan halas ne kada wanda ya kara aibata min ciki bare ya tsinantar min da shi! Idan har wahalar hanya be zubar min da ciki ba, ban ga dalilin da zai sa wani mahaluki ya taba min shi ba!"

Ta na gama fadin haka ta tashi fuuuu ta fice ta bar Anty Sauda da salati da sallallami ta na tafa hannu. Fadi ta ke

"La'ilahaillahu muhammada rasulillahi! Hajja Aleesha wannan yarinya ba cikin hayyacin ta take ba! An riga an juyar da kan ta sai mun dage da addua!"
Ammy kuwa rasa ta cewa ta yi, dama dai in tsiwa ne kadan daga aikin Zainab, mamaki daya shi ne ikirarin da ta ke akan cikin ta,
"Allah dai ya sa ba cikin hayyacin na ta take ba...."

Ammy ta fada a sanyaye.

"There is no two ways about it! Ki ma dena raba dayan biyu ba cikin hayyacin ta take ba, sai an yi rokan Allah!"

Cewar Anty Sauda. Da haka su ka yiwa Likita sallama su ka tafi. Cikin mota su ka tadda Zainab zaune ta hada girar sama da na kasa. Babu wanda ya tanka ta sai bayan da su ka isa gida sannan Anty Sauda ta saka ta a gaba da tambaya. Zaune su ke a falo, sun zagaye Zainab kamar suna gudun za a iya sake sace ta
"Za ki gane wanda ya dauke ki? Wannan tsinannan almajirin ne ko?"

Zainab ta mu su banza. Anty Sauda ta kara da

"Yakura mun san abin da ciwo, matukar ba ki budi baki kin yi magana ba ta yaya za mu iya kwato mi ki hakkin ki daga zalincin da aka aikata mi ki? Ki fada mana ya aka yi ya sace ki, Kuma ina ya kai ki, ya sunan garin...?"

Zainab ta ki amsa ta. Cikin nuna gajiyawa Anty Sauda ta furta

"Ina ga sai dai sojojin nan su tambaye ta kila su ta fada mu su, in ba haka ba Hajja Aleesha sai mun tsaya tsayin daka akan Yakura! Wannan almajirin ya asirce ta ya kuma breaking din ta...."

"Ba zan yi magana da kowa ba!"

Zainab ya katse ta a fusace. Ba ta gushe ba ta kara da

"Kada ki kara kiran miji na da tsinannen almajirin! Usman miji na ne! Eh shi ya dauke ni saboda shi aka daura min! Da zai kai ni ya gusar min da hankali, Amma da ya tashi sallama ta da hankali na ya sallame ni, na roke shi ya sake gusar min da hankali na ko zuciya ta za ta dena min radadin barin sa, ya ki! Yanzu ya sa na dawo gida amma zuciya ta na can tare da shi, Kuma ku bar tunanin addua, cikin hankali na na ke, kuma Anty Sauda zan so ki sarara min dan kuwa maganganun ki kan miji na suna neman yin tsauri dayawa!"

Shiru ne ya biyo baya tamkar wanda ruwa ya cinye, inda kunyar yanda Zainab ta watsawa Anty Sauda kasa a Ido ya rufe Ammy, Anty Sauda kuwa ji ta yi tamkar kasa ta tsage ta shiga. Tashi Zainab ta yi ta shige ciki, bayan tafiyar ta Ammy ta nisa ta ce

"Tabbas Yakura ba ta cikin hayyacin ta, ya asirce ta yayi..."

"Hmmmm kin ga Hajja Aleesha matukar ba Yakura ce da kan ta ta zo ta same ni ta ce min ba cikin hayyacin ta take ba na yi hakuri, wallahi na cire hannuna a kan maganar ta, ke hatta General ma zan fada masa babu ruwan sa....."

"A yi haka Hajja Sauda? Ai hannun ka ba ya rube ka yanke ba ko?"

Anty Sauda na girgiza kai ta furta

"Ah ah Hajja, a dai yi mata addua, matukar ba ta canza ba toh tabbas ki cire rai akan ta kema, ki sa a ran ki babu Yakura. shikenan ya tsafe ta har abada"

"Innalillahi wainnailaihi rajiun!"

Cewar Ammy ta na mai sharar kwalla. Nan Anty Sauda ta barta, cike da bacin rai ta shige ciki tare da kiran mijin ta ta sheda masa halin da ake ciki.

*****

Bangaran Rugar Shehu kuwa, Muhamadu Bello ya tadda Usman tamkar mai makoki, cikin kankanin lokaci ya canza gaba daya. Zaune su ke karkashin bishiya in da Bello ya zo ya tadda shi bayan dawowar sa.

"Idan har ka na kaunar ta haka da ba ka bari ta tafi ba Shehu, domin kuwa Uwargida na kaunar ka ita ma, wallahi halin da ta ke ciki ya sanya na kasa barin ta har sai da na kai ta har Taraba, na bar ta a cikin wani hali"

Maimakon ya bashi amsa daidai da maganar sa, sai cewa yayi

"Ina nan a kan baka na na barin Rugar Shehu sati mai zuwa in Sha Allah, zan shiga uwa duniya kamar yanda na taba shiga a baya, Amma wannan karan hanyar neman cigaban Rugar nan ce zai fitar da ni"

Ya dan dakata kamar mai nazari. Muhamadu Bello ya nisa, kana ya ce

"Duk da ba haka aka so ba, Amma ka riga ka yanke hukunci ba tun yau ba. Ka ga Kado ba su da amana akan dukiya ko neman ta, akwai wani bafulatani dan uwan mu, Ibrahim Yerima Balla, dama mun saba cinikanyar shanu da shi, mutumin birne ne kwarai amma sai amana, ya kuma san darajar dan Adam. Nan Yola ya fiya zama duk da ya ce min ya na da gidaje a Kano da birnin tarayya, me zai hana idan ka tashi tafiya na hada ku?"

Bayan Usman yayi dan tuntuntuni ya furta
"Ka na gani zai iya saka ni hanya Bello? Ni fa yanzu tsoran bil'adama na ke"

" Mutum abin tsoro ne, Amma kada ka damu na shedi Ibrahim, ba ya cutarwa"

"Toh Alhamdulillah, zan shedawa su Kawu Iliya, sati mai zuwa sai mu tasarwa Yola, zan fara tafiya da shanu dari biyu mu gani, idan da bukata wasu nan gaba sai na yo aike"

Da wannan shawarar Usman ya bar Bello ya tinkari su Kawu Iliya. Dan kuwa shi ma ba zai iya jure zaman Rugar Shehu ba bayan tafiyar Zainab, komai na Rugar tuna masa da ita ya ke, sai ya zama tamkar zuciyar ta na ma zuciyar shi fatalwa. Ji ya ke kamar ya bi ta Kanon ko ya sami sauki, Amma taurin kai ya hana, shi ya sa ya yanke hukunci shiga duniya ko ya sami sauki.

******

Babu irin adduar da Ammy ba ta sa an yiwa Zainab ba, islamiyoyi da makarantur allo ta saka aka kai sadaka in da aka sa yara sauka da zikiri. Amma Zainab ko gizau, ta tsaya tsayin daka babu mai zubar mata da ciki.

Bayan sati guda da dawowar Zainab, da la'asar Zainab zaune bakin gadon ta dake tashin ta daga bacci kenan, kamar yanda ta saba ta yi mafarki da Usman, takaicin farkawar da ta yi ne ya sanya ta zaman bakin gado tare da doka uban tagumi.
A hankali aka kwankwasa mata kofa, sanin ba za ta amsa ba ya sa suka bude kofar su ka shigo, Ammy ce a gaba, biye da ita Anty Sauda ce da Halitta. Halitta ta zauna kusa da ita, in da Ammy da Anty Sauda ke tsaye suna duban ta. Cike da damuwa Ammy ta furta

"Yakura wannan tunanin da bakin cikin da ki ke ciki zai iya lahanta ki da dan cikin na ki, me zai hana ki bi Antyn ki ku koma Maiduguri, can zai fi mi ki kwanciyar hankali kafin ki samu ki koma makaranta....."

"Babu in da zani, ba kuma zan sake komawa makarantar ba, Nan zan zauna abu na har sai na haihu, idan kuma zaman nawa na damun ki Ammy sai na sami ko da gidan haya ne....."

"Ah ah Yakura"

Ammy ta yi saurin katse ta. Ta kara da

"Nan din ai gidan uban ku ne, ku ne magada dan ko da aka raba gadon Malam gidan a naku ya fado ina kuma batun neman haya? Kuma ina ki ka taba Jin zaman diya a gida ya dami uwar ta, dama farin cikin ki shi ne fatan mu...."

"Usman shi ne farin ciki na Ammy, rashin shi shi ne sanadin bakin ciki na, idan har kuna so ku sake ganin walwala ta a duniya ku barmin ciki na na haife shi, ban da makiyin da ya wuce wanda zai yi yunkurin raba ni da ciki na, wannan cikin shi ne rayuwa ta....."

Dan takaici Anty Sauda kasa magana ta yi ta juya ta fice fuuu tamkar za ta tashi sama. Ammy na mai dafa kafadar Zainab ta furta

"Na mi ki alkawari Yakura babu wanda zai sake cewa ki zubda cikin nan, Allah ya raba lafiya"

Ta fice jiki a sanyaye. Ya rage da Halitta sai Zainab cikin dakin. Shiru su ka yi kowannan su na sakar zuci, daga bisani Halitta ta furta

"Yakura?"

Halitta ta kira sunan ta a hankali. Zainab ta daga ido ta kalle ta. Karo na farko da su ka zauna tare cikin aminci ba tare da Zainab na neman ta da bakar magana ba. Halitta ta murmusa ta ce

"Kada ki damu, ina goyan bayan ki dari bisa dari"

"Na gode Halitta, Su Ammy sun kasa ganewa, ina son miji na, ina son Usman fiye da tunanin ku, akan wani dalili zan zubda cikin Usman?"
Chapter 27 · 0% Book details