← Book details auren shehu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 34

Sashe 31

auren shehu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan komai ya lafa ya mu su bayanin abin da ya ke tafe da shi. Wato na mayar da Rugar Shehu cikin birni. Kamar yanda yayi hashashe, dayawa daga cikin su sun yiwa maganar mummunar fahimta, ciki har da Kawu Iliya. Amma ko da Usman ya tsaya ya mu su bayani mai gamsarwa sai su ka dan sauko, Amma duk da haka su ka ce bazai yiyu kowa yaye a bar daji ba. Duk sanda Usman ya gama shirin sa ya zo wasu daga cikin jama'ar Rugar su bishi, a fara ganin yanayin zaman da yanda zai kasance, idan har abu yayi kyau saura jama'a su bi bayan su, idan aka sami kishiyar haka kuma toh lalle wanda su ka bishi sai su dawo gida. Haka kuma shanu mallakan sa ne, ko da kuwa dubu zai kore zuwa birni ba zai talauta Rugar Shehu ba, dan haka babu mai tsayar da shi, adduar su dai kawai Allah ya idda nufi, ya kawo mu su alkhairi.

Kwanan Usman biyu kacal a Rugar Shehu, ana gobe zai koma Bello ya zo masa da sakon Raqeeba na ta na so ta gan shi. Usman ya ce toh bisimillah mana. Nan cikin bukkar shi ta zauna tare da mijin ta Bello. Usman na daga zaune can gefe yayinda zuciyar sa ta masa nauyi jin maganganun da ke fita daga bakin Raqeeba. Ta kwashe abin da ya faru tsakanin ta da Zainab, da kuma yanda ta tunzura ta har ta yarda ta hada baki da su Rahila ta fada mu su. Cike da nadama ta kare da

"Abu mai kaunar ka ce kwarai, sharrin shedan ya sa na aikata abin da na aikata amma sam babu laifin ta, laifin ta daya shi ne zafin kishi, dan sai a sannan ni kai na na gane Abu mai kaunar ka ce....."

Ganin Usman ya runtse idanu ya sanya Raqeeba kasa magana, cikin neman agaji ta ke kallan Bello wanda tun da ta gano ta kamu da san shi ta fada masa abin da ta aikata. Bello ya gyara muryar sannan ya furta

"Ta yi kuskure, tun da ta fada min na nuna mata bacin rai na....."

"Tun da ta fada ma ka? Ka na nufin ta ma fada ma ka amma ka kasa sheda min Muhamadu?"

Ya na kokarin kare kan sa ya furta

"Ah ah watan jiya ta sanar da ni, dama jira na ke...."

"Ya salam matar ka ta cutar da ni, ni Kuma na cutar da Abu! Har ka san wannan maganar amma ka kasa fada min? Watan jiya? Kasan kwana nawa na yi kullum da kewan Abu? Ka san dare nawa ya shude kullum da ita na ke mafarki? Kasan kwanaki nawa na yi kullum zuciya ta na kukan rashin ta? Haba Muhamadu Bello! Haba dan Allah!"

Cewar Usman yayinda ya tashi a firgice ya shiga hada kayan sa. Alama Bello ya yiwa Raqeeba da ta tashi ta tafi. Tsoran fushin Usman ya sanya ta kiran su Kawu Iliya. Su ka tadda Usman ya dau jaka har ya fito. Sun yi sunyi su bashi hakuri ya bari gari ya waye sai su tafi amma Usman yaki. Gani ya ke kowani sakan idan ya wuce ba tare da ya na hanyar Kano ba asara ne a gare shi. Dole suna ji suna gani su ka bar shi ya dau hanyar Mambila cikin daren.

Sai da gari ya waye tangararan rana ta hudo kai sannan ya isa Mambila. Nan ma abinci kawai ya ci sannan ya tasa Umar a gaba lalle su dau hanya Kano. Yanda dawo masa afujajan ya sanya Umar shiryawa su ka dau hanya ba tare da ya masa mu su ba. Tun da su ka dau hanya Usman ya je rama baccin da be yi daren jiya ba. Umar ya daga masa kasa har sai da su ka isa Jalingo, bayan sun yada zango hotel din da su ka saba sauka ya je har daki ya same shi.

Babban daki ne wanda ya kai matakin dakunan da alhazawa su ke kamawa. Bayan ya buga masa kofa ya bude masa, ya sake komawa ya yi zaman sa bakin gado, sanye da farar singileti da gajeran wando. Umar ya dube shi ya ce

"Na lura tun da ka dawo ba ka cikin hayyacin ka, me ke faruwa? Me za su yi Kano?"

"Abu zan dauko"

"Wacece Abu Kuma?"

Umar ya tambaya cikin nuna rashin fahimta. Nan Usman ya bashi wani bangare daga cikin rayuwar shi da Zainab ba tare da ya tona sirrin da ya shafi dakin auren sa ba. Kafadar shi Umar ya dafa sannan ya ce

"Sai yanzu na fahimci dalilin da ya sanya ka ki kula kowa. Lalle ni zan raka ka har Kano, Amma fa gaskiya ba za mu je haka yanda ka ke a burkice ba Malam! Sai ka nutsu ka kuma kwantar da hankalin ka!"

"Shin ka na ganin Zainab za ta yafe min?"

Umar na jinjina kai

"Matukar ta na san ka kamar yanda ka nuna min, za ta yafe ma ka Usman, dukkan ku kun yanke hukunci ne cikin rashin sani da gaggawa, duk ilimin ka, ita kuma duk wayewar ta be sa kun iya gujewa kaddarar ku ba, yanda za ka sani ajizanci ne na dan adam, shi dan adam ajizi ne Usman"

Kai Usman ya gyada kawai. Umar ya masa sallama, ya bar shi nan zaune ya na fargaban yanda zai tunkari Zainab bayan wata da watanni da tura ta gida.

Kamar yanda Umar ya ce, sai da ta tabbatar Usman ya nutsu sosai, sun kuma shirya zuwa gidan surukai da kyau sannan su ka dauki hanyar Kano, Usman ya so su bi jirgi, Amma Umar ya dage sai dai su tafi a mota. Daya daga cikin manyan motocin Alhaji Ibrahim Balla ya dauko dan har lokacin Usman be iya mota ba, bare ya mallaki ta kan sa, Umar kuwa ganin za su je gidan surukai da aka dade ba a hadu ba ya ga dacewar a je da babba harka yanda za su cika ido da kyau.

Da ya ke tun asuba su ka bar Yola, kuma Umar ya taka motar sosai, karfe hudu a Kano ta mu su. Kai tsaye Prince hotel su ka wuce in da su ka kama dakuna biyu. Dan zumudi jikin Usman har rawa ya ke. Umar na duban sa cikin zolaya ya ce

"Wallahi in ba ka dena wannan rawar jiki da zumudi ba babu in da za mu je yau sai gobe"

Fuska murtuke Usman ya furta

"Sai in ga me hana ni fita! Da ka san yanda na ke ji Umar da ka tausaya min"

Umar na murmushi ya ce
"Ni ma zolayar ka na ke, maza ka je ka shirya, ka tabbatar ka kure a daka yanda ko Abun ta ka baza ta gane ka ba, bare masu gadin nan da ka ba ni labarin su"

Cike da farin ciki Usman ya bi bayan wanda zai nuna masa dakin sa, ya na mai bawa Umar amsa da

"Yau kuwa zan ba ka mamaki Umari, dan ko kai kan ka ba za ka gane ni ba"

Haka su ka yi sallama su na wasa da dariya. Usman be bata lokaci ba nan da nan yayi wanka. Wata danyar farar getzner wacce aka mata aiki da shudin zare dinkin babbar riga ya sanya. Bayan ya feshe jikin sa da tuare mai tambarin 'Boadicea the Victorious', ya dau hularsa da aka saka da manyan zare kalar aikin babbar rigar sa sai dai kuma akwai wasu kalolin da su ka ratsa jiki, hular ta sha wanki da kari ya sanya. Daga agogon hannun sa har zuwa takalmin kafarsa kudi ne. Shi kan shi da ya kalli madubi, mudubi sai da ya kara dubawa. Lalle kam sutura ita ce mutum!

A restaurant ya sami Umar ya na cin abinci, ko daga shigan Usman ba sauran jama'ar da ke wajan ba, hatta Umar sakin baki yayi ya na duban sa har ya karasa teburin da ya ke.

"Butar shayi mutumin nan ka hadu! Wannan ado duk na zuwa biko ne?"

Cewar Umar cikin zolaya. Kujera ya ja ya zauna, kana ya ce

"Ka yiwa girman Allah ka min adalci ka bar wannan abincin mu tafi, wallahi da ka san halin da na ke ciki da ka tausaya min Umar"

Baki cike da shibkafa Umar ya ce

"Adalcin shi ne ka bari na cika timbi na Alhaji, da dai ace zuwan dadi ne da sai na sa ran za a ba mu na dare, Amma hakan nan siddin mu taso tun daga Yola har Kano ka hana cin abinci? Babu wannan maganar"

Cikin kosawa Usman ya furta
"Sai ka ta ci ai, idan ka gama ina jiran ka a mota"

Ya tashi ya fice in da matan da ke wajan su ka bishi da kallo. Shi kuwa gaba daya hankalin sa yayi gaba, in ba Zainab ya sa a Ido ba ba zai sami nutsuwa ba.

Sai da Umar ya take tumbin sa sannan ya fito su ka dauki hanya. Ko da su ka karasa gidan Malam su ka yi hon, Jauro ya ga motar da ke fake bakin kofa tuni ya bude mu su gate ba tare da ya damu da ya duba su waye cikin motar. Umar ne ya fara fitowa bayan sun yi fakin farfajiyar gidan, da sauri Jauro ya karasa gaban sa ya ba fadin

"Barka da zuwa Alhaji, sannu da zuwa Alhaji"

Ganin dogan mutum fari sol, ga kyau ga kwarjini ga kuma sutura, ya fito daga motar, Jauro be sanda ya zube kasa ba cikin fadanci, fadi ya ke

"Allah shi ja zamanin ka, barka da zuwa"

Shi kan sa abokin aikin Jauro bude baki yayi ya na kallan sa, dan kuwa tun bayan tafiyar musu ya can ji gurbin sa, be taba ganin Jauro ya rikice kamar yau ba. Shi kan sa Usman ya san tabbas Jauro be gane sa ba. Ya na shirin tambayar in da Zainab ta ke sai ga Anty Sauda ta fito. Ganin mota mai numfashi fake farfajiyar gidan da kuma mazan da su ke tafe cikin motar tuni ta karaso ta na tambayar
Chapter 31 · 0% Book details