← Book details auren shehu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 34

Sashe 28

auren shehu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duban ta Halitta ta ke cike da mamakin yanda te ke ikirarin kaunar da ta ke yiwa Usman wanda ada bubu wanda ta tsana kamar shi, lalle shi ya sa ba a so a fiya zurfafa kiyayya ko soyayya ga mutum. Halitta ta ruko hannun ta, cikin rarrashi ta furta

"Amma me zai sa ki dawo gida? Idan har ki na kaunar Usman me ya sa ki ka yarda ki taho ke kadai? Menene dalilin shi na barin ki ki taho?"

"Abubuwa sun faru dayawa Halitta, kin fi kowa sannin yanda na tsani Usman ada, ina zaman zama na Daddy ya daura min auren dole da shi, bayan rasuwar Daddy ni kuma na yi kuskuran sawa a kamo shi domin ya sake ni, shi ne aka kamo kanin sa......"

Nan takwashe komai ta fada ma Halitta, ta kare da

"Bayan ya warke shi ne ya gaba daya ya guje ni, dan Allah ina laifi na Halitta? Wallahi ban san kashe shi za su yi ba, I just wanted to go home then not knowing that Usman is the only home I've, yanzu gashi ya ba ni takarda, Allah kadai ya san saki nawa ya min...."
Ta kare maganar cikin kuka.

"Ina takardar ta ke?"

Kai ta girgiza mata ta ce

"Ah ah wallahi ba zan ba ki ba, ba za a bude ba, ba na so ma na san yawan sakin da ya min, ban shirya ba Halitta, haka ko da wasa kada ki bari su Ammy su san babu igiyar auren Usman a kai na"

"Kai amma be kyauta ba, Usman be ruke amanar Daddy ba....."

"Ya yi iyakar kokarin sa Halitta, Ni na hada baki da ma su neman ran sa, kada ki ga laifin sa Halitta"

"Haka ke ma ba ki da laifi Zainab, kin yi komai dan neman mafita ne, kin yi ne domin ke samu ki tsira, kuma duk wanda yayi judging din ki base on that ba adali ba ne, you did what you thought was right for you"

Shiru su ka yi na wasu mintina kafin Halitta ta nisa, kana ta ce

"Nan da sati biyu zan koma Saudia Yakura, Amma kafin na tafi zan so a ce kin yarda an je makarantar ku a san ya makomar karatun ki ya ke, mate din ki fa sun yi graduating"

Murmushi Zainab ta yi, yayinda ta ja filo yanda za ta dan kishingida, sannan ta furta

"Shin ki na tunanin zan iya komawa makaranta a wannan hali da na ke ciki? Ku yi hakuri ba zan iya ba Halitta, waccar Yakurar da ku ka sani is gone...har abada.."

Tausayin Zainab ya dada rufe Yakura, gashi hawaye ya na son zubo mata, Amma sai kokarin ruke shi ta ke dan kar Zainab ta gani ta kara karaya. Tashi ta yi da sauri za ta fita, har ta kai kofa ta tsaya, ta dan juyo kadan yanda Zainab ba za ta lura da hawayen da ke zuba daga idanun ta ba ta ce
"Falmat ta ce wayar ki ba za ta gyaru ba, wacce iri ki ke so a siyo mi ki?"

"Waya? I don't need it for now, ku bar ta kawai....."
"Yakura! Wani irin rayuwa ce wannan? Hatta waya ma ba za ki ruke ba?"

Zainab na murmushi ta ba ta amsa da

"Sanda ina slaying kun ce na fiya fitina, yanzu kuma I'm managing myself kuna ta kokawa! Dan Adam kenan, ba na bukata dole ne?"

"Ah ah ba dole fa"
Cewar Halitta yayinda ta fice abin ta tana zubda hawaye.
AUREN SHEHU 2

Kamar yanda Ammy ta mata alkawari babu wanda ya kara tunkarar Zainab da maganar zubda ciki, hakan ya sa ta dan sami kwanciyar hankali, musamman da Anty Sauda ta hada na ta ya nata ta koma Maiduguri.

Cikin sati daya Usman ya hade kayan sa, bayan ya shawo kan su kawu Iliya da kyar sun yarda ya sake barin Rugar Shehu. Ana saura kwana uku ya tafi aka daura auren Muhamad Bello da Raqeba. Iyalle ce ta karbi rukon Cangwai duk da a zahirin gaskiya sun gano ba diyar Usman ba ce, rashin Rahila da Tanko ya sanya dole su hakura su zauna da ita.
Muhamad Bello ne da kan sa ya raka Usman har Yola gidan Alhaji Ibrahim Balla kamar yanda ya yi alkawari. Ya karbi bakwancin Usman hannu bibbiyu musammam da ya ga harkar cigaban da ya zo da shi. Cikin gidan gonar sa ya bawa Usman masauki na musammam, cewar shi zai iya zama kafin ya bude ido shi ma ya sami na shi.

Alhaji Ibrahim Balla magidanci ne mai kimanin shekaru hamsin da biyar a duniya, matar shi daya haka kuma dan sa daya tilo kamar tsoka daya a miya, amma hakan be sa ya sangantar da dan na shi ba wanda ake kira Umar. Ya tashi da tarbiya, dattako dadin dadawa kuma ga gata, ilimi wayews da ado tamkar dawisu. Umar saurayi ne mai shekara talatin da biyar a duniya, kasancewar ya karanta health economics a Fannin digiri ya koma yayi development studies a masters ya sa ya zama shi ne jagaba wajan habbaka sana'ar mahaifin na sa, wato sana'ar gidan gona.

Cikin kankanin lokaci Alhaji Ibrahim ya lura da halayyar Usman, da kuma amanar sa, hakan ya sa zuciyar sa kwadaita masa hada shi da dan sa Umar wanda kusan duk abin da ya shafi gidan gonar shi ke tafiyar da shi. Ga kuma ilimin Isalama da ya tabbata Usman na da shi wanda ya ke da yakinin lalle Umar zai amfana sosai, da wannan ya yi kokarin kulla abotan Usman da Umar, duk da kuwa ya san in dai aka zo fannin wayewa hali ya sha bambam.

In da Allah ya kawo abin da sauki, sai ya hada jinin Umar da Usman, yanda ado da wayewar Umar ke burge Usman, shi kuma Usman kamala da ilimin addinin Usman ke burge shi, musamman da ya ji ya na larabcewa da wasu daga cikin abokan sana'ar su da su ke Larabawa, sannan duk wani muhadara da majalisin malamai Usman na kokarin zuwa wani lokaci har gayyatan Umar din ya ke. Kullu yaumin Umar na kokarin jan Usman jiki kamar yanda mahaifin sa ya ba shi umarnin, duk dai Usman na dan janye jikin sa ba dan komai ba sai gudun kar ya kwafsawa Umar, duk wata harka da ya shafi shiga cikin mutane sai Usman ya nemi ya janye jiki, har sai Umar yayi da gaske kafin ya yarda ya bishi. Duk wanda kuwa ya kuskure ko kallan banza ne ya yiwa Usman lalle kuwa a ga fushin Umar.

***

Hutun Halitta wacce ita ce mai debewa Zainab kewa ya kare, Sudais ya ce lalle ta hado nata ya nata ta koma Saudi ba zai iya zuwa Nigeria ba kamar yanda ya mata alkawari ba saboda yanayin aiki da ya yi yawa.

Da yamma likis Halitta shirye tsaf, sanye cikin bakar doguwar riga, suna tafe suna hira Zainab ta raka ta har mota in da Ammy da Falmat ke zaune suna jiran ta su kai ta Airport. Har ta zauna ta dubi Zainab wacce ke tsaye ta na duban ta. Sanye da hijab ruwan dorawa da ya kai mata har kasa, gaba daya ta sauya ba walwala ba farin ciki, kullum cikin damuwa ta ke har ta kai ya fara nunawa a jikin ta.

"Dan Allah Yakura ki rage damuwa ko dan cikin da ki ke dauke da shi"

Cewar Halitta cike da damuwa. Ta kara da.

"Zan mi ki addua in Sha Allah......"

"Idan har irin adduar da kuka min ne har Allah ya sa na dawo gidan ba na so, da ba ku min ba da yanzu ina tare da miji na..."

Jin haka Ammy ta kauda kai gefe. Falmat cikin ran ta cewa ta yi 'aha dama zancen kenan Yakura ta zama sai ka ce mayya!"

"In Sha Allah zan mi ki adduar mafi alkhairi a rayuwar ki"

Cewar Halitta. Zainab ta kada baki ta ce

"Usman ne mafi alkhairi Halitta"

Halitta na mai murmushin yake ta furta

"In dai shi ne toh Allah zai warware komai Yakura, bi'izinllah"

"Allahumma amen, Allah ya tsare ya sauke ku lafiya"

"Ameen ameen, ma yi chatting, ko da yake ke fa ko wayar ma ba ki da shi bare na chat, ki taimake ni Yakura, kira daga Saudi tsadi, ki samu yar waya sai mu ke gaisuwa ta social network, ki taimaka"

Zainab na murmushi ta bata amsa da

"Yar ana ce zai yi tunani akai"

Da haka su ka yi sallama jikin kowa a sanyaye.

***

Watannin Usman uku suna kasuwanci tare da Umar Balla. Hidimar da ke gaban sa be sa ya manta Zainab daidai da sakan daya ba, da ita ya ke tashi da ita ya ke kwanciya cikin ran sa. Wani sa'in sai yayi da gaske ya ke iya jure rashin ta. Har Umar ya kai ga ganewa akwai damuwar da ke tattare da shi, amma ko da ya tambaye shi dalili ce masa yayi babu komai kawai yakan dan yi tuntuntuni ne akan Rugar Shehu da kuma yanda zai bunkasa Rugar a sami cigaba.
Tafe su ke cikin motar Umar, kan hanyar dawowar su daga Mambila in da su ka je su ka yi cinikin shanu. Umar wanda ya ke baki, be da tsayi sosai amma kuma ba a kira shi gajere ba, haka kuma kyawun sa na ba yabo ba fallasa, sanye ya ke da kanana kaya, bakin wando da jar riga mai gajeran hannu. Usman da ke gefan sa sanye da wannan shigar ta sa da ya saba, riga yar shara, da rawanin sa da ya koma yi tun bayan tafiyar Zainab. Hankalin Umar kan kwalta ya furta

"Ni kuwa da za ka bi shawara ta Usman da fili za ka siya babba ko da kuwa a wajan, ka gina gidaje ciki in ya so ka kwaso duka jama'ar Rugar ta ka, ku yi zaman ku ciki "

Cikin kaguwa Usman ya furta

"Shin ka na ganin haka me yiwuwa ne? Kai mutane na fa ba kamar na ku ba ne, zaman bukka ya fiye mu su zaman binni da wahalar ta, Ni dai da ka ganni nan ni ke da kwadayin birni..."
Chapter 28 · 0% Book details