← Book details Auren Raba Gardama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 9

Sashe 6

Auren Raba Gardama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau tun safe ta shirya Cikin Morocco gown blue sai dan siririn gyale data daura.
Hand bag ce kawai ahannunta sai key din motar ta fito a Palo ba kowa
Dan haka bata tsaya shiga dakin Anty basma ba ta fice.

Zaune yake bakin gate yana hangota ya dauke kai sbd daga gani yau rashin mutuncin a kusa yake.

A zazafe ta figi motarta ya bude mata gate ta fice.

School ta tafi suna fitowa lectures suka yi gurin shopping itada maryam dagacan
Bata dawo gidaba sai maraice.

A gajiye tadawo tun a gate ta bar motarta tareda jefawa yaseer mukullai tace yashigo da motar ciki.

Karo taci da jabeer ta ra6asa zata wuce yayi saurin shan gabanta yana cewa,
Sis kwana biyu kinqi bari kowa yaganki,kin kuwa San yanda nayi kewar.....

Ya jabeer pls stop all this drama,
For god sake meyasa bazaku barni ba tunda nariga da nafadi ra'ayina.
Toh let me make sumtin very clear to u again,
Ni lailah banason kowa da aure acikinku so pls stay away,okey.

Dariyar zubair Ce tasasu waiwayowa dan basusan da zuwansaba.

Matsowa yayi zaiyi magana tayi saurin daga masa hannu tace,
Pls ya zubair you just heard what I huta,bana buqatar ko 'dayanku so kubarni na huta pls.

Juyawa tayi kan yaseer daya zo gurin a hasale tace,
And you what do you want?

Key yamiqa mata tareda juyawa.

M & Z
[18/01, 22:56] Hadiza Sani Fbk: 🌕🌕 AUREN RABA GARDAMA🌕🌕

Na

MAMUH GEEE🌕
And

ZINNIE SMART

61~65

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM.

Hannu ta 'daga ta dora akai tareda kurma wani mahaukacin ihu daya ratsa ko ina cikin gidan Wanda hakan yajawo hankalin kowa yayo harabar gidan.
Ganinsu Anty basma da kowa na gidan bikin sun fitone yasa tafara ganinsu dishi dishi kafin idonta ya rufe ruf ta sulale qasa a sume.

Anty kubra da maryam,siyama,ayshat da umman jabeer ne sukayi kanta da sauri suna salati.
Umman zubair kuwa tuni ta kawo ruwa ta antaya mata amma ko motsi batayiba.
Qara zuba mata ruwa akayi still ba alamar zata motsa.
Zubair ne yayi saurin kallonsu Anty basma yace,
Anty ku kamota da sauri muje asibiti.

A gigice suka kamata aka saka motar jabeer suka 'dunguma zuwa asibiti.

A emergency aka karbeta tareda fara bata taimakon gaggawar datake buqata.

Laidar ruwa biyu tasha kafin ta farfado,,
Idonta akan Anty basma da maryam ya sauka duk da daddynta na 'dakin amma saita samu kanta da qin kallon gefensa dan wani zafinsa takeji sbd ya tabbatar mata da baya qaunarta.

Anty basma aure aka dauramin da maigadin gidanmu sbd anga banida uwa,
Dama uwa itake son danta fiye da duk wani Wanda zai nunama soyayya.
Yau na tabbatar da banida mahaifiya a duniya,
A rasa waza'a dauramin aure dashi sai maigadin gidanmu.
Anty basma mum ta gargade ni da zuwa Nigeria na Dage akan zanzo sbd ina tunanin dad da alh tsoho suna sona fiyeda komai,
Ashe rashin sanine,duk wannan soyayyar a dah ne....
No lailah ki daina fadar haka dan ina tabbatar miki ba wani mai sonki da qaunarki a duniya sama da daddynki,
Daddynki yana qaunarki haryanxu kuma ya amince da wannan auren naki ne sbd kawai yiwa alh biyayya.
Kema kuma ina roqonki tareda baki shawarar kiyiwa naki mahaifin biyayya.

Girgixa kai tahauyi tana kuka mai qarfi tanacewa,
Bazan iya ba,
Bazan iya aurensa ba,
Bazan iya rayuwar awa daya dashiba bare rayuwar har abada.,
Bazan iya ba,
Na tsanesa wlh....

Kuka take rerawa cikin tsananin baqin ciki da tausayin kanta.

Dafa kanta dady yayi yace,
Sai hakuri lailah sbd bamuda wani zabi daya rage banda kiyi hkr ki kar6i qaddarar nan
Kuma ina tabbatar da zakiji dadi arayuwa lailah ko bayan raina ne muddin kikayimin wannan alfarmar ta kar6ar wannan hukunci na alh babba.,
Lailah ni mahaifinki haryanxu banida kamarki kuma ina roqonki lailah kiyimin wannan biyayyar dan.....
Jikinsa ta fada da sauri tana sakin wani sabon kukan tareda cewa,
Dady kadaina roqona.
Ki yarda dani lailah ina qaunarki fiyeda komai danake dashi arayuwa.....
Dady nasani kuma na yarda kana sona..

Lallashi tareda kwantar mata da hankali yayi har Dr yashigo tareda basu sallama suka kamo hanyar gida.

A hanya shiru tayi tareda jingina kanta ajikn window ta qurawa hanya ido tana tunanin rayuwarta ta lalace gabaki daya batada wani Abu daya rage mata najin dadi.

Runa isa bakin gate gabanta ya buga da qarfi sai alokacin ta tuno da tajiyo karar fasa kaya adakin yaseer kenan shima bayason auren.
Zanyi maganinsa dansaiya yabawa aya zaqinta.

Hayat ne yabude musu gate sbd yaseer din baya kusa.

Sunayin parking hayat ya matso yayi mata sannu da jiki yace kuma alh tsoho yace su wuce gurinsa yana buqatar ganinta itada dad dinta.

Suna shiga suka Tarar da ayshat tareda jabeer da zubair sai uwayensu.

Nasihar aure yayi musu sosai sbd a Daren ayshat zata tare hakama su zubair zasu tare a sabbin gidajensu da matayensu.

Kallon lailah yayi a natse yace,
Lailah nasan kina cikin damuwar auran da 'aka daura miki to batareda da 6ata lokaci ba dai ina baki umarni dakuma nasihar kiyiwa iyayenki da mijinki biyayya sbd ina hango miki kyakkawar Rayuwa da kwanciyar hankali a tattareda yaseer,
Nasan yaseer tun tuni nakumasan waye yaseer dakuma iyayensa hakan yasa na 'daura miki aure dashi.

Abba naseer ne ya dora da tasa nasihar kafinsu dady daganan aka dauki amarya ayshat zuwa gidanta suma su jabeer da abokanansu suka dunguma zuwa nasu gidajen.

M & Z
[18/01, 22:56] Hadiza Sani Fbk: 🌕🌕 AUREN RABA GARDAMA🌕🌕

Na

MAMUH GEEE🌕
And

ZINNIE SMART

51~55

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM.

Hankalinta bai qara tashiba saida dad dinta yadawo taga baice komai gameda hukuncin da tsoho ya yanke saima lallashinta daya hauyi akan ta daure tazabi daya daga cikinsu.

Yau sati yacika dan haka tana sane taqi zuwa gaida kowa dan kowa gidan haushi yake bata.

Kwanciyarta tayi adaki tanaji wayarta na ringin taqi dagawa sbd tasan cewa xa'ayi take ana kiranta.

Har bacci yafara janta Anty basma tashigo dakin tareda zama bakin gado tace,
Lailah ana kiranki a palon alh babba.

Ba Indi zani ni sbd gskia ni bansan dalilin dayasa ake son shiga life dinaba.

Yi hkr lailah muje kiji koma meyene kadaki manta daddynki na wajen.

Miqewa tayi tana 6ata fuska suka tafi.

Zama tayi tana yatsinar fuska sbd kowama batason gani.

Gyara murya yayi yafara fadin,

Lailah inason ki sanar damu wa kika zaba akan zancenmu na last week.

Turo baki tayi tace,
Nifa gaskia nafada banason kowa acikinsu barema wani aure.

Jinjina kai yayi yace,
To kisani kinyi wasa da damarki dan kuwa bazan janye zancenaba na aurar dake ga duk Wanda naga damaba matuqar baki fidda daya acikinsuba.

Dan haka kowa ya shirya ranar juma'a zan aurar da ita ga duk Wanda nasama,
Haka kuma jabeer da zubair Ku fiddo da mata tare duka za'a hadaku Dana ayshat.

Da gudu tabar palon tana fasa ihu
Sauran jama'ar palon ma da dai dai suka fita sbd hukuncin baima kowa dadi ba bama kamar dad dinta dayakeso tafara gama karatunta.

***************
3 days later,

Lallashin dunia dad da Anty basma sunyi mata amma taki daina kuka.

Yau maryam tazo tasamu ta lallabata dakyar suka fita yawo.

Sosai taji dadin yawon sbd tamanta matsalarta kuma maryam ta tabbatar matada wasace tsoho ke mata dan ba yanda za'ayi ayi mata auren dole
Hakan yasa ta sake suka hau chilling dinsu.

Ta 6angaren su zubair kuwa sunga ba kowa sai Allah sun fidda matayensu har ankai komai anfara shirye shirye.

Gida yacika maqil da 'yan biki domin kuwa hidima tayi nisa
Su lailah da siyama tareda maryam ba abinda ya damesu sbd lailah tuni tayi watsi da komai dan tasan ba abune mai yiyuwaba auren dole agareta.

Duk gyaran da akewa ayshat amarya itama sai anyi mata nata bare ma Anty basma data dage gurin gyaranta.

Anyi kamu da walima ana gobe daurin aure suka fita itada maryam da siyama harda ayshat zasu karbo sauran dinkunan ayshat.

Basu dawo gidaba sai maraice.
Agajiye suke dan haka suna shiga daki ta fada toilet tayo wanka sbd tana period ne.

Doguwar sleeping dress tasaka baqa sbd black shine best colour dinta.

Cornflakes tasa safiya takawo mata tasha tana gamawa saiga hayat brothern zubair yashigo dakin.

Zama yayi akan stool yana cewa,

Lailah kunada baqo a qofar gida tun dazu yazo yaseer maigadi ya hanasa shiga yace saiya kiraki yace yanata kira baki dagaba.

Wat" tafada da qarfi tana miqewa sbd tasan bilal ne brothern maryam Wanda shi take dating 'yan kwanakin.

Miqewa tayi ta 'Dora gyale akanta ta fito.

Tana isa bakin gate ta tarar dashi yana alwala fizge butar tayi tareda wankesa da ruwan.

Dagowa yayi yana mata kallon ido cikin ido wayar hannunta ta jefesa da ita tana nunasa da yatsa tace,
Kai ko acikin dabbobi bansan kai wayeba sbd daqiqancin yayi yawa.

Wani wawan kallo ya jefeta dashi
Hannu ta 'daga zata kai masa mari
Hannunta taji anriqe riqon daya razanata sbd taji maza.

Kallonsa tayi tareda fizge hannunta tafara zazzaga masa rashin mutunci agaban mutane har hkr ake bata amma bata saurara masaba.

Daga qarshe dai shigowar alh tsoho daga masallaci yasa kowa watsewa.
Kallon yaseer yayi yace......

M & Z
[18/01, 22:56] Hadiza Sani Fbk: 🌕🌕 AUREN RABA GARDAMA🌕🌕

Na

MAMUH GEEE🌕
And

ZINNIE SMART

66~70

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM.

Tunda tashiga dakinta dake zaune gaban mirror tana kallon fuskanta.
Tunani take ta ina zata fara?
Abu daya dayayi mata dadi shine babu alamar yanxu za'ayi maganar tarewarta ko wani Abu daya danganci auren.

Toilet ta fada tayo wanka tana fitowa su siyama da maryam nadawowa daga kai ayshat da'akayi.
Mamaki sukayi ganin tayi shirin bacci tana qoqarin kwantawa.
Maryam tayi qarfin halin fadin,
Lailah ya jikin naki?
Hummm my friend dnt worry abt me am fine now,in fact I will be fine every day.

Hmmmn wat a miracle my frnd,meya canxaki lokaci daya?

Babu abinda ya canxa ni kawai dai nayi wani tunani naga meye abin damuwa ga auren da ni ban dauka aure ba,hakama Wanda aka daura dashi shima bai daukesa aureba.
So inaga wannan ba aure bane daxan ringa damun kaina akai.
Tana gama fadar haka taja bargo ta lullubewarta.
Chapter 6 · 0% Book details