← Book details Auren Raba Gardama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 9

Sashe 9

Auren Raba Gardama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Itama fuska ba walwala tace banajin yunwa,dariya ce ta tashi su'buce masa ganin yadda tawani d'aure fuska,ala dole bataci komai ba,

Magani zaki sha kuma kinsandai ba a taking drugs ba aci komai ba so dole kitashi kici abinci kisha mganinki,

Nifa bazanci ba, dan ba a dole,ta fad'a had'i da murgud'a baki,

Aikuwa dole kici, yafad'a daidai lokacin d yake saka aninin rigarsa,

To tunda ana dolene ni ka kyaleni ai dai cikina ne...............

Finciko ta yayi tunbata 'karasa ba, janta yari'kayi har gun da kayan suke sannan yadangwarar da ita, hannu yakai zai bude warmer d'in da chips ke ciki,

Dasauri tari'ke masa hannun, nidai umhumm na ce maka na 'koshi tafad'a tana shirin yin kuka,

Wata dariya ce tazo masa sai yayi hanxarin maidata, fuskarsa yad'aure yace ok tom leave my hand,

Ni zanci da sauri tad'ago kai tace ba kaciba kuma........saurin yin shiru tayi ganin tana shirin yin kato'bara,

Murmushi yayi sannan ya jaye hannunsa, had'i da d'aure fuska yace any way ni nafita idan kingadama ki karya kisha mganinki idn kuma kinso ma karki sha matsalar ki ce,

Duk abunda kike bu'kata kikira za akawo miki......

Daga haka yasa kai yafita abunsa,

Yana fita wani irin kewar gida yashigeta ta fashe da kuka,

Tana nadamar dawowarta Nigeria d duk haka bata faru d ita ba...................

M&Z
[18/01, 22:58] Hadiza Sani Fbk: 🌕🌕 *AUREN* *RABA* *GARDAMA* 🌕🌕

®🌲 *REAL* *HAUSA FULANI* * *WRITER'S* *FORUM*🐄

_Dan Allah_ _kucigaba da_ _mana uzuri wlh_ _abubuwanne Sai_ _a hankali_

🙏🏻 _please _masu_ _son_ _auren_ _raba__ _gardama daga_ _farko kuri'ka_ _tambayawa a_ _groups wlh tura_ _wanne da wuya_ _ko kuyi ha'kuri_ _idan mun 'kare_ _zamuyi_ _document._

_M&Z love you_ _fans sossai_ _sossai_ 😍💋💋

Na
MAMUH GEE
And

ZINNIEE SMART

91~95

Asubar farko yami'ke yayi alwala yanufi masallaci, yana dawowa itama ya tadata, ke jekiyi sallah,

Wani irin haushinsa takeji musamman idan yakirata d wani ke, mtsss tamike tanufi toilet d'in dan yin alwala,

Koda tafito yana zaune kan sallaya yana karatun Qur'an suratul Rahman yake karantawa cikin sassanyar muryarsa mai dad'in saurare,

Kallonsa tayi da gefen ido, tana matu'kar jin dad'in muryarsa, batasan meyasaba hakannan kawai muryarsa kemata dad'i lumshe idanuwanta tayi,

Tana cigaba d saurarensa had'i da sa'ke sa'ke a ranta, harya yagama yayi addu'a tana gurin da take a tsaye,

'Dago d kansa yayi yaganta tsaye a gun,nazarinta yad'anyi sannan yace,

Malama kinsandai shi jirgi baya jiran mutum,

A dan razane ta bud'e idonta had'i da kallonsa, a ranta tace jishi dn Allah dayana karatu tamkar na Allah, amma ynxun zakaga yakoma wani wicked,

Kinsan Allah bazaki sa mu rasa jirgi ba yau wlh idn kika bari nayi wanka nafito na shirya baki shirya ba hmmmm i'm sorry for you,

Tsaki tayi ciki ciki ta kama gunguni, yenyen yen yin, mtsss idn kaso ma ka kasheni,

Sallaya tanufa ta kabbarta sallah dn shi tuni yanufi bathroom,

Har yafito tana zaune kan sallayar duk da ba abunda take,

Ke wai me kike nufi, d'ago kai tayi dn tabashi amsa, da sauri tad'auke kanta kamar taga kashi dn ganinsa da tayi d towel a 'kugunsa,

Shikuwa ganin yadda tawani d'auke kai Sai yazaci, rainin wayau ne dn shi kallon fitsararriya yakemata,

A hankali cikin tafiyarsa d ke nuna mazan ta karsa ya 'karasa inda take had'i da du'kawa ya kamo ha'barta,

Ke uban waye kika gani kika wani d'auke kai???yafad'a d sigar tambaya had'i da'kura mata idanuwansa masu masifar razanata,

Ai kuwa da sauri ta runtse idon,

Ba dake nake ba yafad'a loudly

Turo bakinta tayi tana magana 'kasa 'kasa wanda bai fahimtar me take cewa, hannunta tasa tana 'ko'karin ture nasa hannun d yad'ago da ha'barta,

Nidai karabu dani mugu kawai,
Shikad'ai yafahimta acikin mganarta,

Au nid'inne mugu?tun banfara miki muguntar ba,

Baki ta'bud'e zata sake zuba wata tsiwar aikuwa, d hanzari ya zura nasa bakin, Laila ji tai gaba d'aya kamar 'kasa ta bud'e ta shiga dn itakam koda tayi zama a turai wannan shashancin ta tsaneshi dn mommyn ta ma bata wasa gurin kula d shige d ficenta,shiyasa yau yazamarmata wani irin ba'kon al'amari,

Shikuwa kissing d'in bakinta yake tamkar yasamu gurbin zuma, shida yayi niyyar yimata mugunta amma Sai yatsinci kansa d jin dad'in bakinnata,

'Ko'karin zarcewa yake dn har yafara shafan Boob's d'inta cikin hijab, itakuwa gabad'aya jinta take tamkar ba itaba, haushinsa d tsanarsa tasake ji amma me saitaji takasa hanashi abunda yake, saima hawaye da ke tsiyaya a idonta,

Laila ganindatayi abunnasa bana'karewa bane shiyasa ta daddage ta hankad'ashi had'i d rushewa d wani irin kuka Wanda itama bazata ce ga dalilin yinsaba,

Shikuwa Sai ynxun ma yalura da kato'barar d yatashi yi, amma Sai kawai yafuske, had'i d mi'kewa yace, ke dallah tashi kishirya,

Dn indai kukane ko farawa ma bakiyi ba kinji nafad'amiki,

Useless girl,

Laila kuwa tana shiryawa tana surfamasa Allah y isa d tsinemasa a zuciyarta..........
******************

6:00jirginsu yasauka a Miami, motar da tazo d'aukarsu ya nufa had'ida da fad'in,

Follow me, dasauri kuwa tabishi dn tasan halin muguntarsa,gashi ba 'kasar da tasani ba,

Suna Shiga motar takawarda kanta,tana kallon hanya hawaye na sirnano mata akan fuska,

Ji tayi duk duniyar tamata zafi kowama taji yafice mata a rai,

Duk tawani koma tamkar ba Laila yr gata d hutuba Lailan dady,

******************

M&Z🌕👌
[18/01, 22:58] Hadiza Sani Fbk: 🌕🌕 *AUREN* *RABA GARDAMA*🌕🌕

®🌲 *REAL* *HAUSA FULANI* *WRITER'S* *FORUM* 🐄

Na
MAMUH GEE
And

ZINNIEE SMART

101~105

Laila ce zaune a palon Mami kasancewar aikawa da tayi akirata,

Mamin ce tafito dga bedroom d'inta, sannu da fitowa Mami yawwa Laila,

Tafad'a had'i da zama kujerar da Lailan ke kai,

Hakan yasa tad'an matsa cike da jin kunya dn sossai take jin nauyin surikartata,

Laila bakomai yasa nace akiramun ke ba face inason intunatar dake wani abu,

Wato Laila na fahimci cewar babu wata jituwa tsakaninki da yaseer wanda Sam bana jin dad'in hakan,

Nasan auren da akaimuku dikkanninku ba wanda yake son d'an uwansa amma tunda anriga da anyi ykamata Ku fuskanci junanku,

A matsayina ta mahaifiyar yaseer na yi 'ko'karin ganincewar na daidaitaku, to nafara takan yaseer amma ba wani ci gaba dn hakanema nace zandawo takanki dn ko ba komai ke d'in macece,

Wacce natabbata duk girmankan namiji macce nasakashi yasauko,

Laila ina so kid'auke ni tamkar mahaifiyarki ba suruka ba, dn sossai nake 'kaunarki tun ranarda nafara ganinki naji kinkwantamun a rai dn hakane ma nakeso kiyi rayuwa da d'ana cikin farinciki da kwanciyar hnkali,

Tunda tafara magana kan Laila ke sunkuye dn tsananin kunyarta takeji ba kad'an ba,

Laila inaso ki kula da mijinki ki lura da me yakeso meye baya so kiyi 'ko'karin masa domin kisiye zuciyar mijinki dn Allah ysani mata da yawa dakike gani anacewa sun mallake mazajensu tofa ba wata mallaka,

Face tsantsar biyayya da kula da shi da me yakeso meye bayaso, tofa matu'kar kikatsare, wannan,

Wlh kingama sace zuciyar mijinki,Laila ina fata kinji mai nace,

Gyad'a kanta tayi a kunyace, tace naji Mami kuma insha'Allah zaki sameni mai bin dukkan maganganunki,

To Masha'Allah gskya naji dad'i sossai, tashi kije mijinki yakusa dawowa dn gobe ne d'ayan mai gidan naki zai dawo insha'Allah,tafad'a tana murmushi,

Ynzunma saida gabanta yasake fad'uwa, to Allah ydawo dashi lfy,

Amin Laila Allah y miki albarka,

Amin ngode mami,
******************

Sashenta tanufa tana tunanin maganganun Mami ta wani 'bangare kuma tana fargabar dawowar Saleem,
******************

Yauce ranar dawowar saleem, dn haka dukkan ma aikatan gidan sai faman aikace aikace sukeyi dn shalelen gidan zai dawo,

Sai faman d'orawa da saukewa ake,

Karfe 11:00 agogon Miami jirginsu yasauka yayin da yaseer da driver tuni suka tsufa a airport suna jiran saukan jirginsu,

A hankali yake saukowa cikin fasinjojin,jirgin, kyakyawane, Sossai kallo d'aya zaka masa kaga tsantsar kamar sa d yaseer,

Hangosa yaseer yayi dasauri kowannensu ya 'karasa ga d'an uwansa,

Hugging d'in junansu sukayi, cike da farincikin ganin juna,

Hello brother yakake, I'm cool bro, I'm so glad of meeting u again,

Same here bro,

So let go home, OK ??alright we can go..............

Haka suka nufi gida cike da farinciki,

Da farinciki Mami tatari d'an autan nata shikuwa zubewa yayi yanata zubamata shagwa'barsa, kai Saleem kullum baka girma oh Mami yaza ai nayi girma Inada mom da kuma yayana mai ji dani, dariya suka sa, dukansu,nan suka zube Palon ta sunata fira da barkwanci,

Laila kuwa tanacan d'aki ta 'kunshe, duk inda nutsuwarta take tafita daga jikinta,

Saima tunanin yadda zasu 'kar'ke da saleem takeyi,

Yaseer ne yaturo 'kofar d'akinta yayi sallama wacce balallai tajita ba, dn gabad'aya bata masan yashigo d'akin ba,

Murmushin mugunta yayi, a ransa yace is left to u yarinya,

Dungurin kanta yayi wanda yatilasta mata d'ago da kanta,

Ganinsa yasa ta'bata rai had'i da cino bakinta, d'alle bakin yayi da yatsarsa, d'an 'kara tasaki dn taji zafi sossai a ranta tace mugu,

Zaman me kikeyi a d'aki bakizo kintarbi brother na ba ??rasa mezatace masa tayi hakan yasa tace,

Kaina ke ciwo wani irin killer smile yayi yace to kedai fad'i gskya kodai ciwon so ne ya motsa....

Gabanta ne yafad'i dn a tunanin ta ko ya fahimci tafara sonsa ne??to amma yaushe ta farama da zaice ya tashi ??

Rasa amsa tayi kawai tayi banza dashi,

Anyway, kifito muci abinci dn Mami ce ma ta matsa a kiraki da bazanzo ba,

Ta'be baki tayi a ranta tace nidama kayi zamanka,

Hannunta yari'ke lokacin da zasu shiga palon mamin d'aga kanta tayi tadubeshi,

A mamakinta shi ko a jikinsa 'ko'karin shiga ma yake, hannunta tahau 'ko'karin kwacewa,

Kallonta yayi fuskarnan a had'e yace, meye haka?

Ai kai zanwa wannan tambayar to ba amsa kinji ko,

Daga haka yaja hannunta yayi ciki..............

Yayin da gaban Laila ke bugawa..

******************

M&Z🌕👌
Chapter 9 · 0% Book details